Yan wasa na daf da fitowa fili, Paris St-Germain v Arsenal
An fito da katafaren kofin Champions League cikin fili, yanzu yan wasa sun fara fitowa da shirin fara wasan da kowa ke jira.
Wannan shi ne karo na takwas da za su kece raini bayan kowacce ta yi nasara biyu da canjaras uku.
Dabarun da Arsenal za ta iya amfani da su ta lashe Champions League
Arsenal da koci Mikel Arteta na fatan ƙara ɗaukar kofi mai suna Champions League a karon farko, bayan lashe Premier League, inda za ta kara da Paris St Germain a wasan karshe ranar Asabar.
Arsenal ta yi fice a wasannin Turai ta hanyar mallakar ƙwallo da bani in baka da kuma rage damar bai wa abokan hamayya sararin cin ƙwallo. Hakan ya taimaka mata wajen yin wasa ba tare da ƙwallo ta shiga ragarta ba, mafi yawa a gasar kenan.
A gefe guda, PSG ta fi kowace kungiya cin ƙwallaye a wannan kakar a Champions League, inda ta zura 44 a raga, yayin da Arsenal ke da 29.
Champions League: Damar da PSG ke da ita a kan Arsenal
Da alama babu wani abu da ya fi ƙayatarwa a ƙarshen wannan kakar kamar karawar da za a yi tsakanin ƙungiyoyin Ingila da Faransa a wasan ƙarshe na gasar Champions League, bayan shafe tsawon kakar ana gwagwagwa.
Ƙayataccen wasan da zai gudana a filin wasa na Puskas Arena da ke birnin Budapest na ƙasar Hungary, shi ne karawa ta 63 da Arsenal za ta yi a wannan kaka, wadda ta fara kakar da nufin lashe kofuna huɗu rigis, har sai zuwa farkon watan Afrilu inda ta tabbatar hakan ba zai yiwu ba.
Kocin Paris Saint-Germain, Luis Enrique, ya gargadi Arsenal cewa ƙwazon da ƙungiyarsa ke da shi na kare kambun Champions League ya fi ƙarfin burin Gunners na lashe kofin a karon farko.
PSG na neman zama ƙungiya ta biyu kacal a zamanin Champions League na zamani da za ta iya kare kambunta cikin nasara, bayan Real Madrid wadda ta lashe kofin sau uku a jere tsakanin 2016 da 2018.
A kakar da ta gabata, PSG ta doke Arsenal a wasannin gida da waje a zagayen kusa da na ƙarshe, kafin daga bisani ta murƙushe Inter Milan da ci 5-0 a wasan ƙarshe, inda ta lashe kofin Champions League na farko a tarihinta.
Yanzu Arsenal ce ke fuskantar irin wannan ƙalubale, yayin da take neman lashe kofin zakarun Turai karo na farko a tarihinta.
Wannan ne wasan ƙarshe na biyu da Arsenal za ta buga a gasar, bayan ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Barcelona a wasan ƙarshe a shekarar 2006 da aka buga a birnin Paris.
Saboda haka, wasan ƙarshe na bana zai kasance babban gwaji tsakanin PSG mai neman ci gaba da mulki a Turai da kuma Arsenal mai neman rubuta sabon tarihi.
Asalin hoton, Getty Images
Yadda Arsenal ta kai wasan karshe
Karawar cikin rukuni
2-0 Athletic Club (waje)
2-0 Olympiacos (gida)
4-0 Atletico Madrid (gida)
3-0 Slavia Prague (waje)
3-1 Bayern Munich (gida)
3-0 Club Brugge (waje)
3-1 Inter Milan (waje)
3-2 Kairat (gida)
Yan 16: 3-1 gida da waje da ta doke Bayer Leverkusen (1-1, 2-0)
Kwata fainal: 1-0 gida da waje da ta yi nasara a kan Sporting (1-0, 0-0)
Daf da karshe: 2-1 gida da waje da ta fitar da Atletico Madrid (1-1, 1-0)
Asalin hoton, Getty Images
Yadda PSG ta kai wasan karshe a Champions League
Daga karawar cikin rukuni
4-0 Atalanta (gida)
2-1 Barcelona (waje)
7-2 Bayer Leverkusen (waje)
1-2 Bayern Munich (gida)
5-3 Tottenham (gida)
0-0 Athletic Club (waje)
1-2 Sporting (waje)
1-1 Newcastle (gida)
Cike gurbi: ta ci 5-4 gida da waje a wasa da Monaco (3-2, 2-2)
Yan 16: 8-2 gida da waje ta doke Chelsea (5-2, 3-0)
kwata fainal: 4-0 gida da waje ta yi wa Liverpool (2-0, 2-0)
Daf da karshe: 6-5 gida da waje ta fitar da Bayern Munich (5-4, 1-1)
Asalin hoton, Getty Images
Barkanmu da zuwa Budapest
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Magoya baya sun taru a filin Emirates
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Tarihin lashe European da Champions League daga Burtaniya
Asalin hoton, Getty Images
A tarihin gasar European Cup da kuma UEFA Champions League, kungiyoyin Birtaniya sun lashe kofin har sau 16.
Celtic ce ta fara kafa tarihi, bayan ta doke Inter Milan da ci 2-1 a wasan ƙarshe na kakar 1966-67.
Shekara guda bayan haka, Manchester United ta zama kungiyar Ingila ta farko da ta lashe wannan babbar gasa ta Turai.
Kungiyoyin Birtaniya da suka lashe kofin:
Celtic – 1967
Manchester United – 1968, 1999, 2008
Liverpool – 1977, 1978, 1981, 1984, 2005, 2019
Nottingham Forest – 1979, 1980
Aston Villa – 1982
Chelsea – 2012, 2021
Manchester City – 2023
Yanzu kuma Arsenal na da damar shiga cikin wannan jerin masu daraja idan ta doke Paris Saint-Germain a wasan ƙarshe na Champions League 2026.
Idan Arsenal ta yi nasara, za ta zama kungiyar Ingila ta bakwai da ta taba lashe kofin zakarun Turai.
Asalin hoton, Getty Images
Barkanmu da kasancewa
BBC Hausa zai kawo muku wasan karshe tsakanin Paris St Germain da Arsenal a Champions League ranar Asanar 30 ga watan Mayu.
Sunana Mohammed Abdu zan kasance tare da ku, za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook.
Asalin hoton, Getty Images
Ga Premier League ga Champions League
Wannan na iya zama kaka mafi girma a tarihin Arsenal.
Bayan shekara 22 suna jiran dawowar kofin gasar Ingila, a ƙarshe Arsenal ta sake zama zakarar Premier League, kuma yanzu tana da damar cimma wani abin tarihi da ba ta taɓa yi ba a rayuwarta.
Kungiyar ta Landan na daf da zama zakarar Turai a karon farko idan ta samu nasara a wasan ƙarshe a UEFA Champions League Final.
Sai dai akwai babban ƙalubale a gabanta. Mai rike da kambun gasar, Paris Saint-Germain (PSG), ita ce ke tsaye a hanyarta.
Za a buga wannan babban filin Puskas Arena da ke birnin Budapest na ƙasar Hungary.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni
Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu kawo muku wasan karshe a Champions League tsakanin Paris St Germain da Arsenal ranar Asabar 30 ga watan Mayun 2026.
Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.