Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilan da suka sa tattalin arzkin China ya fuskanci koma-baya a bana
Tattalin arzikin China ya fuskanci komabaya a tsakanin farkon watan Afrilu da ƙarshen watan Yuni, sakamakon raunin buƙata a cikin gida da kuma tasirin da yaƙin Iran ya yi kan farashin mai, duk da cewa fitar da kayayyakin ƙasar zuwa ƙasashen waje ya ci gaba da kasancewa mai ƙarfi."
Alƙaluman hukuma na yawan abin da ƙasa ke samarwa (GDP) sun nuna cewa tattalin arzikin ƙasa ta biyu mafi girma a duniya ya bunƙasa da kashi 4.3 cikin 100 a rubu'in shekara na biyu, adadin da ya gaza cimma burin da gwamnatin Beijing ta sa a shekarar.
Sanarwar na zuwa ne kwana guda bayan wasu bayanan gwamnati sun nuna cewa fitar da kayayyakin China zuwa ƙasashen waje ta karu da kashi 27 cikin 100 a watan Yuni idan aka kwatanta da na lokacin bara.
A watan Maris, China ta rage burinta na bunƙasar tattalin arziki zuwa tsakanin kashi 4.5 zuwa 5 cikin 100, wanda shi ne mafi ƙanƙantar burin ci gaban tattalin arzikin da ƙasar ta sa tun shekarar 1991.
Wadannan alkaluma su ne na farko da suka shafi cikakken rubu'in shekara na tattalin arziki tun bayan fara yaƙin Iran a ranar 28 ga Fabrairu, kuma sun zo ne bayan da tattalin arzikin China ya bunƙasa da kashi 5 cikin 100 a rubu'in shekara na farko.
Wasu bayanai da aka fitar ranar Laraba sun kara fito da ƙalubalen tattalin arzikin da gwamnatin Beijing ke fuskanta a cikin gida, ciki har da komabaya a fanin kasuwar gidaje da ya shafe lokaci yana ci gaba da tabarbarewa, da kuma raunin kashe kuɗin da masu amfani da kayayyaki ke yi.
Farashin sabbin gidaje ya sake faduwa, ko da yake raguwar da aka samu ta kashi 0.1 cikin 100 a watan Yuni ta kasance a hankali idan aka kwatanta da watan da ya gabace shi.
Sai dai tallace-tallacen kayayyaki ga masu amfani da su sun karu da kashi 1 cikin 100 a watan Yuni, lamarin da ya nuna ɗan farfaɗowa idan aka kwatanta da raguwar kashi 0.6 cikin 100 da aka samu a watan Mayu.
"Bayanan hukumar kwastam na watan Yuni, waɗanda aka fitar ranar Talata, sun nuna cewa fitar da kayayyakin fasaha na China zuwa ƙasashen waje ta ƙaru sakamakon ƙaruwar buƙatar na'urorin kwamfuta a duniya, waɗanda ake amfani da su wajen sarrafa cibiyoyin adana bayanai na fasahar basirar na'ura mai kwaikwayon tunanin ɗan Adam (AI).
Haka kuma, ƙaruwar buƙatar motocin lantarki na China a kasuwannin duniya ta ba da gagarumar gudunmawa ga fitar da kayayyakin ƙasar zuwa ƙasashen waje, inda yawan motocin da China ta fitar a cikin wata guda ya haura miliyan ɗaya a karon farko.