Ministan harkokin cikin gidan Pakistan ya gana da Araghchi a Tehran
Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsen Naqvi, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, a birnin Tehran.
Kafin hakan, a daren Asabar, Naqvi ya kuma gana da takwaransa na Iran, Eskandar Momeni.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce bayan ganawar, Naqvi ya bayyana cewa ya kai ziyara Tehran ne domin isar da wata “wasika ta musamman” da kuma wani “muhimmin sako” daga babban kwamandan rundunar sojin Pakistan da kuma firaministan ƙasar zuwa ga Mojtaba Khamenei.
Sai dai rahotannin ba su bayyana cikakken abin da sakon ko wasikar suka ƙunsa ba.
Likitoci na fuskantar hare-hare a Najeriya - NARD
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar likitocin Najeriya masu neman ƙwarewa (NARD) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 da ta fara aiwatar da tsarin kasa na kare ma’aikatan lafiya daga hare-hare sakamakon ƙaruwar cin zarafi da farmaki da ake kai wa likitoci a faɗin ƙasar.
Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai bayan kammala babban taronta na yau da kullum da aka gudanar a Kano.
Haka kuma ta ayyana rikicin kwadago da gwamnati kan wasu bukatu 14 da har yanzu ba a warware ba a bangaren lafiya.
Shugaban NARD, Mohammad Suleiman, ya ce yawaitar hare-hare da tsoratarwa da cin zarafi da kuma amfani da karfi kan likitoci na barazana ga tsarin kiwon lafiyar Najeriya wanda tuni yake fuskantar ƙalubale.
Ya bayyana wannan yanayi a matsayin abin takaici kuma mai haɗarin gaske ga ɗorewar tsarin kiwon lafiya a kasar.
Daga cikin bukatun da ƙungiyar ta gabatar akwai gaggauta bincike, kama da hukunta waɗanda ke kai hare-hare kan ma’aikatan lafiya, tare da kara tsaurara matakan tsaro a asibitoci da wuraren kiwon lafiya.
NARD ta kuma buƙaci gwamnati ta fara aiwatar da tsarin kariya da martani ga hare-haren da ake kai wa ma’aikatan lafiya tare da fara aiwatar da dokokin da za su magance matsalar cikin kwanaki 21.
NARD ta yi gargadin cewa idan ba a biya wadannan buƙatu cikin kwanaki 21 ba, ba za ta iya tabbatar da zaman lafiya a harkokin aiki ba, kuma hakan na iya haifar da ƙarin matakan yajin aiki a fadin kasar.
Ba mu ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ba - Iran
Asalin hoton, Getty images/Tasnim
Wani mamba a kwamitin tsaron kasa na majalisar dokokin Iran, Vahid Ahmadi, ya ce babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka, yana mai gargadin cewa akwai yiwuwar ɓarkewar wani sabon yaƙi.
A wata hira da ya yi da shafin labarai na Fararoo, Ahmadi ya ce abin da ke akwai a yanzu shi ne dakatar da faɗa na wani lokaci, ba cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita wuta ba.
Ya ce Amurka ba ta cimma manufofin da ta sanya a gaba a lokacin yaƙin ba, kuma a yanzu tana ƙoƙarin matsa wa Iran lamba ta fuskar tattalin arziki ta hanyar toshe hanyoyin ruwa.
Sai dai ya ce wannan mataki ma bai kai ga nasarar da Amurka ke nema ba.
Ahmadi ya ƙara da cewa akwai yiwuwar sabon rikici ya sake barkewa, yana mai cewa Iran na da wasu sabbin damar da za ta iya amfani da su idan hakan ta faru.
Har ila yau, ya soki wasu ƙasashen yankin Gulf, yana mai cewa tsawon shekaru sun dogara da Amurka wajen neman kariya.
A cewarsa, yakin baya-bayan nan ya nuna cewa ba za a iya samun cikakken tsaro ta wannan hanya ba.
Hezbollah ta ce ta kai hare-hare kan wuraren sojojin Isra’ila a Kudancin Lebanon
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon ta sanar da cewa ta kai hari kan wani hedkwatar rundunar sojin Isra’ila da ke birnin Naqoura a kudancin Lebanon da jirage marasa matuƙa nau’in “Ababil”.
Hezbollah ta kuma yi iƙirarin cewa mayaƙanta sun kai hari kan sojojin Isra’ila a yankin Hadada da ke kudancin kasar da jirage marasa matuka guda biyu.
Haka kuma ta ce ta harba rokoki da harsasai na manyan bindigogi kan wuraren da ke kusa da sansanin Beaufort Castle.
A daren jiya, rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa cikin sa’o’i 48 da suka gabata ta kai hare-hare 150 a kudancin Lebanon, inda ta ce ta nufi wuraren da ke da alaka da kungiyar Hezbollah.
A gefe guda kuma, dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kudancin Lebanon sun yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan wata motar sojojin Lebanon a yankin Nabatieh, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji uku.
Assalamu alaikum
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.