Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 25 ga watan Yulin 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Iran ta fitar da gangar ɗanyen mai miliyan 73 a wata ɗaya

    Iran ta samu damar fitar da kusan gangar danyen mai miliyan 73 daga yankin da takunkuman Amurka suka yi wa katanga cikin kusan wata guda, bayan da Washington ta ɗan sassauta wasu takunkumai da ƙuntatawar da ta sanya kan sayar da man ƙasar.

    Daga ƙarshen watan Yuni zuwa tsakiyar watan Yuli, jiragen dakon mai na Iran da dama sun fara bayyana a ruwan gabashin Malaysia suna kan hanyarsu zuwa kasuwannin Asiya.

    Kamfanin Kepler mai bibiyar jigilar makamashi ya shaida wa BBC cewa man da aka fitar a wannan lokacin na iya kai wa darajar kusan dala biliyan shida.

    Sai dai duk da wannan gagarumar fitar da mai, rahotanni sun nuna cewa manyan masu sayen man Iran a China sun rage sayayyarsu.

    Sai dai Amurka ta janye sassaucin takunkuman da ta yi wa Iran a ranar 7 ga Yuli, bayan ta amince na ɗan lokaci da sayar da ɗanyen man ƙasar tun daga 21 ga Yuni."

  2. Iran ta ƙudiri anniyar kare tsaronta daga barazanar Amurka a mashigar Hormuz

    Iran ta bayyana cewa ta ƙuduri aniyar kare muradunta da tsaron ƙasarta tare da hana Amurka amfani da Mashigar Hormuz wajen yin barazana ga tsaronta.

    Ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, a gefen taron Majalisar Ministocin Harkokin Wajen ƙasashen mambobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO) da ake gudanarwa a Kyrgyzstan.

    A cewar kafofin watsa labaran Iran, Araghchi ya ce rashin tsaron da ake fuskanta a yanzu a Mashigar Hormuz “sakamako ne kai tsaye na karya alƙawarin da Amurka ta yi.”

    Ya ƙara da cewa Iran ta nuna muhimmancin diflomasiyya a harkokin ƙasa da ƙasa, amma a lokaci guda za ta ci gaba da kare muradunta da tsaron ƙasarta daga duk wata barazana.

    A wani ɓangaren kuma, Araghchi ya tattauna ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen Masar da Oman a ranar Alhamis kan abubuwan da suka shafi yankin.

  3. Assalamu alaikum

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Asabar.

    Aisha Babangida ke sake fatan kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Za kuma ku iya yin tsokaci a shafukanmun na sada zumunta: facebook, X, instagram, YouTube sai kuma zaurenmu na WhatssApp.