Iran ta yi iƙirarin nasara yayin da tace saura ƙiris a cimma matsaya da Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa ta samu muhimman nasarori waɗanda suka kawo su kusa da cimma yarjejeniya da Amurka domin kawo ƙarshen rikicin da ake fama da shi.
Ya ce batutuwan da ake tattaunawa sun haɗa har da batun buɗe mashigar ruwan Hormuz, wanda ya ce yana da matuƙar muhimmanci a yarjejeniyar.
A wata hira da ya yi a gidan talabijin na cikin gida a Iran, Araqchi ya ce bangarorin biyu sun kai mataki mafi kusa da cimma matsaya fiye da kowane lokaci a baya.
Ya bayyana cewa yanzu haka ana dab da fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, yana mai cewa “an kusa cimma matsaya, saura kaɗan ne.”
Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai na Iran da su guji yin hasashen da zai iya jefa shakku ko ya dagula tattaunawar, yana mai cewa irin waɗannan rahotanni na iya lalata damar da ake da ita na cimma yarjejeniya.
A cewarsa, takardar fahimtar juna da ake aiki a kanta ba ta wuce shafi ɗaya da rabi zuwa biyu ba, amma duk da haka an shafe watanni biyu ana nazari da tattauna kowace kalma da ke cikinta sosai.
Araqchi ya ƙara da cewa an kasance ana sanar da hukumomin tsaro, ciki har da Majalisar Koli ta Tsaron Ƙasa, game da duk wani ci gaba a kai a kai.
A ƙarshe ya jaddada cewa sakamakon wannan aiki zai ƙara ƙarfafa matsayi da ƙarfin Iran a cikin gida da kuma a idon ƙasashen duniya, yana mai cewa mashigar Hormuz na ƙarƙashin ikon Iran da Oman.













