An bude makarantar sakandaren ƴansanda ta farko a Iran
Iran ta buɗe makarantar sakandaren kwana ta farko ta ƴansanda a birnin Tehran. Jami'ai sun ce makarantar za ta haɗa karatun sakandare na yau da kullum da horo na musamman kan lafiyar jiki da ƙirƙirarriyar basira da amfani da makamai da sauransu.
A cewar kamfanin dillancin labarai na IRNA, shirin da aka keɓe musamman domin maza an tsara shi ne domin gano ɗalibai masu hazaƙa tun da wuri, da kuma samar da hanyar horas da ƙwararrun ma'aikata da kuma kwamandojin ƴansanda na nan gaba.
Rahotanni sun ce shirin na nuna yadda ake ƙara mayar da hankali kan sake gina tsarin tsaron Iran, bayan asarar rayukan jami'an tsaro sakamakon yakin.
An sanya wa makarantar sunan Manjo Janar Mohammad Bagheri, tsohon Shugaban Hafsoshin Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda aka kashe a ranar 13 ga Yuni, 1404.





























