Dangote, Habasha da Djibouti za su gina bututun mai na dala miliyan 600

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Attajirin Afirka Aliko Dangote da gwamnatocin Habasha da Djibouti sun cimma yarjejeniyar gina bututun man fetur da rumbun ajiyarsa da za su haɗa ƙasashen biyu, a wani aiki da zai laƙume dala miliyan 600.
Aikin zai haɗa da gina bututun mai mai tsawon kilomita 120 da zai haɗa tashar jiragen ruwa ta Damerjog a Djibouti zuwa cibiyar rarraba mai da ke Dewele a Habasha. Haka kuma, za a gina rumbunan da za su iya ɗaukar kusan lita miliyan 400 na man fetur.
Ana sa ran fara aikin cikin watanni 18.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ce bututun zai rage lokacin da ake ɗauka wajen jigilar mai daga tashar jiragen ruwa ta Djibouti zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha, daga kwanaki biyar zuwa kwana ɗaya.
A matakin farko, za a riƙa jigilar muhimman albarkatun man fetur, ciki har da man jirgin sama, dizal da fetur.
Da yake jawabi a bikin ƙaddamar da aikin, Dangote ya ce aikin zai ƙarfafa makamashi a Habasha tare da inganta tsarin samar da man fetur na ƙasar.





















