Alhassan Ɗantata: Ɗan Najeriya da ya je aikin Hajji a jirgin ruwa

Alhassan Ɗantata

Asalin hoton, Hassan Sanusi Dantata

Bayanan hoto, Alhassan Ɗantata yana da ƴaƴa 65 ciki har da Alhaji Aminu Dantata da Alhaji Sanusi Dantata wanda kaka ne ga Aliko Dangote.
    • Marubuci, Usman MINJIBIR
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shekaru kimanin 99 kenan da attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka ta yamma a wancan zamanin, Alhaji Alhassan Ɗantata ya gudanar da aikin Haji tare da tawagar mutanen da ya ɗauki nauyi su 15.

Masana tarihi sun ce Alhaji Alhassan Ɗantata shi ne fitaccen ɗan Najeriya na biyu da ya je aikin Hajji a jirgin ruwa, bayan Sarkin Katsina, Muhammadu Dikko a 1921, abin da ya ɗauki hankalin duniya a zamanin.

Mafi yawancin maniyyata a wancan lokacin na zuwa aikin Hajji ne ta amfani da jakuna da dawaki da raƙuma sannan kuma suna yada zango a ƙasashe da garuruwa kafin su isa Makka.

Domin kawo muku tarihin aikin Hajjin na marigayi Alhaji Alhassan Ɗantata, BBC ta yi amfani da littafin rayuwar Alhaji Alhassan Ɗantata mai suna "The Life and Times of Alhaji Alhassan Ɗantata, A merchant par exellence", wanda Hassan Sanusi Dantata ya rubuta.

Tafiya daga Kano zuwa Makka

Alhassan Dantata da tawagarsa

Asalin hoton, Hassan SanusiƊantata

Bayanan hoto, Alhaji Alhassan Dantata tare da tawagarsa a jirgin ruwa a yayin tafiyarsu zuwa aikin Hajji.

Alhaji Alhassan Ɗantata da tawagarsa ta mutum 15 da ya biya wa sun bar Kano zuwa Legas a ranar 1 ga watan Afrilu na 1927.

Tawagar ta mutum 16 ta kuma isa gaɓar tekun Tema da ke ƙasar Ghana kafin daga bisani su isa tashar ruwa ta Liverpool da ke Burtaniya a ranar 21 ga watan Afrilu na shekarar.

Ɗantata ya samu tarba ta musamman daga Sarkin Ingila na lokacin King George V, mahaifin sarauniyar Ingila, inda ya tarbe su a fadar Buckingham, a matsayinsa na fitaccen ɗan Najeriya na farko da ya ratsa ta Ingila domin tafiya aikin Hajji.

Tawagar maniyyatan ta yi kwana biyu a Ingila kafin ci gaba da tafiya a ranar 24 ga watan na Afrilu inda ta isa zuwa ƙasar Faransa a ranar 26 ga watan sannan daga bisani suka tankarar da tashar ruwa ta Port Sa'id kafin shiga birnin Alƙahira (Cairo) a ranar 7 ga watan Mayun 1927.

Daga tashar ruwan birnin na Alƙahira na ƙasar Masar ne kuma tawagar da mutumin mafi kuɗi a Afirka ke jagoranta ta nufi birnin Jedda inda kuma ta sauka a birnin a ranar 16 ga watan Mayun shekarar wanda ya yi dadai da 14 ga watan Dhulƙada 1345.

Yadda Ɗantata ya gudanar da aikin Hajji

Ka'aba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton Ka'aba a shekarun 1930s

Bayan barin Jedda, Ɗantata ya shiga birnin Makkah inda bayanai suka nuna cewa ya fashe da kuka a lokacin da ya yi ido biyu da ɗakin Allah.

A cikin littafin da Sanusi Ɗantata ya rubuta, an rawaito cewa Ɗantata ya kasance mutum mai tawali'u inda ya ƙi amincewa ya zauna a ɗakin sama da aka ba shi.

Bayanai sun nuna cewa Alhassan Dantata ya kasance a koda yaushe yana Ka'aba domin yin ɗawafi da sallaoli da karatun Alƙur'ani tare da kasancewa da makarantar Alƙur'ani.

Hakan ya kasance abin da yake yi a kullum har zuwa lokacin da aka fara aikin Hajji, kuma bayan nan ne ya ɗauki hanya zuwa Madina bayan kwashe kwanaki 15.

Attajirin da ɗaya daga cikin mahajjatan da suka hau dutse Arafa ba tare da takalmi ba saboda girmamawa.

Takardar yabo ga Ɗantata daga Saudiyya

Ɗantata

Asalin hoton, Hassan Sanusi Dantata

Bayanan hoto, Takardar yabo da hukumomin Saudiyya suka aika wa Alhaji Alhassan Ɗantata.

Kamar yadda yake a littafin da Hassan Sanusi ya rubuta, Alhaji Alhassan Ɗantata ya bayar da tallafi domin kula da Ka'aba.

Ya kuma bayar da tallafin samar da ruwan sha ga mahajjata da ake kira da "Aynu Zubayda."

Baya ga wannan tallafin, Dantata ya ƙara da alƙawarin bayar ci gaba da bayar da tallafin a duk shekara domin kula da mazauna birnin Makka da ba su da ƙarfi.

Sakamakon irin tallafin da Alhaji Alhassan Ɗantata ya bai wa hukumomin Saudiyya, ya sa suka rubuto masa takardar godiya da yabo.

"Mun karɓi famafamai (pound sterling) daga Alhaji Muhammadu Sani Sharu kamar yadda aka saba (duk wata). An sanya kuɗin a asusun shirin samar da ruwan sha na "Aynu Zubayda"

Ɗantata ya biya wa mutum 430 su koma gida

..

Asalin hoton, Hassan SanusiƊantata

Bayanan hoto, Alhaji Alhassan
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan isar Ɗantata Makka halayyarsa ta taimakon al'umma ta ƙara fitowa fili, inda ya rinƙa ɗaukar ɗawainiyyar mahajjatan da ba su da ƙarfi domin gudanar da ayyukan hajjinsu ba tare da samun damuwa ba.

Attajirin ya sayi raguna ga maniyyatan da ba su da ƙarfi sosai domin yin layya, inda bayanai suka nuna cewa sai da ya tabbatar duk wani ɗan Najeriya da ya haɗu da shi ya yi layya.

Bugu da ƙari, Alhassan Dantata ya nemi sanin mutanen da ba su da guziri na komawa gida musamman ƴan najeriya da suka fito daga garuruwan Kano da Katsina da Sokoto da Zaria.

An dai ce attajirin ya sa aka yi shelar neman duk wanda yake son komawa gida amma ba shi da hali, inda kuma aka samo mutum 430 da suka ce za su koma gida kuma haka ya biya musu kuɗin komawar, al'amarin da gwmnatin Saudiyya ta yi matuƙar yabawa da shi.

A ranar 25 ga watan Yuni ne Alhaji Alhassan Dantata tare da tawagarsa ya bar birnin Jeddah inda kuma ta sauka a birnin Kano a ranar 11 ga watan Agustan 1927.

Hakan na nufin tawagar da Alhaji Alhassan Dantata ya jagoranta ta yi kwana 140 wato wata huɗu da kwana 20.

Mutanen da ke tawagar Ɗantata

  • Abdullahi - Babban ɗan Ɗantata
  • Malam Abubakar - Malamin Ɗantata
  • Malam Muhammadu
  • Adamu Bangwaje - Surukin Ɗantata
  • Bashari - Surukin Dantata
  • Abubakar - Surukin Dantata
  • Barau -Surukin Dantata
  • Yusuf - Kanin Dantata
  • Malam Madu - Aminin Dantata
  • Abubakar - Ma'aikacin Dantata
  • Abdulmumin- Surukin Dantata
  • Malam Adhama- Malamin addini kuma aminin Dantata
  • Abdullahi, Wakilin Sarki
  • Malam Umaru - Babban Malami Madabo
  • Malam Balarabe - Ma'aikacin Dantata

Wane ne Alhassan Ɗantata?

Alhaji Alhassan Ɗantata a hoto.

Asalin hoton, Hassan Sanusi Dantata

Bayanan hoto, An haifi Alhaji Alhassan Dantata a shekarar 1877 ya kuma rasu a 1955.

An haifi Alhaji Alhassan Ɗantata a shekarar 1877 a garin Bebeji da ke jihar Kano kuma mahaifansa ƴan kasuwa da ke gudanar da kasuwanci tsakanin Najeriya zuwa Ghana, kamar yadda yake a littafin tarihin na Ɗantata "The Life and Times of Alhaji Alhassan Ɗantata, A merchant par exellence", wanda Hassan Sanusi Dantata ya rubuta.

Sunan mahaifinsa Malam Abdullahi da ake wa laƙabi da Baba Talatin wanda yake zaune a garin Madobi kafin ya koma Bebeji, garin da aka haifi Ɗantata.

Bayan rasuwar Malam Abdullahi sai mahaifiyar Alhassan ta koma ƙasar Ghana kusa da kawunta, inda ta bar Alhassan tare da ƴanuwansa ga wata baiwarta da ake kira Tata.

Kuma zama da shaƙuwar da Alhassan ya yi da Tata ne ya sa ya samo laƙabin 'Dantata' da har yau ɗin iyalansa ke amfani da shi.

Ɗantata shi ne mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka ta yamma a wancan lokaci, inda ya kafa kasuwanci iri-iri da suka haɗa da cinikin gyaɗa da shanu da goro sakamakon alaƙarsa da Turawa.

Alhaji Alhasan Ɗantata ya rasu a shekarar 1955, inda ya bar ƴaƴa 65, ciki har da Alhaji Aminu Ɗantata da Alhaji Sanusi Ɗantata wanda kaka ne a wurin mutumin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirka wato Alhaji Aliko Dangote.