Zaɓen Amurka da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 4/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 4 ga watan Nuwamba, 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima
  • Dattijuwa

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Fiye da rabin yara ba sa samun ilimi a makaranta a Afghanisan - MDD

    Afghanistan

    Wani rahoto na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa fiye da rabin yara da suka kai shekarun shiga makarantar firamare a Afghanistan yanzu ba sa samun ilimi a makarantu na hukuma.

    Rahoton ya kuma bayyana cewa a matakin manyan makarantun sakandare, yawan ya haura zuwa kusan kashi 80 cikin 100.

    Ƴan mata ne suka fi fuskantar matsalar, inda hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi hasashen cewa an hana 'yan mata sama da miliyan 2 da rabi na zuwa makaranta tun bayan da Taliban ta karɓe iko a ƙasar shekaru biyar da suka wuce.

    A don haka Majalisar ta Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa wannan haramcin, tare da hana mata zuwa jami’o’i, na nufin Afghanistan za ta fuskanci ƙarancin mata masu ilimi a fannonin da suka haɗa da lafiya, da ilimi, da shugabanci da sauran fannoni da ƙasa ke buƙata domin ci gabanta a nan gaba.

    Majalisar ta kuma sake kira da a bai wa dukkan yara, musamman ‘yan mata, damar samun ilimi ba tare da takurawa ba.

  2. 'Sakamakon zaɓen rabin wa’adin Amurka koma baya ne ga Trump'

    Babban jami’in harkokin tsaro na Iran, Mohsen Rezaei, ya bayyana sakamakon zaben rabin wa’adin mulki na Amurka a matsayin koma baya ta fuskar siyasa ga Shugaba Donald Trump.

    Yayin da shugabannin Iran ke nuna farin ciki da sakamakon zaben, babban jagoran addini na kasar, Mojtaba Khamenei, ya gargadi cewa matsayin Amurka kan Iran ba zai sauya ba.

    Ya ce idan Shugaba Trump ya yanke shawarar ci gaba da yakin, martanin Iran zai kasance mai muni da matukar tasiri.

    A lokaci guda kuma, akwai rahotannin da ke cewa Amurka ta aika da wani karin jirgin ruwan yaki mai dauke da jiragen sama zuwa yankin.

    Tun da farko, Shugaba Trump ya yi gargadin cewa zai iya kaddamar da sababbin hare-hare kan Tehran bayan kammala zaben.

    Bangarorin biyu sun yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman dar-dar kan dangantakar Amurka da Iran, lamarin da ke kara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin fargabar yiwuwar karin rikici.

  3. Yaƙin Iran ne ya sa jam'iyyar mu ta yi mummunar asara a zaɓen rabin wa'adi - Trump

    Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya amince cewa akwai gaskiya a ikirarin cewa yakinsa da Iran ne babban dalilin da ya sa jam'iyyar Republican ta yi mummunar asara a zaben rabin wa'adi, amma ya ce bai yi nadamar matakin da ya dauka ba.

    Trump ya yi wannan bayani ne bayan rahotannin da suka nuna cewa jam'iyyar Republican ta yi gagarumar asara a zaben, yayin da jam'iyyar Democrat ta karbe iko a duka majalisun dokokin kasar biyu - ta dattawa da kuma ta wakilai.

    Shugaban ya bayyana hakan ne bayan mataimakinsa, JD Vance, ya yi suka mai tsauri, inda ya dora alhakin sakamakon zaben kan yakin da aka yi da Iran.

    Da yake magana a wurin aikin gina sabon babban dakin liyafar Fadar White House, Trump ya ce ya san tun farko cewa yakin da Iran zai haifar da tashin farashin man fetur.

    Ya bayyana cewa karin farashin makamashi na daga cikin muhimman abubuwan da suka sa wasu Amurkawa suka kada kuri'ar kayar da jam'iyyar Republican.

    Sai dai Trump ya ce duk da haka bai yi nadamar matakin da ya dauka ba.

    Ya kuma nuna cewa yana iya yin aiki tare da 'yan Democrat bayan zaben, yana mai cewa akwai yiwuwar su fahimci juna a wasu fannoni.

    Game da yiwuwar yunkurin tsige shi daga mulki, Trump ya ce ba ya jin tsoron hakan, yana mai nuna cewa a shirye yake ya fuskanci duk wani kalubalen siyasa da zai taso.

  4. 'Masana sun ba da shawarar kara sabbin alluran riga-kafin Ebola a Kongo'

    Ebola

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce masana sun bayar da shawarar a kara sababbin alluran riga-kafin Ebola guda biyu cikin gwajin da ake ci gaba da yi a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

    Za a sanya alluran rigakafin, daya da Jami’ar Oxford tare da Serum Institute ta India suka kirkira, da kuma wata da kamfanin Moderna ya samar, a gwajin ne bayan hukumomin lafiya na Kongo sun amince da su.

    Wannan ne karon farko da za a gwada alluran rigakafin da aka kirkira musamman domin kare mutane daga kwayar cutar Ebola nau'in Bundibugyo a lokacin da ake fuskantar barkewar cutar.

    Masana suna fatan sababbin alluran za su taimaka wajen kara yaki da cutar da ta yi sanadin mutuwar dubban mutane.

    Alkaluman da aka fitar, sun tabbatar da cewa sama da mutum 10,000 suka kamu da cutar, yayin da kusan wasu 5,000 suka rasu sakamakon barkewar cutar.

  5. Ƴan Najeriya sun gaji da gafara-sa ba tare da sun ga ƙaho ba - Atiku

    Atiku

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce ƴan Najeriya sun gaji da halin yunwa da kuma rashin cika alkawura da ake yi musu.

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, ya bayyana haka ne ranar Laraba bayan isarsa Jihar Sokoto domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a ranar Alhamis.

    Ya kuma sha alwashin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi ƙasar da kuma rage tsadar rayuwa idan ya zama shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya gode wa magoya baya da suka fito domin tarbarsa a jihar, inda ya kwatanta Sokoto a matsayin jiha da ke da tarihin addini da kuma jagoranci.

    Ya ƙara da cewa kamfe ɗin sa na da kudurin kawo sauyi a ɓangaren shugabanci.

    Ya ce kaddamar da yaƙin neman zaɓensa a jihar Sokoto, lokaci ne na fara tafiyar ceto Najeriya, inda ya nuna ƙwarin gwiwar cewa ADC za ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

  6. Ƴansandan Abuja sun tsinci jariri a leda a anguwar Bwari

    Ƴansanda

    Rundunar ƴansanda a Abuja ta ce ta tsinci wani jariri da aka jefar a cikin leda a anguwar Bwari.

    Kakakin ƴansandan na Abuja, SP Josephine Adeh ce ta bayyana haka cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook ranar Talata, inda ta buƙaci al'umma da su taimaka da bayanai da za su kai ga gano mahaifiyar jaririn.

    Ta ce an tsinci jaririn ne ranar Litinin, inda aka garzaya da shi zuwa asbiti domin samun kulawa bayan samun sa cikin yanayi mara kyau.

    Adeh ta ce jaririn ya samu kwarzane a hannunsa, inda ta ƙara da cewa ƴansanda na ci gaba da ƙoƙari wajen ganin ya samu kulawar da ta dace.

    "Mun tsinci jaririn a cikin yanayi mara kyau. Jaririn namiji ne. An jefar da shi cikin wata leda kuma ya samu raunuka a jikinsa," in ji ta.

  7. Ba ni da burin kai wa Iran hari a nan kusa - Trump

    Trump

    Donald Trump ya shaida wa jaridar Financial Times cewa a halin yanzu ba shi da wani shiri na kai wa ƙasar hari a nan kusa.

    "Yanzu alamu na nuna muna samun duk abin da muke so," in ji shugaban Amurka a wata tattaunawar waya ta minti shida da ya yi da jaridar sa'o'i kaɗan kafin rufe rumfunan zaɓe a zaɓukan majalisar dokoki.

    Donald Trump ya bayyana halin da ake ciki a matsayin "mai ƙayatarwa", kuma yana magana kan killace Iran ta ruwa da kuma takunkumai, ya ce Amurka "a zahiri ba ta yaƙi" da Iran:

    "Mun kai mata hari da jiragen sama na B-2 sannan muka lalata ƙarfinta na nukiliya. Daga nan muka yi wannan gagarumin martani." Sannan ya ƙara da cewa "a zahiri ba mu daɗe muna yaƙi da su ba, watanni shida, ko ma fiye da haka."

    Da aka tambaye shi game da bayyanawa a sarari da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi cewa za a iya kai hari daga baya a wannan makon, Mista Trump ya ce: "Ina a shirye, muna a shirye, idan ya zama dole mu ɗauki mataki, gaba ɗaya muna a shirye. Amma kuma akwai yiwuwar babu wani dalili ko kaɗan na yin hakan."

  8. Shugaban Isra'ila ya soki kalaman wariyar launin fata da ke yi Larabawan ƙasar

    Isaac Herzog

    Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya soki abin da ya bayyana a matsayin kalaman wariyar launin fata da aka yi wa Larabawan Isra’ila bayan zaɓen majalisar dokoki da aka gudanar a makon da ya gabata, yayin da yake ƙoƙarin haɗa kan shugabannin jam’iyyu domin kafa gwamnati.

    Mista Herzog na tuntuɓar shugaban kowace jam’iyya domin yanke shawarar ko Firaminista Benjamin Netanyahu ko kuma ƙawancen adawa ƙarƙashin jagorancin Gadi Eisenkot ne zai fara yunƙurin kafa gwamnatin kawance.

    Falasdinawan da ke zaune a Isra’ila sun fito zaɓe da yawa, lamarin da ya ba su damar samun adadin kujeru mafi yawa a tarihinsu a majalisar dokoki.

    Dukkanin ɓangarorin biyu dai a baya sun yi watsi da yiwuwar yin haɗin gwiwa da jam’iyyun Larabawa na Isra’ila wajen kafa gwamnati.

  9. Amy Acton ta zama mace ta farko da aka zaɓa gwamnar Ohio

    A wani sabon tarihi da aka kafa a zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka, Amy Acton ta zama mace ta farko da aka zaɓa a matsayin gwamnar jihar Ohio.

    Amy Acton ta jam'iyyar Demokrats ta doke Vivek Ramaswamy ta Republican wata fafatawa mai zafi kan kujerar gwamnan wannan jiha da ke yankin tsakiyar yammacin Amurka.

    Baya ga Acton, wasu matan da suka kafa tarihi a ranar Talata sun haɗa da Deb Haaland, wadda ta zama mace ta farko daga cikin al’ummar asalin Amurka da aka zaɓa a matsayin gwamnar jihar New Mexico, da kuma Keisha Lance Bottoms, wadda ta zama mace baƙar fata ta farko da aka zaɓa a matsayin gwamna a wata jiha bayan nasararta a jihar Georgia.

  10. Masu tunanin samun sauyin ƙiyayyar Amurka ga Iran sun yi kuskure - Mojtaba

    Hoto

    Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce waɗanda ke tunanin sauye-sauyen siyasar Amurka za su kawo canji a “ƙiyayyar Amurka ga Iran” suna “cikin babban kuskure”.

    Khamenei ya kuma yi barazanar cewa idan Amurka ta sake kai hari kan Iran, martanin da za a mayar “zai ƙaru zuwa wani mataki mafi girma”.

    Jagoran Addinin, wanda ya gaji mahaifinsa Ali Khamenei wanda aka kashe a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai ranar 28 ga Fabrairu, bai fito bainar jama'a ba tsawon watanni.

    Kalaman sun fito ne cikin wani rubutaccen saƙo mai shafuka shida da aka fitar a yau domin tuna mamayar ofishin jakadancin Amurka da aka yi a Tehran a shekarar 1979.

  11. Wasu shugabannin duniya na maraba da nasarar Demokrats

    Trump

    Ba abin mamaki ba ne ganin cewa wasu shugabannin ƙasashen da Donald Trump ya taɓa suka ko nuna adawa da su na maraba da gagarumar nasarar da jam'iyyar Democrat ta samu a zaɓen rabin wa'adi.

    • Firaministan Sifaniya, mai ra'ayin sassauci, Pedro Sanchez, ya ce Amurkawa sun zaɓi kawar da ƙiyayya, musun sauyin yanayi da kuma fifita masu gata a cikin al'umma.
    • Shi ma takwaransa Jonas Støre, firaministan ƙasar Norway, wadda Trump ya soko a makonnin baya saboda ba ta ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ba, ya ce wasu sabbin muryoyi na tasowa a Amurka waɗanda suka fi dacewa da manufofin birnin Oslo.
    • Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda Trump ya zarga da aikata kisan kare dangi kan fararen fata, ya ce zaɓukan za su kawo sabon zamani a dangantakar ƙasashen duniya.
    • A wani ɓangaren kuma, mataimakiyar shugabar Majalisar Tarayyar Turai, Christel Schaldemose, ta ce tana da fata cikin taka-tsantsan cewa sakamakon zaɓen na iya haifar da ƙarin goyon baya ga Ukraine.
  12. Amurkawa sun nuna wa Trump cewa ba sa son yaƙi - Iran

    Mohammad Bagher Ghalibaf

    Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, wanda ke cikin manyan masu tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran, ya yi tsokaci kan sakamakon zaɓen tsakiyar wa'adin mulki da aka gudanar a Amurka.

    "Saboda lamiri ko kuma tsadar rayuwa, Amurkawa sun nuna ba sa son yaƙi, kuma muna goyon bayan wannan mataki," kamar yadda ya rubuta a shafin X.

    "Idan gwamnatin Amurka ta yi watsi da ra'ayin jama'arta domin yi wa wasu ƴan ƙasashen waje da masu yin barazana hidima, yanzu ta fahimci Amurkawa ba sa goyon bayan hakan''.

    Da yake magana da gidan talabijin na Fox News a baya, Donald Trump ya ce "dole ne mu yi wani babban abu" lokacin da aka tambaye shi kan rahotannin da ke cewa Amurka na shirin kai wasu hare-hare kan Iran, yana mai ƙara da cewa hakan na iya haɗawa da "mummunan hari".

  13. Demokrats na kafa sabon tarihi a zaɓen Amurka

    Obama

    Democrat na kan hanyar ƙwace kujerun Majalisar Dattawan jihohin South Carolina da Kansas da Texas, waɗanda dukkansu a halin yanzu suna hannun jam'iyyar Republican kuma haka lamarin yake tsawon shekaru da dama.

    Rabon da jihar Kansas ta zaɓi ɗan Democrat zuwa Majalisar Dattawa yau kusan shekara 100 kenan da suka gabata, wato tun a shekarar 1932.

    Hakan ya faru ne a lokacin babban matsin tattalin arziki, kuma a shekarar ce ɗan jam'iyyar Democrat Franklin D Roosevelt ya samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa.

    Ana kuma hasashen cewa ƴan takarar Democrat za su yi nasara a zaɓen majalisar dattawa da kuma na gwamna a jihar Texas, kuma duka biyun za su kasance karo na farko tun farkon shekarun 1990.

    Ɗan jam'iyyar Democrat na ƙarshe da aka zaɓa a matsayin gwamnan Texas ita ce Ann Richards a shekarar 1991.

    Ta yi wa'adin shekaru huɗu kafin ɗan jam'iyyar Republican George W Bush ya kayar da ita a zaɓe, wanda daga baya ya zama shugaban Amurka, bayan kammala wa'adinsa.

    Haka kuma, karo na ƙarshe da jam'iyyar Democrat ta lashe kujerar majalisar dattawa a jihar South Carolina shi ne a shekarar 1998.

  14. Demokrats ta ƙwace jihar Ohio daga hannun Republican

    yartakara
    Bayanan hoto, Ƴartakarar gwamnan Demokrats Amy Acton na kan hanyar samun nasara

    Wannan sakamako ne mai ban mamaki kuma mai muhimmanci ga jam'iyyar Democrat a jihar Ohio, wadda ake hasashen za ta ƙwace kujera a Majalisar Dattawan Amurka tare da kuma karɓe kujerar gwamna daga hannun jam'iyyar Republican.

    Jihar ta kasance kagarar jam'iyyar Republican a tsawon lokacin mulkin Donald Trump, amma jam'iyyar Democrat ta karya wannan rinjaye nata a jihar.

    Wannan ya nuna girman nasarar da jam'iyyar ta samu a daren da ya gabata, domin jihar na daga cikin wuraren da aka fafata sosai kuma aka yi takara mai zafi.

    Trump ya ziyarci Ohio sau uku a lokacin wannan yaƙin neman zaɓe, saboda damuwar da ke akwai game da yadda jam'iyyarsa ke fuskantar.

    An bar kujerar Majalisar Dattawan ne babu mai riƙe da ita shekaru biyu da suka gabata, lokacin da JD Vance ya zama mataimakin shugaban ƙasa.

  15. Labarai da dumi-dumi, Demokrat na kan hanyar lashe zaɓen gwamnan jihar Texas

    Gina Hinojosa

    Jam'iyyar hamayya ta Demokrats na kan hanyar lashe zaɓen gwamnan jihar Texas.

    Kafar yaɗa labarai ta CBS News ta ce ƴartakarar jam'iyyar Gina Hinojosa na kan gaba a sakamakon zaɓen da ke fitowa.

    Jam'iyyar Republican ce dai ke mulkin jihar tsawon shekaru

  16. Yaƙin Iran ne ya janyo wa jam'iyyarmu rashin nasara - Trump

    Trump

    Shugaban Amurka ya ce yaƙin Iran ne ya janyo wa jam'iyyarsa ta Republican gagarumar koma-baya a zaɓen tsakiyar wa'adi na ƙasar.

    Kawo yanzu dai jam'iyyar ta rasa rinjaye a duka majalisun dokokin ƙasar biyu.

    Yayin wata hira da kafar yaɗa labarai ta Fox News, Shugaba Trump ya ce yaƙin ya haddasa tashin farashin gas a Amurka wanda kuma shi ne ya janyo wa Repblican baƙin jini.

    ''Mutane suna ji a jikinsu saboda suna sayen gas da tsada'', in ji shi.

    Shugaban na Amurka ya kuma ce dole Amurka ta yi wani abu kan Iran

    "Ba za mu bari su mallaki makamin nukiliya ba," a cewar Shugaba Trump.

  17. A shirye nake na yi aiki da Demokrats - Trump

    Trump

    Yayin da ƴan takarar jam'iyyar Democrat ke ci gaba da samun nasara a zaɓukan tsakiyar wa'adin mulkin Amurka, Shugaba Donald Trump ya ce zai karɓi tsakamakon zaɓen.

    Cikin wata hira da Jaridar New York Times, Shugaba Trump ya ce a shirye yake "ya amince da wannan sakamakon", kuma yana shirye ya yi aiki tare da jam'iyyar adawa.

    "Gaskiya, muna sa ran yin aiki tare da su," in ji shi.

    "Mai yiwuwa mu cimma wata matsaya tare."

  18. Ministan sufurin Sifaniya ya ajiye muƙaminsa ya kuma haƙura da takara saboda hatsarin jirgin ƙasa

    Ministan sufurin Sifaniya

    Ministan Sufuri na Spain, Óscar Puente, ya yi murabus, kwanaki shida bayan hatsarin jiragen ƙasa wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 69 tare da jikkata wasu da dama.

    Ya sanar da matakin nasa a Majalisar Dokoki, bayan ya bayar da bahasi kan bala'in da ya faru a ranar Larabar da ta gabata kusa da garin Urda, da ke kudancin babban birnin ƙasar, Madrid, inda wani jirgin ƙasa ya buga bayan wani jirgin da ke tsaye.

    "Wani ministan sufuri a ƙasa irin Spain ba zai iya ci gaba da zama a muƙaminsa ba bayan hatsari biyu masu muni cikin ƙasa da shekara guda," in ji shi, yana mai nuni da hatsarin da ya faru a watan Janairu a kan wannan layin dogo, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 46.

    jiragen da suka yi hatsari

    Hatsarin da ya faru a makon da ya gabata na ɗaya daga cikin munanan bala'o'in jirgin ƙasa mafi muni a tarihin Turai a wannan zamani, kuma shi ne mafi munin hatsarin jirgin ƙasa a Spain tun shekarar 2013.

    Puente ya sanar da matakin nasa ne a ƙarshen dogon zaman majalisar dokoki da aka yi a yammacin ranar Talata, inda ya yi bayani kan sabbin matakan tsaron layukan dogo, sannan kuma ƴan adawa suka yi masa tambayoyi masu tsauri.

    Ministan ya kuma sanar da janye takarar majalisar dokokin ƙasar da yake a zaɓen ƙasar da ke tafe

    "Ba wai kawai zan sauka daga muƙamina na ministan sufuri ba, na kuma janye daga takarar majalisar dokokin Sifaniya a zaɓe mai zuwa."

  19. Demokrats na kan hanyar ƙwace majalisun dokokin Amurka

    Obama
    Bayanan hoto, Jagoran jam'iyyar Demokrats, Barack Obama

    Babbar jam'iyyar hamayya ta Demokrats a Amurka na kan hanyar ƙwace iko da majalisun dokokin Amurka biyu.

    Yayin da sakamakon zaɓen ke ci gaba da fitowa Demokrats ta samu kureru 53 cikin 100 na majalisar dattawan ƙasar.

    Yayin da majalisar wakilai zuwa yanzu ta samu kujeru 224, yayin da Republican ta samu 134 cikin kujeru 358 da aka kammala fitar da sakamakonsu a yanzu.

    Zuwa yanzu dai ana dakon sakamakon zaɓen kujerun majalisar wakilai 77.

    Jagoran jam'iyyar, wanda kuma shi ne tsohon shugaban ƙasar, Barack Obama ya ce sakamakon alama ce da ke nuna cewa ƙarara Amurkawa na buƙatar chanji.

  20. Jam'iyyar Trump na shan mummunan kaye a zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka

    Trump

    Jam'iyyar Republican ta Shugaba Trump na ci gaba da shan gagarumin kaye a zaɓukan tsakiyar Amurka.

    Yayin da sakamakon zaɓen ke ci gaba da fitowa, jam'iyyar hamayya ta Demokrats ta kama hanyar ƙwace rinjayen majalisar dattawa da ta wakilan ƙasar.

    Kafin wannan zaɓen dai jam'iyyar Republican ce kje da rinjaye a duka majalisun biyu.

    Tun kafin zaɓen ne dai masu nazarin siyasar ƙasar suka yi hasashen Demokrats za ta ƙwace iko da majalisar wakilai, amma ba a yi zaton za ta ƙwace iko a majalisar dattawa ba.