An yi musayar wuta kan rikicin zaɓe a Somaliya
Dakarun gwamnati da mayaƙa sun yi musayar wuta a Mogadishu, babban birnin Somaliya sakamakon rikici game da jan ƙafa wajen gudanar da zaɓe.
Wa'adin Shugaba Hassan Sheikh Mohamud kan karagar mulki ya zo ƙarshe ranar 15 ga watan Mayu amma an tsawaita shi da shekara ɗaya.
Ɓangaren hamayya ya ce hakan ya saɓa da kundin tsarin mulki inda kuma suka kira a gudanar da zanga-zanga a yau Alhamis.
Rahotanni sun ce an ji ƙarar harbe-harbe a wasu yankuna na babban birnin har zuwa cikin dare, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
Ƴansanda sun ce suna aiwatar da gagarumin samame ne kan mayaƙa masu riƙe da makamai da suka kai hare-hare a yankunan.
Bayan cikar wa'adin shugaban ƙasar ne gwamnatin tarayya da ɓangaren hamayya suka shiga tattaunawa sai dai sun gaza cimma matsaya.