Munanan haɗurran jiragen sama 14 da suka girgiza Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Usman MINJIBIR
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A tarihin sufurin jiragen sama a Najeriya, an samu hatsurruka masu yawa da suka shafi jiragen fasinja, jiragen soja da kuma jiragen haya.
Najeriya ta fuskanci fiye da hatsurran jiragen sama da helikwafta 50 tsakanin shekarar 1956 da 2026.
Kusan duk wani babban hatsari ya kan jawo bincike da sake duba ka'idojin tsaron sufurin jiragen sama a Najeriya amma kuma masana na cewa hakan bai taɓa zama darasi ga afkuwar na gaba ba.
Ga wasu daga cikin manyan hatsurran da suka fi fice a tsawon shekaru 50 a Najeriya.
Oktoba 2026 - Ondo
Sojoji 25 ne suka rasu sakamakon haɗarin jirgin soji mai saukar ungulu da ya faru ranar Litinin 5 ga watan Okotoban a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Hukumomi sun ce jirgin yana kan wani aiki ne na yau da kullun daga Benin zuwa Legas lokacin da ya faɗi kusa da sansanin sojojin ruwa a safiyar Litinin.
Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa jirgin ya faɗi kusa da wani kurmi kuma an gano tufafi da takalma a wurin. Ana iya ganin hayaki yana tashi daga yankin.
Mayu, 2021 - Kaduna
A watan Mayun 2021 manyan sojoji 11 suka rasu sakamakon wani hatsarin jirgin sojin sama mai saukar ungulu a jihar Kaduna ciki har da babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru
Duk da cewa hukumomi ba su tabbatar da musabbabin hatsarin ba, wasu rahotanni na cewa akwai yanayi maras a jihar lokacin da jirgin ya faɗo ƙasa.
Yuni, 2012 - Legas

Asalin hoton, Getty Images
Jirgin Dana Air Flight 992 ya fadi a yankin Iju-Ishaga da ke Legas, inda dukkan fasinjojin 153 suka mutu tare da wasu mutanen da ke kasa. Wannan na daga cikin hatsurran jiragen sama mafi muni a tarihin kasar.
Disamba 2012 - Bayelsa
Gwamnan jihar Kaduna na lokacin, Patrick Yakowa, da tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Owoeye Azazi, sun mutu a hatsarin helikwafta a Bayelsa.
Oktoba, 2006 - Abuja
Jirgin ADC Airlines Boeing 737 ya fadi jim kadan bayan tashinsa daga Abuja, inda sama da mutane 90 suka mutu.
Oktoba 2005 - Ogun
Jirgin Bellview Airlines ya fadi a Ogun, inda mutane 117 suka mutu.
A ranar 22 ga Oktoban 2005, mintuna kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama, jirgin ya kifa zuwa ƙasa.
Dukkan mutane 117 da ke cikin jirgin, wato fasinjoji da ma'aikatan jirgin, sun mutu a hatsarin.
Wannan hatsari na Bellview na daga cikin manyan hatsurran jiragen sama da suka fi tayar da hankali a tarihin Najeriya.
Jirgin Bellview Airlines Flight 210 wani jirgin fasinja ne na cikin gida a Najeriya da kamfanin Bellview Airlines mai hedikwata a Legas ke sarrafawa.
Jirgin samfurin Boeing 737-200 ne wanda ke yin zirga-zirga daga Legas zuwa Abuja.
Disamba, 2005 - Rivers

Asalin hoton, Getty Images
Jirgin Sosoliso Airlines Flight 1145 ya yi hatsari a Fatakwal, inda mutane 109 suka mutu, ciki har da dalibai da dama na makarantar Loyola Jesuit.
Mayu, 2002 - Kano
Jirgin EAS Airlines ya fadi a Kano, inda mutane 148 suka mutu ciki har da wadanda hatsarin ya rutsa da su a kasa.
Fabrairu, 1990 - Akwa Ibom
Wani helikwafta na Birtaniya ya yi hatsari a Eket, jihar Akwa Ibom, inda dukkan mutane 9 da ke cikinsa suka mutu.
Nuwamba, 1983 - Enugu
Wani jirgin Nigeria Airways F28-1000 ya fado a kusa da Enugu, inda mutane 53 suka rasa rayukansu.
Maris, 1978 - Kano
Jirgin Nigeria Airways F28-1000 ya yi hatsari a Kano, inda mutane 16 suka mutu.
Janairu, 1973 - Kano
Jirgin Royal Jordanian Airlines Flight 707 ɗauke da mahajjatan Najeriya 171 ya fado a Kano, kuma dukkan wadanda ke cikinsa suka mutu.
A ranar 22 ga Janairun 1973, wani jirgin Boeing 707 na kamfanin Nigeria Airways ya yi hatsari a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano International Airport yayin da yake ƙoƙarin sauka a cikin iska mai ƙarfi.
Hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 171, ciki har da fasinjoji da ma'aikatan jirgin. Sai dai mutane 26 sun tsira da rayukansu.
Nuwamba, 1969 - Legas
Jirgin Nigeria Airways BAC VC10 ya yi hatsari, inda mutane 87 suka mutu, a birnin Legas.
Jirgin Nigeria Airways Flight 925 na kan hanyarsa ne daga Landan zuwa Legas, tare da tsayawa a Roma da Kano kafin ya isa Legas.
Yayin da jirgin ke shirin sauka a Legas, tare da tayoyinsa a buɗe da kuma fikafikansa na sauka a ɗan buɗe, jirgin samfurin VC10 ya bugi wasu itatuwa.
Daga nan jirgin ya faɗi cikin wani daji mai sarƙaƙiya, inda ya yi bindiga ya kuma kama da wuta. Dukkan fasinjoji 76 da ma'aikata 11 da ke cikin jirgin sun mutu
Yuni, 1956 - Kano
Wani jirgin BOAC Argonaut ya yi hatsari bayan tashinsa daga filin jirgin Kano, inda mutane 32 suka mutu.
Jirgin na Argonaut ya tashi daga filin jirgin sama na Kano zuwa Tripoli a ƙasar Libya.
Jirgin na kan hanyarsa ne daga Legas zuwa Landan, inda ya tsaya a Kano kamar yadda aka tsara. A lokacin ana ruwan sama. Bayan jirgin ya kai tsayin ƙafa 250 (kimanin mita 76) a sama, sai ya fara komowa ƙasa.
Matukin jirgin ya ƙara ƙarfin injin zuwa matsakaicin ƙarfi, amma duk da haka jirgin ya ci gaba da silmiyowa har sai da ya bugi wata bishiya mai nisan kilomita 2.4 daga ƙarshen titin jirgin.
A hatsarin, ma'aikatan jirgin uku daga cikin bakwai da kuma fasinjoji 29 daga cikin 38 suka mutu. Sannan ma'aikata biyu da fasinjoji biyu sun samu munanan raunuka.




























