Yadda ƴan majalisa 8 suka bar jam'iyyar APC a Zamfara

'
Bayanan hoto, Gwamna Lawal Dare
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da babban zaɓen Najeriya ke matsowa, jam'iyyar APC a Zamfara, jihar da jagoran yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu, Sanata Abdulaziz Yari ya fito na fuskantar ƙalubale.

Wata sabuwar rigima ce ta ɓalle, inda lamarin ya kai ga cewa wasu 'yan majalisar dokokin jihar takwas suka sanar da sauya sheka daga jam'iyyar.

Yan majalisar sun bayyana matakin nasu ne a zaman majalisar dokokin jihar da aka gudanar a birnin Gusau, inda aka karanta wasiƙun murabus ɗinsu a hukumance.

Wannan ba shi ne karon farko da ake fama da taƙaddamar siyasa a jihar, wanda ke ƙazancewa har ya dauki hankali ba.

A zaɓen shekara ta 2019 wani rikicin siyasa mai muni ya turnuƙe jam'iyya mai mulki, lamarin da ya sanya kotu ta rushe dukkanin zaɓaɓɓun ƴansiyasa a jihar bayan zaɓe, tare da miƙa dukkanin muƙaman ga jam'iyyar adawa.

A baya-bayan nan gwamnan jihar Dauda Lawal ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulkin ƙasar.

Sai dai harƙallar siyasa da ke tsakanin jiga-jigan ƴan siyasa na jihar na ci gaba da haifar da takun-saƙa.

Waɗanda suka sanar da ficewar tasu sun fito ne daga mazaɓu daban-daban na jihar, ciki har da Bakura da Talata Mafara ta Kudu da Maradun ta Ɗaya da Gummi ta Ɗaya da Kaura Namoda da sauran su.

Matakin da jam'iyyar ta APC ta ce duk da ba ta ji dadinsa ba.

A cikin wasikun sauya sheka da suka aika, yan majalisar sun ce sun ɗauki wannan matsayi ne bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki a mazabunsu.

Sun danganta matakin da abin da suka kira rashin hadin kai tsakanin shugabannin jamiyyar a jihar da kuma zargin rashin adalci da yaudara a harkokin siyasa.

Sun kuma nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al'amuran tsaro a wasu yankunan da ke fama da hare haren 'yan bindiga.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ibrahim Tukur, daya daga cikin yan majalisar dokokin jihar da suka fice daga jam'iyyar ta APC ya shaida cewa sun yi la'akari da wasu abubuwa kafin suka yanke shawarar sauya sheƙar.

''Mun yi kusan wata 32 ana wannan hobbassa da mu kan abin da da ya shafi al'ummarmu, ba ma tsaron kaɗai ba, hatta tallafi da muke zaton za a ba mu. Ana kashe mata sannan yara suna gararamba kuma babu wani mataki wanda jiha ta dauka domin kare rayuwar wadannan alumma'' in ji shi.

Zamfara na fama da matsalar tsaro da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Yanzu haka a garuruwa irin su Bunguɗu al'umma na kwana ba tare da sun runtsa ba sanadiyyar mahara da ke yunƙurin shiga garin a kusan kowane dare.

Hakan na zuwa ne bayan tsirar da shugaban ƙaramar hukumar ya yi, bayan da ya kwashe makonni a hannun ƴan bindiga waɗanda suka sace shi daga gidansa.

Tukur ya ce har yazu ba su koma wata jam'iyya ba, amma ya ce kusan dukkanin jam'iyyun adawa na zawarcin su.

''Mu takwas muka fice, biyar sun fito daga yankin Zamfara ta yamma, sannan akwai wanda suka fito daga Zamfara ta tsakiya da kuma Bungudu,'' in ji shi.

Sai dai mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Mustapha Jafaru Kaura ya shaida wa BBC cewa dalilan da 'yan majalisar da suka sauya sheka suka bayar, cike suke da kura-kurai:

''Ina son na fada wa jama'a cewa su wadannan yan majalisa , yan majalisar dokokin jihar Zamafara ne da aka dakatar kuma dalilan da suka zayyana na babu jagoranci na kwarai wannan labari ne, saboda in babu jagoranci na kwarai da ba su zamo yan majalisu a shekarar 2023 ba''.

Masana dai na kallon wannan mataki a matsayin wani babban sauyi da zai iya yin tasiri ga siyasar jihar Zamfara a zaben shekarar 2026.