Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 14/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 14/07/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ƙasashen Gulf za su fara biyan mu kan tsaron da muke ba su - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dole ne ƙasashen yankin Gulf su biya Amurka saboda kariyar da za ta ba su daga hare-haren Iran.

    Iran ta fara kai hare-hare kan sansanonin sojij Amurka da ke ƙasashen yankin, a matsayin martani kan hare-haren Amurka.

    Yayin da yake magana game da batun a Fadar White House, Shugaba Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da bai wa ƙasashen na yankin Gulf tsaro, amma kuma dole ne su biya.

    "Ina so su biya, saboda muna aikin kare yanki mai arziki ne a duniya, don haka ya kamata a biya mu wannan aiki,'' in ji shi.

    Shugaban na Amurka ya ci gaba da cewa ƙasashen na buƙatar taimakon Amurka.

    "Za mu samu kuɗi daga ƙasashe irin su Saudiyya da UAE da Qatar da Bahrain da Kuwait da sauran ƙasashen, Ba mu muke buƙatarsu ba, su ne suke buƙatarmu. Mu muna da wadataccen mai, ciki har da na Venezuela,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Shugaban na Amurka ya kuma bayyana cewa ƙasarsa za ta rufe tasoshin ruwan Iran.

    Ya kuma bayyana cewa za a ɗora wa kowane jirgin dakon mai da zai wuce ta mashigar Hirmzu harajin kashi 20.

  2. Iran ta ce ta kai hare-haren kan manyan jiragen dakon mai a mashigar Hormuz

    Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce suna kai hare-hare kan manyan tankokin dakon mai a mashigar Hormuz da kuma wuraren da ke da alaƙa da Amurka a ƙasar Bahrain, yayin da rikici a tsakanin Iran da Amurka ke ƙara kamari.

    Dakarun sun ce sun lalata wasu jiragen ruwan dakon mai bayan sun yi watsi da gargaɗin da aka yi musu tare da kashe na’urorin da ke nuna inda suke zirga-zirga.

    A nata ɓangaren, rundunar sojin Amurka ta ce dakarunta sun kai hare-hare kan wuraren da sojoji suke a sassan Iran.

    Rundunar ta kuma ce a yanzu suna da sojoji dubu 50 da aka jibge a yankin Gabas ta Tsakiya.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.