NYSC: Sauye-sauye bakwai da za a yi wa shirin hidimar ƙasa a Najeriya

NYSC

Asalin hoton, NYSC

    • Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Gwamnatin Najeriya ta amince da yin cikakken garambawul ga shirin yi wa ƙasar hidima (NYSC), wanda ya kasance tilas a kan duk wani matashin da ya kammala karatun digirin farko.

Sauyin na zuwa ne shekara 53 bayan ƙirƙiro shirin.

Ministan ci gaban matasa na ƙasar, Ayodele Olawande wanda ya sanar da sauye-sauyen, ya ce an yi gyaran ne don sauya akalar tsarin na NYSC zuwa wanda zai mayar da hankali kan bunƙasa ƙwarewa a fannin sana'o'i, da manufar samar wa matasan ƙasar ayyukan yi.

An kafa Hukumar kula da yi wa ƙasa hidima ta NYSC ne a shekarar 1973 bayan yaƙin basasa na Najeriya, don haɓaka haɗin kan ƙasa ta hanyar tura waɗanda suka kammala karatunsu zuwa jihohin da ke wajen yankunansu na tsawon shekara ɗaya domin gudanar da ayyuka da za su taimaka wurin inganta ci gaban ƙasa.

Shin mene ne zai sauya game da shirin?

Tsarin shugabanci

Daya daga cikin sauye-sauye mafi muhimmanci shi ne wanda za a yi wa tsarin shugabancin shirin. Asali dai sojoji ne ke jagoranatar shirin, amma daga yanzu za a mayar da alhakin gudanar da al'amuran shirin ga farar hula.

An sanar da cewa sojoji za su ci gaba da tabbatar da tsaro ga masu yi wa ƙasa hidima a duk faɗin ƙasar.

Da take ƙarin haske kan waɗannan sauye-sauyen, mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan tsare-tsare Hadiza Bala Usman, ta ce sauya shugabancin shirin daga sojoji zuwa farar hula ba zai rage rawar da sojoji ke takawa wajen tabbatar da tsaro ga shirin ba.

"Tsaron jami'an hukumar da na masu hidimar ƙasa zai ci gaba da zama alhakin sojojin Najeriya, abin da zai sauya shi ne shugabancin hukumar ta NYSC, wanda a yanzu zai kasance ƙarƙashin farar hula, yayin da sojoji ke ci gaba da samar da kayan tsaro da suka dace don nasarar shirin," inji ta.

Wannan dai babban sauyi ne daga yadda abubuwa su ke a baya inda shirin ke ƙarƙashin jagorancin sojoji, tun daga lokacin da aka kafa shi a shekarar 1973.

Sai dai, wannan sauyi zai bukaci a yi wa dokar NYSC gyaran fuska kafin ya fara aiki.

Tsawaita wa'adin horaswa

NYSC

Asalin hoton, NYSC/X

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Za a tsawaita wa'din zaman da masu yi wa ƙasa hidima ke yi a sansanonin horaswa daga mako uku zuwa shida.

Gwamnati na shirin bullo da shirin horaswa na mako shida wanda zai mayar da hankali kan bunƙasa ilimin shugabanci da na kasuwanci da kuma fasahar zamani ta dijital.

Yayin da ake sa ran za a ci gaba da gudanar da atisayen soja da ayyukan motsa jiki, za a faɗaɗa tsarin karatun don tabbatar da cewa waɗanda suka kammala karatun digiri sun shirya tunkarar ƙalubalen samun aikin yi.

Hadiza Bala Usman, ta ce za a sake fasalin zaman da ake yi a sansanonin horaswar masu yi wa ƙasa hidima zuwa matakai uku.

- Makonni biyu na farko za su mayar da hankali ne kan inganta halaye nagari da kishin ƙasa, da kuma bunƙasa ilimin shugabanci tsakanin matasan.

- Makonni biyu masu zuwa za su karkata ne wurin bunƙasa ilimin sana'a da hadahadar kuɗi da kuma yadda za iya samu da kuma sarrafa hannayen jari.

- Makonni biyu na ƙarshe za su zamo na bayar da horo na musamman ne kan samar da ilimin da ya shafi fannin kasuwanci ko sana'ar da matashi ya zaɓa.

A ƙarƙashin sabon tsarin, a lokacin da suke rajista a sansanonin horo, masu yi wa ƙasa hidima za su zaɓi ɗaya daga cikin fannoni sana'o'i da kasuwanci guda 11 da aka ɓullo da su.

Fannonin sun haɗa da: aikin gona, kiwon lafiya, samar da ilimi, kimiyya da fasahar dijital, fannin ilimin shari'a, fannin hidimar al'umma, fannin ababen more rayuwa, harkar inganta muhalli, ilimin kasuwanci, tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma fannin tsaro.

Daidaita wuraren aiki da karatun masu hidimar ƙasa

NYSC

Asalin hoton, Getty Images

Wani zargi da aka daɗe ana yi wa NYSC shi ne rashin daidaito tsakanin abubuwan da masu yi wa ƙasa hidima suka karanta a matakin digiri da kuma wuraren da ake tura su aiki a ƙarƙashin shirin.

A cewar gwamnati, a yanzu za a riƙa tura masu yi wa ƙasa hidima ne zuwa wuraren da za su samu ƙwarewa kan fannonin da suka dace da iliminsu.

Ana tunanin cewa idan an aiwatar da wannan yadda ya kamata, zai iya inganta jin daɗi da samun ƙwarewa a wurin aiki, zai kuma bunƙasa damarmakin samun aiki bayan kammala shirin.

La'akari da tsaro wurin tura masu hidimar ƙasa

Cikin ƴan shekarun nan matsalar rashin tsaro ta kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke ci ma shirn NYSC tuwo a ƙwarya. A ƙarƙashin sabon tsarin za a riƙa la'akari da batutuwan da suka shafi tsaro a lokacin da ake tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa jihohi da yankuna.

Duk da dai gwamnati ba ta sanar da sabon tsarin yadda za a riƙa rarraba matasan ba, wannan na nufin cewa yanayin tsaro zai riƙa taka muhimmiyar rawa kan inda za a iya kai waɗanda ke ƙarƙashin shirin.

Wannan sauyin dai na da niyyar taƙaita haɗarin da masu yi wa ƙasa hidima ke fuskanta a wasu yankuna sakamakon matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan ƙasar.

Zamanantar da hanyar tura masu hidimar ƙasa

Gwamnati na da shirin zamanantar da hanyoyin da ake amfani da su wurin tura masu hidimar ƙasa zuwa jihohi da yankuna domin gudanar da ayyukansu.

Wannan zai ƙunshi amfani da fasahar zamani domin rage matsalolin da ake fuskanta wurin tura masu hidimar ƙasa wuraren da suka dace.

Hakan zai rage lokacin da ake ɓatawa da inganta yin adalci wurin gudanar da al'amuran shirin da kuma tabbatar da daidaito a yadda ake rarraba masu hidimar ƙasa zuwa yankuna da jihohi daban-daban.

Sauya fasalin kayan hidimar ƙasa da soke faretin kammalawa

NYSC

Asalin hoton, NYSC/X

A cewar Ministan ma'aikatar kula da ci gaban matasa na Najeriya, za a sauya kayan da masu hidimar ƙasa ke sanyawa, "matakin da ke da niyyar farfaɗo da martabar tsarin da kuma yadda ake ɗaukar masu hidimar ƙasa a cikin al'umma, zai kuma bunƙasa kishin ƙasa a tsakaninsu".

Sai dai bai yi ƙarin haske kan yadda sabon kayan zai kasance ba.

Bugu da ƙari gwamnatin za ta sauya yadda ake gudanar da bikin kamala shirin, inda a baya ake gudanar da fareti irin na soja yanzu za a fara wani biki ne na musamman da ke da yanayi da bikin kamala makaranta.

Inganta sansanonin horaswa

NYSC

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnati za ta ɓullo da shirin inganta sansanonin horas da masu hidimar ƙasa da ke fadin ƙasar ta hanyar bijiro da wani tsari na musamman na bai wa kowane sansani maki, a kuma sanya su kan wani jadawalin da zai nuna matsayin da kowane sansani ya ke kai, inda ba za a amince da duk wani sansanin da bai kai matakin ingancin da ake buƙata ba.

Wannan mataki dai na da niyyar inganta yanayin sansanonin, da ababen more rayuwa da ke cikinsu tare kuma da tabbatar da samun daidaito a abubuwan da ke akwai a duka sansanonin horaswan da ke faɗin ƙasar.

Ko yaushe waɗannan sauye-sauye za su fara aiki?

Waɗansu daga cikin sauye-sauyen nan, musamman waɗanda suka shafi tsarin shugabanci za su buƙaci a yi wa dokar NYSC da ke kundin tsarin mulki gyaran fuska

Don sawwake aiwatar da sauyin, majalisar ministocin ƙasa ta umurci babban lauyan tarayya da Ma'aikatar kula da ci gaban matasa ta ƙasa da su yi wa dokar NYSC da sauran ka'idojin da suka dace kwaskwarima don samar da tsarin doka da tabbatar da waɗannan sauye-sauyen a hukumance.

Sauye-sauyen dai na nuni ne da cikakken garambawul na farko ga shirin tun lokacin da aka ƙirƙiro shi, inda gwamnatin Najeriya ta ce an tsara sauye-sauyen ne domin ganin shirin na NYSC ya fi dacewa da buƙatun ci gaban tattalin arziki da matasa na Najeriya a wannan zamani.