Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 30 ga watan Yulin 2026.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello

  1. MDD ta tsawaita takunkumai kan ƙungiyoyin ƴanbindiga a Afirka ta Tsakiya

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsawaita takunkumi kan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsawaita takunkumin da ta ƙaƙabawa ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da kuma mutanen da ake zargi da kawo cikas ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yayin da rikici ke ci gaba da ta'azzara a ƙasar.

    A ƙuri'ar da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa a ranar Laraba, an amince da ƙudurin da ya wajabta wa ƙasashe mambobi su ɗauki matakan hana kai ko sayar da makamai da sauran kayan yaƙi ga ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

    Takunkumin, wanda aka tsawaita har zuwa 31 ga Yulin 2027, ya kuma haɗa da haramta wa waɗanda abin ya shafa yin tafiye-tafiye da kuma ƙwace kadarorinsu.

    Da yake jawabi a zaman, wakilin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Marius Aristide Hoja Nzessioué, ya yi maraba da tsawaita takunkumin.

    Sai dai ya kuma yi kira ga ƙasashe da su tabbatar da bin matakan takunkumin yadda ya kamata, yana mai nuna takaicinsa cewa har yanzu 'yan tawaye na samun makamai duk da waɗannan matakan.

    A lokacin da rikicin cikin gida ya ɓarke a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarar 2013, Majalisar Ɗinkin Duniya ta kakaba wa ƙasar takunkumin hana shigo da makamai. Tun daga lokacin ake ci gaba da sabunta takunkumin tare da ɗora takamaiman hukunci kan wasu mutane da ake dangantawa da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ayyukansu.

  2. Za mu tabbatar Iran da Amurka sun sake komawa teburin sulhu - Pakistan

    Pakistan ta ce har yanzu tana ƙoƙarin dawo da Iran da Amurka kan teburin tattaunawa domin jaddada yarjejeniyar Islamabad.

    "Burinmu shi ne mu tabbatar da cewa dukkan ɓangarorin sun koma kan yarjejeniyar ta Islamabad," in ji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Pakistan, Tahir Andrabi, yayin da yake ganawa da manema labarai a yau.

    A cewarsa, Pakistan ta fata ƙasashen biyu su "cika alƙawurransu gaba ɗaya na amfani da ke ƙunshe a yarjejeniyar."

    Amurka da Iran dai sun sanar da cewa sun yi watsi da wannan yarjejeniya, inda suka koma yi wa juna luguden wuta.

    Pakistan dai ce ta shige gaba domin ƙulla yarjejeniyar ta Islamabad, wadda aka sanya wa hannu domin kawo ƙarshen yaƙin.

  3. Mun lalata jiragen yaƙin Amurka ƙirar F-35 guda uku a Jordan - Iran

    Dakarun juyin-juya-halin Iran wato IRGC sun ce sun lalata gaba ɗaya jiragen yaƙin Amurka kirar F-35 guda uku, sannan ta yi wa wasu guda uku mummunar ɓarna a wani harin makamai masu linzami da ta kai kan sansanin sojin sama na Al-Azraq da ke Jordan.

    Sai dai har zuwa yanzu, Amurka ko Jordan, ko kuma wasu majiyoyi masu zaman kansu, ba su tabbatar da wannan ikirari ba.

    Sashen hulɗa da jama'a na IRGC ya bayyana cewa harin martani ne ga hare-haren sama da Amurka ta kai kan gidaje biyu a tsibirin Qeshm, inda ta ce mutane uku na gida, ciki har da wani yaro, suka mutu, yayin da wasu yara biyu suka jikkata.

    IRGC ta kuma yi ikirarin cewa wasu jami'an sojin Amurka da ma'aikatan fasaha sun mutu a harin da aka kai kan rumfar da ake ajiye da gyaran jiragen yaƙi a sansanin Al-Azraq, amma ba ta bayyana adadin waɗanda suka mutu ba.

    A baya, sojojin Jordan sun sanar da cewa tsarin kariyar sararin samaniyarsu ya tare tare da lalata makamai masu linzami guda biyar da aka harba daga Iran, kuma sun ce harin bai yi sanadin asarar rayuka ba.

    Har zuwa yanzu, Amurka ba ta fitar da wani rahoto da ke tabbatar da lalata jiragen yaƙin F-35 ko kuma asarar rayukan sojojinta a wannan harin ba.

  4. 'Yadda na yi auren Mutu'a na tsawon shekara biyu'

    Yayin da ake ci gaba da musayar yawu dangane da halasci ko rashin halascin auren mutu'a wata wanda ta yi auren mutu'a na tsawon shekara biyu ta shaida wa BBC yadda al'amarin ya faru.

    A ƙarshen makon da ya gabata ne dai wani bidiyo na limamin babban masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maƙari ya nuna yadda malamin ke magana kan wata amsar tabbaya da ya ce ya bai wa ɗalibansa da ke harkokin rayuwa a ƙasar waje.

  5. 'Mun haɗa kuɗin fansa sama da miliyan 150 amma ba a sako ƴan'uwanmu ba'

    Kimanin wata biyar kenan bayan da ƴan bindiga suka dira a ƙauyen Woro na jihar Kwara, inda suka yi wa mutane ɗaya daga cikin kisan gilla mafi muni da aka gani a baya-bayan nan a Najeriya.

    Ɓarnar da ƴan bindigar suka yi ta ƙazanta, lamarin da ya janyo hankalin ɗaukacin al'ummar Najeriya da ma masu sanya ido kan harkar tsaro a ƙasashen ƙetare.

  6. Iran ta sake kai sabbin hare-hare a Kuwait da Jordan

    Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan wurare daban-daban a yankin gabas ta tsakiya, bayan sojojin Amurka sun bayyana cewa sun kai jerin hare-haren sama da suka kai kan Iran cikin daren jiya.

    Kuwait ta ce wani makami mai linzami da Iran ta harba ya faɗa kan wani gini a arewacin ƙasar, inda ya kashe mutum ɗaya.

    Sojojin Jordan kuwa sun ce sun harbo makamai masu linzami guda biyar da Iran ta harba.

    Tun da farko, sojojin Amurka sun ce sun kai hari kan wurare da dama mallakin rundunar juyin-juya-halin Iran wato IRGC, a matsayin martani ga harin makamai masu linzami da Iran ta kai ranar Talata kan wani sansanin sojojin Amurka da ke Jordan.

    Kafofin yaɗa labarai na Iran sun ce hare-haren na baya-bayan nan da Amurka ta kai sun kashe mutane uku, ciki har da wani yaro.

  7. 'Hana yara shan sukari na inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu'

    Wani sabon bincike da aka gudanar ya gano shaidar da ke nuna cewa rage yawan shan siga ga yara daga shekara biyu na matuƙar taimakawa wajen kare lafiyar ƙwaƙwalwarsu na tsawon gomman shekaru.

    Binciken wanda jami'ar kimiya da fasaha ta Hong Kong ta gudanar ya yi nazari kan tasirin sukarin a Birtaniya bayan yaƙin duniya na biyu.

    Sakamakon ya nuna mutanen da suke yara a lokacin yaƙin da suka taƙaita shan sukari sun samu kariya daga kamuwa da cutar mantuwa da kusan kashi ashirin da uku cikin ɗari.

  8. Amurka za ta fitar da dala miliyan 600 domin tallafawa allurar riga-kafi

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka za ta fitar da kudade har dala miliyan dari shida nan ba da jimawa ba domin Ƙungiyar Gavi, wacce ke taimaka wa kasashe masu tasowa wajen samar da allurar riga-kafi.

    Tunda farko Sakataren lafiyar Amurka Robert Kennedy ne ya riƙe kuɗaden bayan ya yi amannar cewa Gavi na amfani da sinadaran da aka daina amfani da su wadanda ke da haɗari ga lafiyar dan'adam.

    Sai dai Gavi ta ce matakin nasa ya jefa miliyoyin yara cikin hadarin kamuwa da cututtukan da ake iya ɗauka.

  9. Rasha ta kai mana hare-hare - Ukraine

    Rundunar sojin Ukraine ta ce Rasha ta kai mata hare-hare a yankuna uku na ƙasar.

    Hakan na zuwa ne bayan gargadin da shugaba Zelensky ya yi na cewa Rashar na shirin kai masu gagarumin hari.

    Wakiliyar BBC ta ce magajin garin birnin Kyiv ya ce Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami, inda ya ce an samu rahoton gobara a gudunma biyu na birnin.

    Ya zuwa yanzu mutum biyar ne ciki har da yara biyu suka rasu sakamakon hare-haren, sai kuma gidaje da suka rushe.

  10. Amurka ta ce ta kai hare-hare masu ƙarfi a Iran

    Rundunar sojin Amurka ta ce ta fara kai sabbin jerin hare-hare masu ƙarfi da tasiri kan Iran.

    Hakan na zuwa ne bayan da shugaba Trump ya sha alwashi tare da yin alƙawarin yi wa Iran din luguden wuta mafi muni.

    Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa an kai hari kan matatun man fetur biyu na ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce an samu rahotannin fashewar abubuwa a sassa daban-daban na Iran Iran ma ta bada tabbacin kai hare-hare kan kadadarorin Amurka dake Jordan da kuma kan jiragen ruwa a mashigar Hurmuz.

  11. Farawa

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa, barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.