An yi jana’izar mutum 16 da aka kashe a wani hari a Benue

Asalin hoton, Getty Images
An gudanar da jana’izar jama’a a ranar 8 ga watan Agusta a ƙauyen Efeyi da ke jihar Benue, arewa ta tsakiyar Najeriya, inda aka yi wa mutum 16 da ake zargin wasu ƴanbindiga suka kashe jana’iza, kamar yadda jaridar Vanguard mai zaman kanta ta ruwaito.
Rahotanni sun ce an kashe mutanen ne lokacin da aka kai hari a ƙauyen a ranar 28 ga watan Yuli, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici tare da tilasta wa da dama daga cikinsu tserewa domin tsira da rayukansu.
Mazauna kauyen sun bayyana harin a matsayin mummunan hari da aka kai ba tare da wani dalili ba.
Harin ya faru ne watanni bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama a wasu kauyuka da ke cikin gundumar Ugboju, a ƙaramar hukumar Otukpo.
A wajen jana’izar, ’yan uwa, shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da malaman addini sun hallara domin yin bankwana da wadanda aka kashe.
Wani limamin Cocin Katolika ne ya jagoranci addu’o’in jana’izar, kafin a sauke akwatunan gawarwakin wadanda aka kashe cikin kaburburansu, yayin da ’yan uwa da makusanta ke kuka da alhini.
Jihar Benue, wadda ke yankin Middle Belt na Najeriya, na fama da rikice-rikice da suka samo asali musamman daga hare-haren ramuwar gayya da satar shanu tsakanin makiyaya, wadanda galibinsu Musulmi ne, da manoma, wadanda galibinsu Kiristoci ne.


