Biranen duniya 10 mafiya ƙayatarwa a 2026

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Lindsay Galloway
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Rahoton Oxford Economics World Cities Index na 2026 ya bayyana matsayin birane 1,000 a duniya, bisa la'akari da wasu muhimman fannoni guda biyar: shugabanci da tattalin arziki da albarkatun ɗan Adam da muhalli da kuma ingancin rayuwa.
A bana, birnin New York da London da Paris ne suka kasance a kan gaba, yayin da wasu birane kamar Seattle da Dublin su ma suka samu matsayi na gaba a jerin biranen da suka fi fice.
A cewar rahoton World Cities Index na shekarar 2026, amsar ba ta ta'allaƙa ne kawai kan ƙarfin tattalin arziki ko kyawawan gine-gine ba.
Abubuwa kamar al'adu da fasaha da muhalli da ilimi da kuma ingancin rayuwa su ma suna taka muhimmiyar rawa.
Rahoton ya ce akwai wasu abubuwa da ake la'akari da su wajen tantance ingancin birni da suka haɗa da:
1. Janyo hankalin mutanen duniya
Manyan birane a duniya galibi suna da abu guda da suka yi tarayya a kai: al'ummarsu ta kunshi mutane daga sassa daban-daban, masu fasahohi, ilimi da ra'ayoyi mabambanta.
Wannan shi ne abin da bangaren "jarin ɗan Adam" ke aunawa.
Lokacin da mutane daga wurare da al'adu daban-daban suka zauna a wani birni, sukan zo da sabbin dabaru, fasahohi da al'adu, waɗanda za su iya sauya fannoni da dama na rayuwa, tun daga kasuwanci zuwa abinci, fasaha da rayuwar yau da kullum.
Misali, birnin Boston, wanda yake matsayi na bakwai, na da shahararrun jami'o'i da cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare da dama, lamarin da ya sanya birnin ya zama cibiyar ilimi da ƙwararrun ma'aikata.
Tattalin arzikinsa da ya dogara da ilimi shi ma ya taimaka wajen samar da babban matakin samun kuɗin shiga.
An kuma zuba wani ɓangare na wannan arziki wajen inganta wuraren taruwar jama'a.
Rose Kennedy Greenway na ɗaya daga cikin misalan hakan. Wurin da a da babbar hanyar mota ce da aka ɗaga sama, yanzu an mayar da shi wurin shakatawa mai lambuna, maɓuɓɓugan ruwa da wuraren baje kolin fasahar zane.
Idan kuma kana son fasaha, cibiyoyi irin su gidajen tarihin fasaha na Harvard su ma suna buɗe wa jama'a.
Tattalin arzikin Boston da ya dogara da ilimi ya sanya birnin ya kasance cikin biranen duniya da ke da mafi yawan kuɗin shiga.

Asalin hoton, Getty Images
Dublin ma yana da irin wannan yanayi. Birnin na da ƙwararrun ma'aikata masu ilimi da gogewa, tare da tallafin cibiyoyin ilimi kamar Trinity College Dublin. Wannan ya jawo manyan kamfanonin ƙasa da ƙasa kamar Google, Meta, Microsoft da Accenture.
Kasancewar waɗannan kamfanoni a birnin ba kawai ya sauya tattalin arzikin Dublin ba, har ma ya taimaka wajen farfaɗo da tsohon yankin bakin ruwa da wuraren taruwar jama'a da ke gefen kogin Liffey.
Sai kuma birnin London.
London shi ne birni na farko a fannin jarin ɗan Adam, kuma yana janyo mutane daga kusan kowace ƙasa a duniya. Kusan kashi 40 cikin 100 na mutanen da ke zaune a birnin an haife su ne a wajen Birtaniya.
Wannan bambancin al'ummomi yana bayyana a rayuwar London, musamman a fannin abinci.
A London, abu ne mai sauƙi a samu abinci da ɗanɗanon da suka fito daga sassa daban-daban na duniya.
2.Kyawawan al'adu
Tattalin arziki mai ƙarfi yana da muhimmanci, amma shi kaɗai ba zai iya sa birni ya zama abin sha'awa ba.
Paris misali ne mai kyau. Birnin ya zo na uku a jerin gaba ɗaya, amma ya samu kyakkyawan matsayi a fannin "ingancin rayuwa".
Ɗaya daga cikin dalilan hakan shi ne sauƙin samun damar shiga harkokin al'adu. Paris na da kusan gidajen tarihi 130. Tun daga shekarar 2001, gidajen tarihi 11 na birnin ke ba da damar shiga baje kolin kayayyakin tarihinsu na dindindin kyauta, ba tare da la'akari da ƙasa ko asalin baƙo ba.
Kuma ba nan kawai abin ya tsaya ba. Wasu gidajen tarihi da dama ma suna ba da damar shiga kyauta aƙalla sau ɗaya a wata.

Asalin hoton, Getty Images
Seattle ma yana da fannin al'adu mai ƙarfi. Birnin ya shahara wajen fasaha da kiɗa. Gidan adana kayan tarihi na fasaha na Seattle yana daga cikin fitattun cibiyoyin al'adu na birnin, yayin da tarihin kiɗan grunge ya haifar da fitattun ƙungiyoyin kiɗa a duniya kamar Nirvana da Pearl Jam.
Kwanan nan birnin ya kammala aikin gina wani wurin shakatawa a bakin kogi. Aikin ya maye gurbin wata babbar hanya da ta lalace, inda aka mayar da wurin wata hanya ta musamman ga masu tafiya a ƙafa, tare da sabbin tashoshin jiragen ruwa na jama'a da hanyoyin kekuna.
3. Sauƙin rayuwa da tsafta

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Birni na iya kasancewa mai ban sha'awa kuma mai ɗimbin al'adu, amma gurɓacewar iska ko rashin ingantaccen tsarin sufuri na iya lalata kwarewar baƙo cikin sauri.
Duk da girmanta, London na da kyakkyawan sakamako a fannin muhalli idan aka yi la'akari da girman birnin. Oxford Economics ya ambaci matakai kamar cajin kuɗin cunkoson ababen hawa da kuma yankin da aka haramta motoci masu fitar da hayaki mai yawa, a matsayin wasu daga cikin matakan da suka taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa da gurɓacewar muhalli.
Ana iya ganin waɗannan sauye-sauye musamman a titunan tsakiyar birnin, inda motoci ba su mamaye wuraren kamar yadda suke a baya ba.
San Francisco ma ya samu kyakkyawan matsayi a fannin muhalli. Rahoton ya bayyana tsarin sufuri na birnin a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suka sa mazauna da baƙi ba sa dogaro sosai da motoci. Hakan na taimakawa wajen rage hayaki da kuma kiyaye ingancin iska.
Dublin ma ya samu sakamako mai kyau, sakamakon ƙarancin gurɓacewar muhalli da kuma shirye-shiryensa masu ƙarfi na yaƙi da sauyin yanayi, ciki har da burin cimma yanayin da ba a fitar da iskar carbon mai yawa zuwa yanayi ba nan da shekarar 2030.
4. Rashin tsoro
Fasaha ce ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar wasu daga cikin biranen da suka fi saurin ci gaba a cikin wannan ma'auni.
San Jose, wanda yake matsayi na takwas a jerin gaba ɗaya, shi ne birnin da ke da mafi girman GDP ga kowane mutum a cikin jerin.
Kasancewar manyan kamfanonin fasaha na Silicon Valley, kamar Alphabet, kamfanin da ya mallaki Google, Apple da Nvidia, na daga cikin manyan dalilan wannan sakamakon.
A San Francisco, birnin da ke makwabtaka da San Jose kuma yake da kamfanoni kamar Meta, Uber da Salesforce, motoci masu tuka kansu ba tare da direba ba sun zama wani ɓangare na harkokin sufuri na yau da kullum.
Hakan na bai wa mazauna da masu amfani da su damar ganin irin yadda sufuri a birane zai iya kasancewa a nan gaba a wasu sassan duniya.
Tallinn, babban birnin Estonia, shi ma yana cikin jerin "biranen da ke tasowa", saboda saurin bunƙasar fannin fasaha da kuma yadda ake amfani da fasahar ɗan Adam ta wucin gadi fiye da sauran manyan biranen Turai.
Manyan ayyuka kamar Rail Baltica, wanda ake sa ran zai haɗa ƙasashen Baltic nan da shekarar 2030, an tsara su tare da ba da fifiko ga tsarin "digital first".
Wannan na nufin sanya fasahar zamani a sahun gaba tun daga farkon matakan gini har zuwa lokacin gudanar da aikin.
Wannan tsarin zai bai wa dukkan hanyar jirgin ƙasa damar amfani da makamashi mai sabuntawa, da kuma tsarin sadarwar wayar hannu na 5G, maimakon dogaro da fitilun gargajiya na siginar jirgin ƙasa.
A ƙarshe, matsayi na biranen da suka fi jan hankalin mutane a duniya a shekarar 2026 bai dogara da abu guda ba.
Ƙarfin tattalin arziki, ƙwararrun ma'aikata, al'adu masu armashi, muhalli mai kyau, fasahar zamani da ingancin rayuwa su ne abubuwan da suka haɗu suka sa waɗannan birane suka zama wuraren da mazauna da matafiya daga sassan duniya ke sha'awar zuwa.
Manyan birane 10 mafi fice a duniya a shekarar 2026
A cewar Oxford Economics Global Cities Index na 2026, birane 10 da suka zo kan gaba su ne:
New York, Amurka
London, Birtaniya
Paris, Faransa
Seattle, Amurka
San Francisco, Amurka
Dublin, Ireland
Boston, Amurka
San Jose, Amurka
Tokyo, Japan
Zurich, Switzerland



























