Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 22 ga watan Yunin 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Keir Starmer yayi murabus daga muƙamin firaministan Birtaniya

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da cewa zai sauka daga muƙaminsa na jagoran ƙasar da kuma shugaban jam’iyyar Labour, bayan ya fuskanci matsin lamba daga cikin jam’iyyarsa.

    Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar, inda ya ce ya riga ya sanar da Sarkin ƙasar, Charles game da matakin da ya ɗauka.

    Starmer ya ce kafin ya karɓi jagoranci, jam’iyyar Labour tana cikin wani hali na rauni a fannonin siyasa da tattalin arziki. Duk da wannan, ya jaddada cewa ya yi aiki tukuru wajen sauya alkiblar jam’iyyar, inda ya magance wasu manyan matsaloli da suka addabe ta, ciki har da zarge-zargen wariyar addini, tare da dawo da martaba a fannoni kamar tsaro da tattalin arziki.

    Ya kuma bayyana cewa a yanzu jam’iyyarsa tana tambayar ko shi ne mafi dacewa da zai jagorance ta zuwa babban zaɓe mai zuwa

    Starmer ya kuma ce zai ci gaba da riƙe mukamin firaminista na ɗan lokaci har sai an zaɓi sabon shugaban jam’iyyar kafin dawowar majalisar dokoki daga hutun bazara.

    Ya kuma yi alkawarin tabbatar da mika mulki cikin natsuwa, tare da mika cikakken goyon baya ga wanda zai gaje shi, yayin da ya gode wa abokan aikinsa da ma’aikatan gwamnati kan gudunmawar da suka bayar.

  2. An kammala zagayen farko na tattaunawar Iran da Amurka a Switzerland

    An kammala zagayen farko na tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka a Switzerland, inda tawagar Iran ta fice daga wurin bayan zaman farko.

    Masu shiga tsakani wato Qatar da Pakistan sun bayyana cewa za a ci gaba da tattaunawar a cikin makon nan.

    A cikin sanarwar haɗin gwiwa, ƙasashen biyu sun ce ɓangarorin sun cimma matsaya kan wata hanya da za a bi domin kai ga yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60 masu zuwa.

    Haka kuma sun bayyana cewa an amince da kafa wata hanya ta dakatar da yaƙi a Lebanon, domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

    Bugu da ƙari, masu shiga tsakani sun ce Iran da Amurka sun amince da ƙirƙirar wata hanyar sadarwa kai tsaye domin kauce wa rikice-rikice da rashin fahimta a mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci ga jigilar kayayyaki da makamashi a duniya.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa an samu “gagarumin ci gaba” a tattaunawar, inda ya ce an ɗage takunkumin fitar da man fetur da na petrochemical da aka sanya wa ƙasar.

    Ya ƙara da cewa an saki wasu daga cikin kadarorin Iran da aka ƙwace yana mai jaddada cewa hakan na daga cikin manyan nasarorin tattaunawar.

  3. Nijar ta bayyana sharuɗɗanta na buɗe iyaka da Benin

    Gwamnatin sojin Nijar ta bayyana cewa buɗe iyakarta da Benin zai dogara ne kan wasu muhimman sharuɗɗa da suka haɗa da sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsaro da za ta hana kowace ƙasa amfani da ƙasarta wajen kai hari da tabbatar da cikakken bayani kan duk wani sojin ƙetare da ke yankin iyaka da kuma kafa tsarin musayar bayanan sirri tsakanin ƙasashen biyu.

    Ta ce ba za ta sauka daga waɗannan sharuɗɗan ba yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakan

    Wannan ya biyo bayan wata ganawa da aka gudanar a Cotonou tsakanin jami’an ƙasashen biyu, inda aka tattauna hanyoyin dawo da dangantaka ta yau da kullum.

    Jami’an Nijar sun ce tattaunawar ta kasance mai ma’ana, kuma ta samar da wata kafa da za ta kai ga inganta alaƙar diflomasiyya.

    Amma sun jaddada cewa batun tsaro da na soji su ne suka fi mayar da hankali a kai, la’akari da rashin yarda da juna da ke tsakanin Niamey da Cotonou.

    Dangantakar ƙasashen biyu ta taɓarɓare ne tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a watan Yulin 2023, inda Nijar ta zargi Benin da marawa wasu ƙasashen waje baya wajen kawo cikas.

    Nijar ta kuma danganta wasu hare-haren tsaro da suka faru, ciki har da kai hari filin jirgin Niamey, da taimakon waje, zargin da Benin ta musanta.

    Duk da haka, ƙasashen biyu sun fara sabuwar tattaunawa domin farfaɗo da kasuwanci da inganta tsaro.

  4. An ɗage mana takunkumin man fetur tare da sakin wasu kadarorinmu - Iran

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da ƙasarsa ke yi da Amurka a Switzerland.

    Ya ce an ɗage takunkumin da aka sanyamu kan fitar da man fetur da kayan petrochemical, sannan an dakatar da toshe ruwa da aka yi wa Iran.

    Araghchi ya kuma ce an saki wasu daga cikin kadarorin Iran da aka ƙwace a kasashen waje, tare da fara aiwatar da wani babban shiri na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

    Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya jaddada cewa matakan na daga cikin nasarorin tattaunawar.

    Ministan ya gode wa ƙasashen Pakistan da Qatar bisa rawar da suka taka wajen shiga tsakani, yana mai cewa hakan ya haifar da babbar nasara wajen ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Lebanon.

    Ya ce daga cikin matakan da aka tsara akwai kafa wata hanya ta tabbatar da dakatar da faɗa a Lebanon a matsayin gwajin farko na yarjejeniyar.

    A ƙarkashin yarjejeniyar tsakanin Iran da Amurka, batutuwan da suka haɗa da dakatar da yaƙi a dukkan fannoni da sassauta takunkumi kan fitar da mai, da kuma sakin kadarorin da aka ƙwace na daga cikin manyan abubuwan da ake tattaunawa a kai, yayin da ake ci gaba da tattaunawa domin cimma yarjejeniya ta ƙarshe.

  5. An sanar da jadawalin jana’izar jagoran addinin Iran, Ayotallah Khamenei

    Mahukunta a Iran sun sanar da shirin gudanar da jana’izar marigayi jagoran ƙasar, Ayotallah Ali Khamenei, wanda aka kashe a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila a watan Fabrairu.

    Rahotanni sun nuna cewa za a fara gudanar da bikin jana’izar ne a babban birnin Tehran daga ranar 4 ga watan Yuli, inda za a yi bukukuwan ban kwana na kwanaki da dama.

    Bayan haka kuma, za a ci gaba da jana’izar a birnin Qom, kafin a kammala da binne gawarsa a Mashhad, mahaifarsa, ranar 9 ga watan Yuli.

    Hukumar da ke kula da shirye-shiryen jana’izar ta ce ana sa ran dubban jama’a za su halarci waɗannan bukukuwa a fadin ƙasar, sakamakon muhimmancin da marigayin ya ke da shi a siyasar Iran da kuma duniyar Shi’a.

    Sai dai rahotannin da ke cewa za a gudanar da jana’izar a Najaf da Karbala ba su samu tabbaci daga manyan kafofin labarai ba, duk da cewa an gudanar da wasu gangamin jana’iza na alama a Najaf a baya.

  6. Assalamu alaikum

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye.

    Kamar kullum, yau ma za mu muku labaran abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana ta Litinin.

    Za ku iya yin tsokaci a shafukanmu na sada zumunta: Facebook, X, instagram, YouTube da kuma zaurenmu na WhatssApp.