Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 08/06/2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muslim Muhammad Yusuf, Aisha Babangida da Usman MINJIBIR

  1. Mun kai hari kan sansanonin jiragen saman Isra'ila - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta kai hari kan sansanonin jiragen saman Navatim da Tel Nof na Isra'ila.

    A cikin wata sanarwa da kafafen yaɗa labaran Iran suka wallafa, rundunar ta ce sun yi niyyar kai hare-haren ne kan muhimman cibiyoyi da ke cikin wadannan sansanonin jiragen sama guda biyu.

    Sanarwar ta ce an kaddamar da hare-haren ne a matsayin mayar da martani ga abin da ta kira hare-haren Isra’ila kan muhimman cibiyoyin tsaro na Iran

  2. Atiku ya jinjinawa sojojin Najeriya kan ceto mutum 360 da aka sace a Borno

    Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yaba da nasarar da sojojin ƙasar suka samu wajen ceto mutane 360 da aka sace a kauyen Ngoshe da ke Jihar Borno.

    An gudanar da aikin ceto ne a yankin Dutsen Mandara, inda aka ce mayaƙan Boko Haram suka riƙe mutanen da aka sace tun bayan harin da suka kai a wani sansanin soji da ke Ngoshe.

    A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Atiku ya nuna farin cikinsa kan ceto mutanen, yana mai cewa hakan ya kawo sauƙi ga waɗanda aka sace da kuma iyalansu da suka shafe watanni cikin damuwa tun watan Maris.

    Ya ce: “Na ji daɗin jin labarin ceto mutum 360 da ‘yan ta’adda suka sace a Ngoshe, jihar Borno.”

    Ya ƙara da cewa duk da wannan nasara, har yanzu ƙasar na fuskantar barazanar ta’addanci da kuma hare-haren ‘yan bindiga.

    Atiku ya kuma yaba wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro da suka taka rawa wajen nasarar aikin yana mai cewa ƙoƙarinsu ya taimaka wajen kubutar da mutanen.

    Ya ce ya yi imanin cewa idan aka ba dakarun tsaro kayan aiki da cikakken goyon bayan shugabanci mai inganci, za su iya shawo kan matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.

  3. Hezbollah ta ƙaddamar da harin ramuwar gayya kan sojojin Isra'ila a Lebanon

    Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta harba jerin makamai masu linzami kan jerin motocin sojin Isra’ila da dakarunsu da ke kudancin Lebanon da safiyar yau.

    A cikin wani saƙo da ta wallafa a Telegram, Hezbollah ta bayyana cewa ta kai farmaki kan taron sojojin Isra’ila a wajen garin Beit Yahoun.

    Ta ce harin martani ne ga abin da ta kira karya yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma hare-haren Isra’ila kan ƙauyukan kudancin Lebanon.

    Har zuwa yanzu, Isra’ila ba ta fitar da wani bayani ba kan lamarin, kuma ba a tabbatar da girman ɓarnar ko adadin waɗanda suka samu rauni ba.

    Sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon, a abin da suke cewa na da nufin hana Hezbollah ci gaba da kai hari kan arewacin Isra’ila.

  4. Gwamnatin Najeriya ta rage kuɗin gudanarwa da ake ba ministoci zuwa 700,000

    Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sabbin matakan da ke da nufin ƙarfafa ladabtar da harkokin kuɗi a ma’aikatun gwamnati, ta hanyar rage adadin kuɗin da ake warewa ministocin domin gudanar da ayyukan gaggawa da dai sauransu.

    Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da riƙon amana a kashe kuɗaɗen gwamnati.

    Sabbin ƙa’idojin sun fito ne a cikina cikin takadar da ta ƙayyade iya kudaɗen da aka kashe da Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya sanya hannu a kai, wadda Ofishin Akanta-Janar na Tarayya ya fitar a matsayin sanarwar hukuma.

    Takardar ta ba da damar a rage kuɗaɗen kashewa da ake warewa ministoci zuwa Naira 700,000, yayin da sakatarorin dindindin da shugabannin hukumomi zuwa naira 500,000.

    Daraktoci da shugabannin sassa kuma an rage nasu zuwa naira 300,000, yayin da shugabannin ofisoshi a matakin jihohi da sauran masu riƙe da muƙami zuwa naira 100,000.

    Gwamnatin ta kuma bayyana cewa wannan mataki na cikin tsarin bin dokokin kuɗi tare da ƙarfafa cewa dukkan sayayya da ta haura Naira miliyan ɗaya dole ne a bi tsarin kwangila kamar yadda doka ta tanada, a wani yunƙuri na rage almubazzaranci da inganta gaskiya a amfani da kuɗin jama’a.

  5. Farashin mai ya tashi bayan hare-haren Iran da Isra’ila

    Farashin mai ya fara tashi a kasuwannin duniya bayan rahotannin musayar hare-hare tsakanin Iran da Isra’ila.

    Masana tattalin arziki sun ce fargabar ɓarkewar rikici mai tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya na daga cikin abubuwan da ke jawo tashin farashin.

    Man Brent ya ƙaru da kashi 4.5 cikin 100 inda ya kai dala 97.30 kan kowace ganga, yayin da man West Texas Intermediate na Amurka ya tashi da kashi 3.4 cikin 100 zuwa kusan dala 94.50 kan ganga ɗaya.

    Wannan na nuna yadda kasuwar makamashi ke amsawa ga duk wani tashin hankali a yankin da ke samar da kaso mai yawa na mai a duniya.

    A kasuwannin Asiya kuma an samu faɗuwa mai tsanani a farkon safiyar Litinin, inda manyan ma’aunai suka ragu sosai.

    Rahotanni sun nuna cewa ma’aunin hannayen jarin Kasar Koriya ta Kudu, Kospi, ya ragu da kusan kashi 8 cikin 100, abin da ke nuna damuwar masu zuba jari kan yiwuwar taɓarbarewar tattalin arziƙin duniya.

    Masana suna cewa wannan yanayi na nuna yadda rikicin siyasa a Gabas ta Tsakiya ke iya yin tasiri kai tsaye ga farashin makamashi da kuma kasuwannin duniya, lamarin da ke shafar ƙasashe masu dogaro da shigo da mai da kuma masu fitar da shi.

  6. Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta tabbatar da kai hari kan Isra’ila

    Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta tabbatar da kai hari kan Isra’ila, inda ta ce harin ya nufi wani yanki da ta kira “yankin Jaffa da aka mamaye.”

    Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, wadda ta ƙara da cewa matakin na cikin jerin hare-haren da take ci gaba da kai wa dangane da rikicin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya.

    A cikin sanarwar, ƙungiyar Houthi ta kuma bayyana haramta zirga-zirgar jiragen ruwan Isra’ila a Tekun Bahar Maliya.

    Sun ce duk wani jirgin ruwa mai alaƙa da Isra’ila ba zai samu damar wucewa cikin yankin ba har sai an kawo ƙarshen abin da suka kira zalunci kan Falasɗinawa.

    Wannan sanarwar na ƙara nuna yadda rikicin yankin ke faɗaɗa, tare da tasirin da ke bayyana a hanyoyin ruwa da harkokin kasuwanci a Tekun Bahar Maliya.

  7. Amurka ce ke da alhakin hare-haren da Isra’ila ta kai mana - Iran

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqaei, ya ce Amurka ce ke da alhakin hare-haren da Isra’ila ta kai wa Iran.

    Da yake magana a taron manema labarai na mako-mako, Baqaei ya bayyana cewa duk wani abu da ya faru a yankin, to Amurka ce za ta ɗauki alhakin hakan.

    “Duk abin da ya faru a yankin, ko Amurka da kanta ce ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar kai hare-hare kan jiragen kasuwancin Iran da kutsawa yankunan kudancin kasar da dai sauransu, Amurka ce ke da alhaki kai tsaye.

    Haka kuma sakamakon duk wani ƙarin tashin hankali zai rataya a wuyanta.”

    Bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a daren jiya, jami’an Amurka sun bayyana cewa sojojin Amurka ba su da hannu a harin.

    Sai dai Baqaei ya ce rundunar sojojin Amurka ta CENTCOM tana aiki tare da Isra’ila a ɓangarorin kai hari da kuma kariya.

    Da aka tambaye shi game da rahotannin da ke cewa an kai hari sansanin sojin Yarima Sultan da ke Saudiyya, Baqaei ya ce rundunar sojin Iran kan sanar a hukumance duk wurin da ta kai hari.

  8. Iran ta kai harin ramuwar gayya kan cibiyoyin man Isra'ila

    Dakarun juyin juya halin Iran, IRGC, sun ce sun ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya da makamai masu linzami kan cibiyoyin man Isra'ila da ke Haifa.

    A wata sanarwa da IRGC ta fitar, ta ce ta kai harin ne bayan da Isra'ila ta kai mata hari kan cibiyoyin man ƙasarta.

    Isra'ila ta kai harin ne kan matatar man Iran ta Karun Mahshahr. duk da yake IRGC ba ta bayyana sunan matatar a bayanin nata ba.

    Ta ƙara da cewa, "kai hare-hare kan fararen hula da matatun mai babbar barazana ce da za ta iya jefa yankin cikin matsalar makamashi",

    Kakakin hukumar kula da cibiyoyin man ya bayyana a wata sanarwa cewa: "an kai hari sau biyu a kan matatar ta Karun" amma ba a samu jikkatar mutane ba kuma ana ci gaba da duba ɓarnar da harin ya yi.

  9. Iran ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama

    Iran ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a babban filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa da ke babban birnin ƙasar, Tehran.

    Haka kuma an rufe sararin samaniyar yammacin ƙasar har sai abun da hali ya yi.

    A Syria ma mahukunta sun dakatar da sauka da tashin jiragen sama a babban birnin kasar Damascus, tare da rufe sararin samaniyar kudancin ƙasar na tsawon sa’o’i goma sha biyu.

    Ita ma Iraqi ta sanar da rufe sararin samaniyarta na tsawon sa’o’i saba’in da biyu.

  10. Iran da Isra’ila sun yi wa juna ruwan wuta da makamai masu linzami

    Iran da Isra’ila sun ci gaba da musayar hare-haren makamai masu linzami cikin dare har zuwa safiyar yau Litinin.

    Wannan na zuwa ne bayan harin da Iran ta kai arewacin Isra’ila a ranar Lahadi, wanda shi ne na farko tun bayan tsagaita wuta da aka cimma a watan Afrilu.

    Tehran ta ce harin da ta kai shi ne na farko, a jerin hare-haren da za ta shafe mako guda tana kai wa Isra'ila, wadda ta zarga da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ta hanyar kai hari Lebanon.

    Zuwa yanzu ba a bayar da rahoton samun asarar rayuka sakamakon hare-haren ba.

    Isra'ila ta mayar da martani duk da cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bukaci kada ta ta tanka Iran, saboda hakan na iya mayar da hannun agogo baya.

    Yanzu haka rahotanni na cewa dakarun tsaron Isra'ilar sun bada wata sabuwar sanarwar gargadi ga jama'a da ke cewa Iran din ta sake harbo karin wasu makamai masu linzami, don haka jama'a su yi maza su shige wuraren neman mafaka da aka tanada.

    Bayanai na cewa ita ma kungiyar Huthi da ke Yemen da Iran din ke mara wa baya ta harba wa kasar makami mai linzami wanda yanzu haka ke kan hanya.

  11. Barka da safiya!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana ta Litinin,

    Za ku iya yin tsokaci a shafukanmu na sada zumunta: Facebook, X, instagram, YouTube da kuma zaurenmu na WhatssApp.