Wane ne Nana Patekar, fitaccen jarumin fina-finan Indiya da ya rasu?

.
Bayanan hoto, Patekar ya gamu da bugun zuciya a gidansa da ke Goa.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Nana Patekar, wanda aka san shi da ƙwarewarsa wajen iya kwaikwayo da kuma salon gabatar da jawabai na musamman, ya rasu a Goa yana da shekara 75.

Ɗansa, Malhar, ne ya tabbatar wa BBC Marathi labarin rasuwar.

Patekar na daga cikin fitattun jaruman da suka yi shuhura a harkar fina-finan Indiya.

Ya lashe Kyautar Fina-finai ta Ƙasa ta Indiya (National Film Award) har sau uku, kuma an san shi da taka rawar jaruman da ke da sarƙaƙiya, waɗanda galibi suke da zafin hali.

Ya kuma taka muhimmiyar rawa a fina-finan Marathi da kuma wasan kwaikwayo na dandali.

An garzaya da shi asibiti bayan an same shi a sume a gidansa da ke Goa a safiyar Alhamis.

Likitocin Asibitin Manipal da ke Goa sun shaida wa kamfanin dillancin labaran ANI cewa, "Duk da ci gaba da yi masa CPR na tsawon mintuna 45, ba a samu nasarar farfaɗo da shi ba."

A ranar Alhamis, Firaministan Indiya Narendra Modi ya jagoranci masu aika saƙonnin ta'aziyya ga iyalan marigayin. Ya kuma yaba da hazaƙarsa da kuma kasancewarsa mutum mai bayyana ra'ayinsa a fili.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Modi ya rubuta a shafinsa na X cewa Patekar ya taka rawar a zo a gani a fina-finai da "za su ci gaba da kasancewa a cikin zukatan jama'a da dama", yana mai cewa rasuwarsa ta "bar babban giɓi a duniyar fasaha".

Shahararren jarumin Bollywood, Akshay Kumar, wanda ya fito tare da Patekar a fim ɗin barkwanci mai suna Welcome, ya tuna da shi a matsayin wani jarumi na musamman wanda muryarsa da kishinsa da kuma gaskiya wajen yin aikinsa ke jan hankalin masu kallo.

Patekar ya fara fitowa a fina-finai a shekarar 1978 a fim ɗin Gaman, sannan ya ci gaba da taka rawa a fina-finai da dama.

Sai dai kuzari da kishinsa wajen yin wasan kwaikwayo a akwatunan talabijin sun kasance abubuwan da ke da wuya a mata da su.

A shekarar 1989, an ba shi damar taka rawa a fim ɗin Parinda, wanda ya sa ya shahara sosai a duk faɗin ƙasar ta Indiya.

Ya lashe kyautarsa ta farko ta National Film Award da kuma kyautar Filmfare Award saboda rawar da ya taka a matsayin wani ɗan bindiga mai suna Anna a fim ɗin.

Bayan haka, bai sake waiwaya baya ba, inda ya taka rawar jarumai da dama da suka kasance abin tunawa a cikin shekarun 1990.

Abubuwan da ya yi sun nuna zurfin basirar da yake da ita wajen wasan kwaikwayo da kuma ƙwarewarsa ta fasaha.

Rawar da ya taka a matsayin Major Chauhan a fim ɗin Prahaar, wanda shi kansa ya shirya kuma ya ba da umarni, ta samu yabo sosai.

Sauran su ne fim ɗin Tirangaa da kuma Pratap Narayan Tilak a Krantiveer, waɗanda ya yi fice har ma ya samu ya samu kyaututtuka.

A lokacin da masu sukar fina-finai suke ganin cewa taka rawar mutane masu yawan magana da zafin rai ita ce babbar ƙwarewarsa, ya karya wannan tunanin ta hanyar yin abin a zo a gani a fim ɗin Khamoshi, inda ya fito a matsayin wani mutum kurma kuma bebe.

.
Bayanan hoto, An haifi Patekar a jihar Maharashtra a shekarar 1951, kuma ya fara sana'ar wasan kwaikwayo ne a gidan wasan kwaikwayo kafin daga bisani ya koma harkar fina-finai.

Fim ɗin Rajneeti na shekarar 2010, wanda Prakash Jha ya ba da umarni, ya ƙara fito da wani sabon salo a rayuwar Patekar a wasan kwaikwayo, inda ya kwaikwayi wani ɗan siyasa mai wayo da dabara.

Rayuwar Patekar a harkar fina-finai ta ƙunshi nau'o'in fina-finai daban-daban. Ya yi nasarar kwaikwayon mutane masu bambancin hali, tun daga ɗan daba har zuwa ɗan sanda.

Ya kuma yi aiki a bayan kyamara, inda ya kasance darakta da marubucin fina-finai.

Kyaututtukan National Film Award guda uku da ya samu saboda fina-finan Parinda, Krantiveer da Agni Sakshi, sun kuma zama shaida kan faɗi da kuma bambancin da ke tattare da rayuwarsa ta sana'a.

Patekar ya kasance mutum mai tasiri a harkar wasan kwaikwayo ta Marathi da Hindi.

Kafin ya shiga fina-finai, ya fara ne da wasan kwaikwayo a dandali, inda ya haɓaka salon isar da saƙo mai ƙarfi, tare da koyon irin ƙwazo da kuzarin da daga baya ya riƙa amfani da su wajen kwaikwayon jarumai a fina-finai.

Purush da Hamidabai Chi Kothi na daga cikin shahararrun wasannin kwaikwayo da ya yi.

Duk da nasarar da ya samu a fina-finai, ya ci gaba da yin wasan kwaikwayon dandali a duk tsawon rayuwarsa ta sana'ar fina-finai.

.
Bayanan hoto, Patekar ya kuma kasance babban jigo mai tasiri a harkar wasan kwaikwayo ta Marathi da Hindi.

An kuma san Patekar da ɗabi'a taimakon al'umma, kuma ya yi fice wajen yin kakkausar suka ga gwamnatin ƙasar.

Ya kasance yana magana kai tsaye ba tare da jin tsoron bayyana ra'ayinsa ba game da ministocin gwamnati da manufofinsu, inda yake bayyana sukar sa a fili.

Batutuwan da suka shafi manoma na daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a wajensa.

Ayyukan sa na taimakon al'umma ba su tsaya ga jawabai kawai ba.

A shekarar 2015, shi da abokin aikinsa a fina-finai Makarand Anaspure sun kafa Gidauniyar Naam, wadda ke aiki wajen tallafa wa manoma da kuma kiyaye albarkatun ruwa a jihar Maharashtra.

Sai dai, rayuwarsa ta sana'a ba ta rasa abubuwan da suka jawo ce-ce-ku-ce ba.

A shekarar 2018, jarumar fina-finai Tanushree Dutta ta zargi Patekar da cin zarafin mata, lamarin da ake zargin ya faru a wajen daukar wani fim shekaru goma kafin lokacin.

A shekarar 2019, an cire sunansa daga cikin waɗanda ake tuhuma, bayan da 'yan sanda suka ce ba su samu isassun hujjojin da za su gurfanar da shi a gaban kotu ba.