Somalia ta yi maraba da yarjejeniyar tsaron Sadiyya, Turkiyya da Pakistan
Gwamnatin Somalia ta fitar da sanarwa kan yarjejeniyar tsaron bai ɗaya da aka sanya wa hannu a yau tsakanin Saudiyya, Turkiyya da Pakistan.
Yarjejeniyar ta tanadi cewa duk wani hari da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen uku za a ɗauke shi a matsayin hari da aka kai wa dukkansu.
A cikin sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Somalia ta fitar, ta taya ƙasashen Musulmi murnar rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Sanarwar ta ce: "Ma'aikatar Tsaron Jamhuriyar Tarayyar Somalia na taya Masarautar Saudiyya, Jamhuriyar Turkiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Pakistan murnar sanya hannu kan Yarjejeniyar Makka ta Tsaron Bai Ɗaya."
Somalia ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi wajen ƙarfafa tsaro na bai ɗaya, bunƙasa haɗin gwiwar tsaro da kuma gina ingantaccen kawance da dabarun tsaro domin tunkarar barazanar tsaro da ƙasashen ke fuskanta tare.
Ma'aikatar Tsaron ta kuma bayyana cewa wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen ƙarfafa ƙoƙarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin da ma duniya baki ɗaya, tare da inganta ƙa'idojin haɗin gwiwa, haɗin kai da ɗaukar nauyi tare.
Ta ƙara da cewa yarjejeniyar za ta amfani al'ummomin yankin, tare da tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da ingantaccen tsaro.