KAI TSAYE, Gasar kofin duniya 2026: Netherlands 0-0 Japan

Takaitaccen Bayanin Wasa

Netherlands 0 , Japan 0
Netherlands
Japan
38 minutes , in progress

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. , Netherlands 0-0 Japan

    Kwallon ta je wajen Keito Nakamura a cikin da'ira ta bugun fenariti, sai dai kamar ya rasa mai zai yi, amma ya sa kafa ya taɓa, amma babu wata barazana.

    Sai dai Hiroki Ito ya gwada sa'a, sai dai ƙwallon da ya buga ta yi sama sosai.

  2. , Netherlands 0-0 Japan

    An ci gaba da wasa, amma dai karawar nan ba haka aka sa ran za a buga wasan ba, an sa ran za a ga kazar-kazar daga Japan, amma sai aka ga tana bin wasan a hankali, domin ta sa Netherlands ba karamar kasa bace.

    Crysencio Summerville ya kalubalanci Daizen Maeda

    Asalin hoton, Getty Images

  3. , Netherlands 0-0 Japan

    An je hutun shan ruwa domin ƴan wasa su huta, saboda yanayin zafin kasar.

  4. , Netherlands 0-0 Japan

    Netherlands ta samu ta shiga gidan Japan ta kuma yi ɗan kazar-kazar da ƙwallo, amma ba ta samu wata dama ba, an kuma fitar da ƙwallon.

  5. , Netherlands 0-0 Japan

    Ana raba ƙwallo mai ƙyau, inda Japan ke fatan shiga gidan Netherlands

    Shogo Taniguchi ya yi gudu a gefen hagu da ƙwallo, ya kuma buga amma ta yi faɗi.

  6. , Netherlands 0-0 Japan

    Ritsu Doan ya bar kwallon yayi tunanin akwai nasa a bayansa wanda zai iya karɓar ƙwallon, amma sai ta je wajen Netherlands.

    Japan da sauri ta dawo ta tare gida.

  7. , Netherlands 0-0 Japan

    Ana gara leda mai ban sha'awa.

    Babu wani kazarkazar sosai, amma dukkansu sun ƙwan da sanin mahimmacin samun maki uku a wannan karawar. Wasan ya fara ɗan nutsawa.

  8. , Netherlands 0-0 Japan

    An yi wa Keito Nakamura laifi daga Micky van de Ven kenan Japan ta samu bugun tazara.

  9. , Netherlands 0-0 Japan

    Mai tsaron bayan Liverpool, Virgil van Dijk bai samu hutu da yawa ba.

    Wannan shi ne wasa na 66 da yake buga wa a 2025-26 daga ciki 55 a Liverpool da kuma 11 a Netherlands, kuma kowanne da shi ake fara wasa.

  10. , Netherlands 0-0 Japan

    An yi hasashen cewa nan gaba za a yi guguwa a birnin Dallas amma hakan ba zai shafi wasan ba, domin ana rufe saman filin babu wata matsala.

  11. , Netherlands v Japan

    An fara wasan kuma Neterlands ce ta fara take leda da mayar da ƙwallo gida.

    Za a buga minti 45, za kuma a bayar da hutun shan ruwa domin an wasa su huta, saboda yanayin zafi. Daga nan aje hurtun rabin lokaci.

    Ko za a ci ƙwallo a cikin waɗan nan mintunan ko kuma yaya?

  12. , Netherlands v Japan

    An kammala rera taken kasashen biyu, yanzu ake sa ran fara wasan, ƴan ƙwallo na cikin fili.

    'Yan wasan Holland sun yi kira ga taken kasa

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Me ya faru a wasannin Lahadi?, Netherlands v Japan

    Tawagar Jamus ta fara gasar bana da kwarin gwiwa, sakamakon doke Curucao 7-1.

    Scotland da Australia dun sun fara da samun maki uku-uku.

    Magoya bayan Jamus

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Manyan ƴan wasan Japan da ke jinya, Netherlands v Japan

    Kyaftin din Japan, Wataru Endo, wanda ya hakura da buga gasar cin kofin duniya a wannan makon, yana ɗaya daga cikin manyan da ba za su buga wasan ba.

    Ɗan wasan, Brighton Kaoru Mitoma ya ji rauni, haka shima Takumi Minamino na jinya.

  15. , Netherlands v Japan

    Magoya bayan Netherlands sun je filin wasan makil suna tafiya ta gargajiya kamar yadda suka saba a kowacce gasa.

    Magoya bayan Netherlands

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Netherlands

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Netherlands

    Asalin hoton, Getty Images

  16. , Netherlands v Japan

    Magoya bayan Japan je birnin Dallas kwai da kwarkwata.

    Magoya bayan Japan

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Japan

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Japan

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Ko Japan za ta ci gaba da yin abin ban mamaki a gasar cin kofin duniya?, Netherlands v Japan

    Kowacce gasa da Japan ke halarta ta yi yin abin ban mamaki, wanda ke wuce tsammani ko hasashen masana tamaula.

    A wannan gasar kasashe kalilan ne ke wasa irin na Japan, wanda take sa sauri da kai hare-hare ta kowacce kusurwa ga kuma ɗan karen gudu.

    A gasar da aka buga a 2022 a Qatar ta doke Jamus da Sifaniya ta kuma ja ragamar rukuni na biyar a lokacin.

    To sai dai an yi waje da ita a zagayen ƴan 16 a hannun Croatia a bugun fenariti.

    Yanzu dai shekara huɗu tsakani, kenan tana da damar yin wasu abubuwan bajinta a wasannin bana.

    Sauran tawagogin da suke rukuni na shida sun haɗa da Sweden da kuma Tunisia.

  18. , Netherlands v Japan (21:00 BST)

    Netherlands za ta fara wasan gasar cin kofin duniya ba tare da wani ɗan wasa da ke buga babbar gasar tamaula ta Netherlands, wato Dutch Eredivisie a karon farko a tarihi, yayin da abokiyar hamayya, Japan take da ƴan wasa biyu da ke taka leda a gasar ta Dutch da ya haɗa da Tsuyoshi Watanabe da kuma Ayase Ueda.

  19. Labaran da ya shafi ƴan wasan tawagogin biyu, Netherlands v Japan

    Daizen Maeda na Japan mai taka leda a Celtic zai ja ragamar ƴan wasa a kokarin da tawagar ke yi na ci gaba da taka rawar gani a wasannin.

    Haka kuma za ta fara wasan da mai tsaron bayan, Bayern Munich Hiroki da kuma Ritsu Doan mai taka leda a Eintracht Frankfurt.

    Ƴan wasan Japan 11: Suzuki, Ito, Taniguchi, Watanabe, Nakamura, Kamada, Sano, Doan, Maeda, Kubo, Ueda.

    Kyaftin din Netherlands, Virgil van Dijk na Liverpool, zai jagoranci tawagar da Ronald Koeman ke horarwa. Haka kuma Van Dijk zai taka leda tare da takwarorinsa da suke wasa a Liverpool da ya haɗa da Cody Gakpo da kuma Ryan Gravenberch.

    Mai tsaron bayan Tottenham, Micky van de Ven yana ciki tare da ƴan wasa biyun da ke wasa a Brighton, wato mai tsaron raga, Bart Verbruggen da kuma Jan Paul van Hecke. Ɗan wasan Manchester City, Tiijani Reijnders, yana ciki, tare da na West Ham United Crysencio Summerville.

    Ƴan wasan Netherlands 11: Verbruggen, Van de Ven, Van Dijk, Van Hecke, Dumfries, Reijnders, De Jong, Gravenberch, Gakpo, Malen, Summerville.

    Japan XI

    Asalin hoton, BBC Sport

    Netherlands XI

    Asalin hoton, BBC Sport

  20. , Netherlands v Japan

    Wannan shi ne ake kira filin wasa na AT &T!

    A nan filin Ingila za ta buga wasan farko a rukuni da za ta kara da Crotia ranar Laraba.