Mene ne tasirin soke haye-hayen al'ada a Kano

..
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Matakin da gwamnatin jihar Kano ta ɗauka na hana gudanar da hawan doki ya haifar da muhawara tsakanin al'umma, inda wasu ke ganin matakin ya zama dole saboda dalilan tsaro, yayin da wasu kuma ke kallon sa a matsayin barazana ga ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan al'adun jihar.

Hawa ba kawai wani biki ba ne na nishaɗi ko nuna ado da kwalliya; al'ada ce da ta kasance wani ɓangare na tarihin masarautun Hausawa, musamman Kano, inda sarakuna da fadawansu ke amfani da taron wajen nuna dangantaka da al'umma da kuma tabbatar da al'adun gargajiya.

A tsawon lokaci, hawan ya zama wani abin jan hankalin baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje, lamarin da ya sanya ake kallon sa a matsayin wata muhimmiyar hanya ta bunƙasa yawon buɗe ido da kuma adana tarihin al'umma ga masu tasowa.

Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan hana hawan, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: Ta yaya dakatar da wannan al'ada za ta shafi al'adun Kano, martabar masarautarta da kuma ƙoƙarin da ake yi na kare tarihi da aka gada tun ƙarni-ƙarni?

Ta yaya matakin zai shafi al'ada da tarihin Kano?

,..

Farfesa Aliyu Muhammad Bunza fitaccen masanin al'adu kuma malami a jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya ce matakin barazana ce ga wanzuwar tsohuwar al'adar.

Ya ce hawan doki da ake yi a ƙasashen Hausawa alami ne na yadda aka rinƙa fita yaƙi a wancan lokaci wanda haramta yin hawan ka iya sanya masu tasowa su zama ba su san al'adar ba.

"Tsarin masarautu an samar da shi ne ta yadda ake sigar yaƙi a lokacin sarakunan baya, akwai bayi da ke gaban sarki sannan sarki da kuma hakimansa waɗanda yawancinsu 'ya'yansa ne da za su iya sarauta a gaba.

Cikinsu waziri ne kawai bai iya sarauta da yake cikin tawagar," in ji Farfesa Bunza.

Farfesa Bunza ya kuma ƙara da cewa a baya sarakuna ne kan gaba a kuma sama da kowa, amma a tsarin shugabancin yanzu yawancin shugabannin siyasa babu ruwansu da al'adu, wani dalilin da ya sa ba su damu da kawar da al'adar ba.

"Ko da ɗan sarki za a iya haɗa kai da shi wajen ruguza al'adun sarauta, musamman idan ya tabbatar da cewa ba zai yi sarauta ba. Wannan ya taimaka wajen dakushe hasken sarautar da kuma kwarjininta a tsakanakin mutane musammam a irin jihohi irin su Kano da aka yi Sarki Ado Bayero a tarihi. In ji Bunza.

To sai dai gwamnatin jihar Kano ta sha musanta irin wannan tunani na masana inda take cewa dalilan tsaro ne da ka iya janyo wa jihar lalacewa ke tilasta mata saka irin waɗannan dokoki.

Manyan haye-hayen al'ada biyu a Kano

..

Hawan Sallah:

A duk lokacin bukukuwan sallah babba ko ƙarama,a Kano ana haye-hayen dawaki guda biyar domin nuna murnar bikin. Haye-hayen su ne

  • Hawan Idi
  • Hawan Daushe
  • Hawan Nassarawa
  • hawan Fanisau
  • Hawan Dorayi

Wakilin BBC Khalifa Shehu Dokaji wanda masani ne kan harkoki Masarautu ya ce " a yanzu mahayan Kano sun fi tafiya Zaria ko Katsina ko wasu jihohin domin su yi hawan".

.
Bayanan hoto, Ziyarar Sarauniyar Ingila a Najeriya a 1956

Hawan Daba:

Akwai hawan Daba da ake yi domin girmama baƙi daga wani sashen ƙasa ko kuma daga wasu ƙasashen waje.

Irin wannan Daba aka yi wa Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth da ta zo ko wanne mai riƙe da sarauta a lokacin zai zo ya wuce ta gabanta ana gabatar da shi a gare ta.

A lokacin baya an yi wa manyan mutane da kudancin Najeriya irin wannan hawa domin nuna musu al'adun yankin wadanda suka sha ban-ban da nasu.

Abubuwa biyar da suka sa Kano ta shahara

Jihar Kano na arewa maso yammacin Najeriya ne, kuma ta zama jiha ne a ranar 27 ga watan Mayun 1967.

Ta yi iyaka da Katsina daga arewa maso yamma, ta yi iyaka da Jigawa daga arewa maso gabas, ta yi iyaka da Bauchi daga kudu maso gabas.

Tana da fadin kasa kilomita 23,131, kuma ita ce jihar da tafi kowacce yawan kananan hukumomi inda take da 44.

Mafi yawan al'ummar jihar Hausawa ne, sai kuma Fulani da sauransu. Jihar na da manyan cibiyoyin ilimi na gwamnatin jiha da na tarayya.

Baya ga wadannan abubuwa kuma, akwai wasu kebabbun abubuwa biyar da jihar ta shahara da su kamar haka:

  • Yawan al'umma: Kano ce jihar da tafi duk jihohin Najeriya yawan al'umma. Kidayar da aka yi a shekarar 2006 ta nuna cewa akwai mutum miliyan tara da dubu dari hudu da dari biyu da tamanin da takwas, 9,401,288. Sannan kiyasin da aka yi a shekarar 2011 ya nuna cewa kasar na da yawan al'umma miliyan goma sha daya da dubu hamsin da takwas da dari uku, 11,058,300. Sabon ƙiyasa na 2026 ya nuna cewa jihar Kano na da yawan mutane fiye da miliyan 18.
  • Kasuwanci: Jihar Kano ce cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya. Ta shahara a fannin kasuwanci tun karni na 16. A 2019, Gwamnatin jihar ta ce ana mu'amala ta naira biliyan 20 a kowacce rana a jihar a harkokin kasuwanci. Jihar ce ta biyu wajen manyan masana'antu a Najeriya bayan Lagos, sai dai a baya-bayan nan rashin wutar lantarki ya jawo durkushewar bangaren masana'antu a jihar.
  • Tarihi: Kano gari ne mai dimbin tarihi saboda dadewarsa da kuma irin rawar da ya taka a kasuwanci da addini da ma wasu fannonin ci gaban arewacin Najeriya. Fitattun abubuwan tarihi da jihar ke tunƙaho da su sun haɗa da haye-hayen dawaki.