Ana zanga-zanga a Kenya kan shirin buɗe cibiyar Ebola ta Amurka a ƙasar
Zanga-zanga ta ɓarke a garin Nanyuki da ke Kenya game da shirin gina cibiyar killace masu Ebola ta Amurka a sansanin sojin sama na Laikipia.
Mazauna garin sun yi tattaki inda suke ihu, wasu kuma sun toshe tituna lamarin da ya sa ƴansanda suka harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.
A cewar masu zanga-zangar, cibiyar na iya jefa rayukan mutanen ganin cikin haɗari da kuma yiwuwar ɓarkewar cutar.
Joyce Wangui, wata mazauniyar Nanyuki ta ce "abin takaici ne yadda gwamnati ta nuna rashin damuwarta game da lafiyar ƴaƴanmu da al'ummarmu. Ba ma son a gina wannan cibiya a Laikipia."
Marlin Ndegwa, wani shugaban al'ummar yankin ya ce masu zanga-zangar sun ɗauki matakin ne domin su nuna rashin goyon bayansu ga gina cibiyar Ebola a garin.
A makon da ya gabata ne wata kotun Kenya ta dakatar da shirin Amurka na buɗe cibiyar killace masu Ebola ta Amurkawa a ƙasar. Lamarin dai ya janyo cece-kuce da kuma damuwa a tsakanin jama'a.
Zuwa yanzu ba a samu ɓullar Ebola a Kenya ba sai dai ma'aikatar lafiya ta kafa cibiyar kula da kuma killace masu cutar a sassan ƙasar.

















