Marco Rose ya amince zama sabon kocin Bournemouth, Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Jamus, Marco Rose, ya amince da karɓar aikin horar da Bournemouth bisa kwantiragin shekara uku, wanda zai fara aiki da zarar kocin yanzu Andoni Iraola ya bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana.
Bournemouth ta sanar a ranar Talata da ta gabata cewa Iraola, mai shekaru 43, ba zai sabunta kwantiraginsa ba, lamarin da ya buɗe hanyar ɗaukar wani sabon koci.
Rahotanni sun nuna cewa Rose na daga cikin ƴan takara uku da Bournemouth ta duba kafin yanke hukunci, tare da kocin Ipswich Town, Kieran McKenna da kuma kocin Rayo, Vallecano Inigo Perez.
Rose, mai shekaru 49, bai da ƙungiya tun bayan sallamarsa daga RB Leipzig a watan Maris a shekarar 2025, kuma wannan ne karon farko da zai yi aikin horaswa a kasar Ingila.
Ya fara aikin kociya tun a shekarar 2012 da Lokomotive Leipzig, sannan ya rike shugabanci a manyan ƙungiyoyi da suka haɗa da Red Bull Salzburg da Borussia Dortmund da Borussia Monchengladbach da kuma RB Leipzig.
A nasarorin da ya samu, Rose ya jagoranci Red Bull Salzburg zuwa lashe gasar Austrian Bundesliga biyu tare da kofin Austrian Cup, sannan ya lashe DFB-Pokal da kuma DFL-Supercup yayin da yake tare da RB Leipzig.















