'Tattaunawa tsakanin wakilan Trump ta Putin ta yi kyau'
Wani jami'in Fadar White House ya bayyana tattaunawar da aka yi a Kremlin tsakanin Shugaba Putin da manyan wakilan Donald Trump kan yaƙin Ukraine a matsayin batu mai muhimmanci.
Tun da farko Yuri Ushakov wani mataimakin Putin ya ce ya yin tattaunawar ta sa'o'i uku Mista Putin ya jaddada bukatar janye batun da ya haifar da rikicin.
Har yanzu akwai alamar bai watsar da bukatunsa na tsattsauran ra'ayi ba ɓangarorin biyu sun kuma duba yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin Rasha da Amurka don aiwatar da wasu manyan ayyuka.
Wakilin BBC ya ce wakilan Amurkan yanzu sun nufi birnin Kyiv don ganawa shugaba Zelensky