Ba za a buɗe mashigar Hormuz ba har sai mun ga dama - Iran
Iran ta ce za ta buɗe mashigar Hormuz ne kawai idan ta ga damar yin hakan.
A cikin wani jawabi da ya yi, shugaban Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Dokokin Iran, Ebrahim Azizi, ya ce wannan abu ne da yake bayyane ƙarara.
A cewarsa, "Iran na nuna wa Amurka ƙarfinta domin tabbatar da cewa barazanar da take yi ba ta banza ba ce."
A cikin ƴan kwanakin nan, Amurka ta kai hare-hare da dama a kudancin Iran, tana mai cewa manufarta ita ce lalata ikon Iran na dasa nakiyoyi a Mashigar Hormuz da kuma kai hare-hare kan jiragen ruwa.
Sai dai Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Jordan da Kuwait da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)