Jihohin Najeriya da suke da arzikin man fetur

Kolmani
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Najeriya na daga cikin ƙasashen da suke da ɗimbin albarkatun man fetur, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati tun bayan gano shi.

A yau, jihohi da dama ne ke samar da ɗanyen mai, musamman a yankin Neja Delta, wanda ya kasance cibiyar harkokin man fetur a ƙasar.

Sai dai duk da yawan albarkatun da wasu jihohi ke da su, har yanzu ana ci gaba da muhawara kan yadda arzikin man fetur ya shafi ci gaban tattalin arziki da rayuwar al'ummar yankunan da ake haƙo shi.

Yayin da wasu ke ganin man fetur ya kawo damarmaki da kuɗaɗen shiga masu yawa, wasu kuma na nuna cewa har yanzu akwai ƙalubale na talauci, rashin ababen more rayuwa da matsalolin muhalli a wasu daga cikin yankunan masu arzikin mai.

A shekarun baya-bayan nan, bincike da ayyukan neman man fetur sun bazu zuwa wasu sassan ƙasar, lamarin da ya haifar da fatan cewa ƙarin jihohi za su shiga sahun masu samar da ɗanyen mai.

Hakan ya jawo hankalin masana da masu tsara manufofi kan muhimmancin yadda za a gudanar da albarkatun cikin adalci da kuma anfani da su wajen bunkasa ci gaban kasa baki daya.

Bambancin albarkatun mai

A wata tattaunawa, masanin tattalin arzikin man fetur a Abuja, Farfesa Ahmed Adamu, ya yi bayani kan matsayin jihohin da ke da arzikin man fetur a Najeriya, inda ya ce akwai jihohin da suke fitar da man, sannan akwai jihohin da aka gano man amma ba a fara haƙowa ba.

Masanin harkokin man ya ce ɗanyen mai ya kusan karaɗe sassan ƙasar, sai ya nanata cewa haƙo man na buƙatar ɗimbin kuɗi.

Dangane da yiwuwar samun man fetur a wasu sassan Najeriya, Farfesa Adamu ya bayyana cewa akwai matakai daban-daban na tabbatar da albarkatun mai.

"Akwai wuraren da ake kyautata zaton akwai mai, akwai wuraren da bincike bai kai matakin tabbatarwa ba, sannan akwai wuraren da aka tabbatar da samuwarsa," in ji shi.

Ya ce a halin yanzu mafi yawan man fetur da Najeriya ke da shi, kusan ganga biliyan 40 na ajiyar danyen mai, na fitowa ne daga yankin Neja Delta.

Sai dai ya ce bincike ya nuna akwai alamun man fetur a wasu yankuna kamar Kolmani da ke arewa maso gabashi da kuma wasu sassan jihohin Borno da Sokoto.

"An gano mai a Kolmani, kuma an gudanar da bincike a yankunan Borno da Sokoto. Amma binciken man fetur yana buƙatar maƙudan kuɗaɗe kuma babu tabbacin samun mai a kowane wuri. Shi ya sa gwamnati ke haɗa hannu da kamfanoni masu zaman kansu wajen gudanar da irin waɗannan bincike," in ji shi.

Jihohin da aka tabbatar suna mai

A cewar Farfesa Ahmed Adamu, wanda ya ambato bayanan Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya daga watan Janairu zuwa Agusta, akwai jihohi tara da aka tabbatar suna samar da man fetur a Najeriya.

Waɗannan jihohi su ne:

  • Abia
  • Akwa Ibom
  • Anambra
  • Bayelsa
  • Delta
  • Edo
  • Imo
  • Ondo
  • Rivers.

Masanin ya bayyana cewa daga cikin waɗannan jihohi, guda huɗu ne suka fi sauran yawan samar da ɗanyen mai. Su ne:

  • Akwa Ibom
  • Bayelsa
  • Delta
  • Rivers

Jihohin da aka gano mai

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai duk da cewa waɗannan ne aka tabbatar suna da man fetur a halin yanzu, akwai wasu yankuna da bincike ya nuna yiwuwar samun albarkatun mai a ƙarƙashinsu.

Farfesa Adamu ya ce daga cikin wuraren da ake da kyakkyawar fata akwai filin Kolmani da ya shafi jihohin Bauchi da Gombe, da kuma yankunan Nasarawa da Ebonyi, inda aka gudanar da ayyukan bincike da haƙo mai.

Masanin ya sauran sun haɗa da Benue da Neja da Kogi da Kwara a yankin Bida Basin. Haka kuma akwai Sokoto Basin wanda ya nausa sassan jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi, da kuma Chad Basin da ya ratsa jihohin Borno da Yobe.

A kudu maso yammacin ƙasar kuwa, masanin ya ce akwai Benin Basin wanda ya shiga sassan Ogun, Oyo da Ekiti, yayin da ake kuma ci gaba da bincike da nazarin albarkatun man fetur a jihar Legas.

Duk da hakan, masanin ya jaddada cewa tabbatar da samuwar man fetur na buƙatar cikakken bincike da gwaje-gwaje kafin a ayyana wani yanki a matsayin mai arzikin mai.