Cristiano Ronaldo: Shin ko Portugal ta ci moriyar ganga?

Ronaldo
    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A tsawon sama da shekara 20 sunan Cristiano Ronaldo ya zama tamkar alamar ƙwallon ƙafa ta Portugal. Daga matashin ɗan wasa da ya fara bugawa ƙasar wasa a shekarar 2003 zuwa gwarzon da ya jagoranci ƙasar zuwa lashe manyan kofuna a tarihi.

Ronaldo ya sauya matsayin Portugal daga tawagar da ba ta yi suna ba a fannin taka leda zuwa ɗaya daga cikin manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa a duniya.

Sai dai duk da waɗannan nasarori, akwai masu tambayar ko Portugal za ta girmama shi yadda ya kamata idan ya yi ritaya daga buga wa ƙasar tamaula.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai Hukumar Kwallon Kafa ta Portugal (FPF) ta dakatar da Cristiano Ronaldo na wucin gadi.

A wata sanarwa, FPF ta ce an sanya masa "dakatarwa ta wucin gadi" a ranar 9 ga Oktoba, kuma an baiwa lamarin fifiko domin a kammala bincike cikin gaggawa.

Dokokin FPF sun tanadi cewa duk ɗan wasan da ya ƙi halarta ko ya bar aikinsa na ƙasa ba tare da izini ba zai iya fuskantar dakatarwa daga wata ɗaya zuwa shida, tare da tara.

Shugaban FPF, Pedro Proenca, ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Portugal cewa:"Wannan lokaci ne na natsuwa da kwanciyar hankali. Dukkanmu muna zaune tare domin tattaunawa.

Har yanzu ana ta mamaki yadda aka samu rashin jituwa tsakanin Ronaldo da kocin Portugal da ta kai mai taka leda a Al-Nassr ya bar sansanin kasar a Denmark.

Lionel Messi abokin hamayyar Ronaldo ne a fannin taka leda a duniya, sai dai kuma Argentina ta yi wa kyaftin dinta bikin ban kwana a wasan sada zumunta da Benin.

Shin ya da ce itama Portugal ta karrama gwarzon nata da yi masa biki na kasaita da zarar ya sanar da yin ritaya?

Yaya matakin Portugal a kwallon kafa kafin zuwan Ronaldo?

Ronaldo
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafin Ronaldo ya fara buga wa Portugal wasa a watan Agustan 2003, ƙasar na da tarihi mai tsawo amma ba tare da lashe wata babbar gasa ba.

Portugal ta halarci gasar cin Kofin Duniya sau uku kacal (1966 da 1986 da kuma 2002), sannan ta samu shiga gasar Euro sau uku kacal kafin zamanin Ronaldo ya fara taka mata leda. Bugu da ƙari ba ta taɓa lashe wata babbar gasa ba.

Duk da kasancewar taurarin da suka wakilci kasar kamar Eusebio da Luis Figo da Rui Costa, Portugal ta yi fama da rashin taka rawar gani a manyan wasanni kuma ba ta kai matsayin ƙasashen da ke cin manyan kofuna ba kamar Jamus ko Faransa ko Spain ba.

Nasarorin da Portugal ta samu tare da Cristiano Ronaldo.

Babu shakka Ronaldo ne ya zama ginshiƙin mafi nasarrorin da kasar ta samu a tarihin ƙwallon ƙafar Portugal.

1. Kofin Euro 2016

Wannan ita ce babbar nasarar farko da Portugal ta samu a tarihi. A karkashin jagorancin Ronaldo a matsayin kyaftin, Portugal ta lashe Euro 2016 bayan doke Faransa a wasan ƙarshe.

2. UEFA Nations League 2019

Ronaldo ya sake jagorantar Portugal zuwa lashe gasar Nations League na farko a tarihi a tsakanin tawagogin Turai.

3. UEFA Nations League 2025

Portugal ta ƙara wani babban kofi a shekarar 2025, abin da ya sa adadin manyan kofunan da ƙasar ta lashe a zamanin Ronaldo ya kai uku.

4. Tarihin da ya kafa da babu kamarsa a Portugal

Ronaldo shi ne:

Wanda ya fi kowa yawan buga wa ƙasa wasa a tarihi mai 234

Wanda ya fi kowa yawan cin ƙwallaye mai 146.

Wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin gasar Euro.

Me ya sa aka yi wa Messi bikin ban kwana?

Ronaldo da Messi

A Argentina, Messi ya cika babban burin da al'umma suka dade suna jira, wato lashe Kofin Duniya a 2022. Wannan nasara ta sanya kusan kowane dan Argentina ya ɗauke shi a matsayin gwarzon ƙasa.

Bayan nan ya lashe Copa America biyu, bayan da aka baya ake sukar tsohon dan wasan Barcelona da cewar baya saka kwazo a wasannin kasa kamar yadda yake yi a Sifaniya.

An taba tunzarar Messi da ta kai ya sanar da cewar ya yi ritaya, kafin daga baya a rarrashe shi ya koma fagen taka leda.

Sai dai kuma ana gama gasar cin kofin duniya da aka yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico ya sanar da yin ritaya.

Hakika babu wani abun da Messi zai nema sabo a fannin taka leda, kuma shekaru sun fara ja, saboda haka magoya baya sun taya shi murnar rataye takalman da ya yi.

Haka kuma akwai banbanci tsakanin Argentina da Portugal wajen karrama duk wanda ya taka rawa a tawagar.

Bambancin Al'adu

Argentina na da al'adar girmama fitattun yan wasanta sosai. Diego Maradona ya samu makamancin wannan matsayi. Portugal kuwa tana da al'adar da ta fi karkata ga kungiyar ƙasa gaba ɗaya maimakon mutum guda.

Rarrabuwar Ra'ayi Kan Ronaldo

Ko da yake Ronaldo ya kawo nasarori masu yawa ga tawagar Portugal, sai dai wasu lokuta yana samun suka da yawa, saboda halinsa na son yin takara da tarin buruka da yadda yake amsa tambayoyin manema labarai, da kuma yadda wasu ke ganin ya dade yana riƙe matsayi a tawagar. Wannan ya haifar da cece-kucen cewar ya kamata ya matsa ya baiwa wasu dama, domin lokacinsa ya wuce.

Shi kuwa Ronaldo yana ganin har yanzu yana da rawar da zai taka yana kuma da burin da yake son cimma, sai dai lokuta da dama ya sha sanar da cewar idan babu gudunmuwar da zai bayar ya kamata a sanar da shi ya kauce daga tawagar ta Portugal.

Shin Portugal ta ci moriyar ganga za ta yarda kwaure?

Ronaldo da Messi

Ronaldo ya fara buga wa Portugal tamaula ba tare da lashe manyan kofuna ba, amma a zamaninsa ƙasar ta dauki Euro da Nations League sau biyu, ta kuma zama tawagar da ke shiga manyan gasa akai-akai.

Ko da yake ra'ayoyi kan rawar da yake takawa a halin yanzu na iya bambanta, tarihi zai tuna cewa babu wani ɗan wasan Portugal da ya yi tasiri kamar Ronaldo. Ya lashe manyan kofi uku da kafa tarihi na ban mamaki, kuma ya sanya sunan Portugal cikin manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa na duniya.

A ƙarshe, koda Portugal ta shirya masa kasaitaccen bikin ban kwana kamar yadda aka yi wa Messi ko kuma ba za ta yi hakan ba, babu abinda zai canza cewar Cristiano Ronaldo ya rubuta sunansa a kan zinare a tarihin Portugal, kuma gudunmawarsa na daga cikin mafi girma da ɗan wasa ya taɓa bayarwa ga ƙasarsa.