KAI TSAYE, Gasar kofin duniya 2026: An koma zagaye na biyu Belgium 0-1 Masar

Takaitaccen Bayanin Wasa

Belgium 0 , Egypt 1
Belgium
Masar
59 minutes , in progress
Hutun rabin lokaci Belgium 0 , Masar 1

Key Events

Belgium

    Masar

    • Emam AshourGoal 19 minutes
    Ba da ƙwallo a ci
    Masar,Mohamed Salah (19 minutes)

    Taƙaitattu

    Rahoto kai-tsaye

    Mohammed Abdu tare da taimakon AI

    1. , Belgium 0-1 Egypt

      Kadan ya rage a ci Belgium, bayan da aka bugo kwallo daga gefen hagu zuwa gidan Belgium, sai Salah ya sa kai nan da nan golan Belgium ya sa hannu ya doke kwallon daga nan ta je wajen Ashour, amma da ya buga ta yi fadi da yawa ba wani hadari.

    2. , Belgium 0-1 Egypt

      Kevin de Bruyne ya yi bugun tazara ta je ta bugi turke ta yi waje. Dama mai kyau da Belgium ta samu tun bayan da aka shiga zagaye na biyu.

    3. , Belgium 0-1 Masar

      Masar ta kusa samun zura kwallo ta biyu a raga, yayin da Mostafa Zico ya zura a guje zuwa cikin da'irar Belgium, amma ya yi kuskuren da kwallon ya je wajen Omar Marmoush wanda bai amfana da ita ba.

      Masara ta fara wasan zagaye na biyu da karfi gwiwa, so take ta samu dama tab kara na biyu, domin ta kwan da sanin za a iya farke kwallo daya a kowanne lokaci.

    4. , Belgium 0-1 Masar

      Tun lokacin da Belgium ta ci kwallo ta karshe a gasar cin kofin duniya da a Qatar a 2022, Kasar ta buga kwallo 38 zuwa raga ba tare da ta ci ba.

    5. An koma zagaye na biyu, Belgium 0-1 Egypt

      Ko Belgium za ta farke kwallon ko kuwa ya yi za ta kasance?

      Masar dai ba ta taba yin nasara a wasan gasar cin kofin duniya, ko wannan karon za ta yi a kan Belgium?

      Brandon Mechele ya yi gwagwarmaya don kwallon tare da Omar Marmoush

      Asalin hoton, Getty Images

    6. , Belgium 0-1 Egypt

      An je hutu za su yi minti 15 sannan aci gaba da zagaye na biyu.

    7. , Belgium 0-1 Egypt

      Haka itama Masar ta samu damar kara cin kwallo amma ta yi gefe da yawa, inda Marmoush ya buga ta bugi kafar mai tsaron ragar Belgium ta je bugun kusurwa.

    8. , Belgium 0-1 Egypt

      Doku ya samu dama mai kyau da zai farke kwallo daga cikin gidan Masar, sai dai kwallon da ya buga ta yi sama da yawa.

    9. , Belgium 0-1 Egypt

      An yi karin minti hutu daga nan za a je hutu

    10. , Belgium 0-1 Masar

      Belgium tana shan wahala a wannan zagayen farko, kuma tana kai hare-hare, amma ba wasu na tashin hankali ba.

      Kamar da Masar ta shirya wa wasan nan da wuri.

    11. , Belgium 0-1 Masar

      Akwai aiki a gaban kociyan Belgium, Rudi Garcia kan yadda ya kamata su farke kwallon nan, sai kai kora suke yi.

      Rudi Garcia

      Asalin hoton, Getty Images

    12. , Belgium 0-1 Egypt

      Egypt tana nuna kuzari sosai a wasan nan.

      Suna gudu, suna kuma matsa lamba, suna kuma yin abin da ya dace daga tsakiya.

      Hakan ya sa Belgium ba ta samun sukunin da take bukata.

    13. , Belgium 0-1 Egypt

      Belgium ta ƙirƙiri wata dama mai kyau, amma Emam Ashour ya yi kokari sosai, amma ta kai ga ya yi keta.

      Kwallon ta dawo ga Kevin De Bruyne, ya buga da karfi sai dai ba ta shiga raga ba.

    14. , Belgium 0-1 Egypt

      Tuni an sha ruwa an kuma ci gaba da wasan, inda Belgium ke kara kai matsi kan ko za ta iya farke kwallon.

    15. , Belgium 0-1 Masar

      Wannan shi ne karon farko da Emam Ashore ya ci wa kasarsa kwallo.

      Yan wasa sun tafi shan ruwa daga baya su dawo a ci gaba da fafatawar.

      Nasan Belgium za ta yi kokarin fitowa gabaki daya ta farke kan hutun rabin lokaci.

      Emam Ashour ya yi murna tare da abokan aikinsa

      Asalin hoton, Getty Images

    16. GOAL - Belgium 0-1 Egypt, Emam Ashour

      Kwallon ta yi kyau matuka, domin daf da layin da'ira ta 18 aka bai wa Ashour kwallo ya kuma juya ya buga daga wajen da karfi haka ta je ta wuce mai tsaron tagar Belgium.

      Kwallon ya buge bayan net

      Asalin hoton, Getty Images

    17. Katin gargadi ga Belgium, Belgium 0-0 Egypt

      Timothy Castagne ya karbi katin gargadi, sakamakon yi wa Mohamed Salah keta.

    18. Katin gargadi na farko, Belgium 0-0 Egypt

      Katin gargadi na farko a wasan ga Marwan Attia, bayan da ya kayar da Nathan Ngoy.

    19. , Belgium 0-0 Egypt

      Mohamed Salah ya fadi ƙasa yana neman bugun tazara, amma alkalin wasa bai bayar da komai ba.

    20. , Belgium 0-0 Egypt

      Yanzu kuma Belgium ce ke kai kora zuwa gidan Masar sun dan yi bani in baka, kuma De Bruyne ya buga kwallo da karfi amnma ta yi fadi ta fita waje.

      Idan zai ci gaba da haka komai zai iya faruwa.

      Kevin De Bruyne ya harbe a karkashin matsin lamba daga Marawan Attia

      Asalin hoton, Getty Images