Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ta yaya ƙasashen duniya 9 suka mallaki makamin nukiliya?
Makaman nukiliya sun sauya yadda ƙasashe ke kallon yaƙi da tsaro gaba ɗaya.
A yau, akwai ƙasashe tara da aka sani da mallakar irin waɗannan makamai da suka haɗa da Amurka da Rasha da Birtaniya da Faransa da China da Indiya da Pakistan da Isra'ila da kuma Koriya ta Arewa.
Sai dai waɗannan ƙasashe ba su kai wannan mataki ta hanya ɗaya ba. Wasu sun fara haɓaka makaman nukiliya tun lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, wasu kuma a lokacin Yaƙin Cacar Baki tsakanin manyan ƙasashen duniya.
A wasu ƙasashe kuwa, gasa da maƙwabta da kuma fargabar tsaro su ne suka kasance manyan dalilan da suka sa suka nemi mallakar makaman nukiliya.
Ta yaya ƙasashen suka mallaki makamin nukiliya?
Amurka ce ƙasa ta farko a duniya da ta fara ƙera makaman nukiliya ta hanyar wani sirrin shiri da aka sani da Manhattan Project a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu.
A watan Agustan 1945, ta yi amfani da bama-baman nukiliya guda biyu a biranen Hiroshima da Nagasaki na Japan.
Wannan mataki ya nuna irin ƙarfin da waɗannan makamai suke da shi, tare da ƙaddamar da gasar mallakar makaman nukiliya tsakanin ƙasashen duniya.
Tarayyar Soviet (yanzu Rasha) ta fara ƙoƙarin ƙera bam ɗin nukiliya tun lokacin yaƙin, kuma ta gudanar da gwajinta na farko cikin nasara a shekarar 1949.
Hakan ya kawo ƙarshen mamayar da Amurka ke yi ita kaɗai a wannan fanni, tare da haifar da gagarumar gasar makamai tsakanin ƙasashen biyu.
Birtaniya kuwa, wadda ta yi aiki tare da Amurka a lokacin yaƙin, ta zama ƙasa ta uku da ta mallaki makaman nukiliya a shekarar 1952.
Faransa da China sun biyo baya a shekarun 1960, inda Faransa ta gudanar da gwajinta na farko a 1960, yayin da China ta yi nata a 1964.
A wannan lokaci, Amurka da Tarayyar Soviet da Birtaniya da Faransa da China sun riga sun kafa kansu a matsayin ƙasashen da suka mallaki makaman nukiliya.
Fargabar cewa wasu ƙasashe za su iya bin sawunsu ce ta sa aka samar da Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Makaman Nukiliya (NPT) a shekarar 1970.
Indiya ta shiga sahun waɗannan ƙasashe a shekarar 1974 duk da cewa ba ta sanya hannu a yarjejeniyar NPT ba.
Pakistan, wadda ita ma ba ta cikin masu rattaba hannu kan yarjejeniyar, ta biyo baya, kuma gasa ta fuskar tsaro tsakaninta da Indiya na daga cikin manyan dalilan da suka sa ta haɓaka wannan makami.
Pakistan ta gudanar da gwajinta na farko a shekarar 1998.
Isra'ila kuwa tana da matsayi na musamman. Ba ta taɓa tabbatarwa ko musanta a hukumance cewa tana da makaman nukiliya ba, bisa wata manufa da ake kira "nuclear ambiguity" wato barin al'amarin cikin duhu.
Haka kuma, Isra'ila ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar NPT ba.
Sai dai bayanai da kimantawar masana sun sa ake saka ta cikin jerin ƙasashen da ake zargin suna mallakar makaman nukiliya, inda wasu ƙididdiga ke nuna cewa tana iya mallakar kusan kawunan yaƙin nukiliya 90.
Koriya ta Arewa kuma ta taɓa kasancewa mamba a yarjejeniyar NPT, amma ta janye daga cikinta a shekarar 2003, tana mai danganta matakin da zaman ɗarɗar siyasa da soja tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu.
Ta gudanar da gwajinta na farko na makamin nukiliya a shekarar 2006, kuma tun daga wannan lokaci take ci gaba da bunƙasa shirinta na makaman nukiliya da kuma makamai masu linzami.
Me ya sa sauran kasashe suka yi watsi da shirinsu na mallakar makamin?
Shirin ƙasa na ƙera makaman nukiliya ba lallai ba ne ya kai ga kammala mallakar waɗannan makamai.
A tarihin duniya, akwai ƙasashe da dama da suka taɓa fara shirye-shiryen ƙera makaman nukiliya, amma daga bisani suka yi watsi da su.
Daga cikin irin waɗannan ƙasashe akwai Brazil da Sweden da Switzerland, waɗanda suka dakatar da ƙoƙarinsu kafin su kai ga mallakar makaman.
Mafi shahararren misali shi ne Afirka ta Kudu. Ƙasar ta yi nasarar ƙera makaman nukiliya, amma daga baya ta rusa su tare da kawo ƙarshen shirinta na nukiliya.
Wannan mataki ya samo asali ne daga wasu dalilai da suka haɗa da ƙarshen mulkin wariyar launin fata (apartheid), raguwar rikice-rikicen yankin da kuma sauyin yanayin siyasar duniya.
Bayan rugujewar Tarayyar Soviet a shekarar 1991, ƙasashen Ukraine, Belarus da Kazakhstan sun gaji wasu daga cikin makaman nukiliyar Soviet da ke kan ƙasashensu.
Sai dai dukkaninsu sun yi watsi da mallaka ko amfani da waɗannan makamai.
Ukraine ta miƙa makaman nata ne ƙarƙashin Yarjejeniyar Budapest ta shekarar 1994, inda a madadinsu ta samu tabbacin kariya da tsaro daga Amurka da Birtaniya da kuma Rasha.
Wannan ya kasance wani muhimmin mataki a ƙoƙarin rage yaɗuwar makaman nukiliya a duniya.
Adadin makaman nukiliya da duniya ta mallaka
Saboda yawancin gwamnatoci ba sa bayyana cikakkun bayanai game da yawan makaman nukiliyar da suke da su, babu wata ƙididdiga da za a iya cewa tabbatacciya ce ɗari bisa ɗari.
Sai dai, a cewar Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Duniya ta Stockholm (SIPRI), ƙasashe tara masu mallakar makaman nukiliya suna da kimanin makaman 12,187 zuwa watan Janairun 2026.
Daga cikin waɗannan, kusan 9,745 suna cikin rumbunan soji domin amfani da su idan buƙatar hakan ta taso, yayin da kusan 4,012 tuni aka ɗora su a kan makamai masu linzami ko jiragen yaƙi.
Ko da yake jimillar makaman nukiliya a duniya na raguwa tsawon shekaru, SIPRI ta yi gargaɗin cewa ƙasashen da suka mallaki irin waɗannan makamai na ci gaba da inganta su tare da ƙirƙirar sabbin hanyoyin da za su iya kai su ga wuraren da ake niyya.
Har yanzu, Amurka da Rasha ne ke riƙe da mafi yawan kaso na makaman nukiliya a duniya, lamarin da ke sa ƙasashen biyu su kasance manyan masu tasiri a fagen ƙarfin soji da tsaron duniya.
Za a iya samun wasu ƙasashe su mallaka?
Muhimmancin wannan tambaya ya ƙaru sosai a 'yan shekarun nan, musamman sakamakon muhawarar da ake yi kan shirin nukiliyar Iran.
Iran mamba ce a Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Makaman Nukiliya (NPT), kuma ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kawai, ba ƙera makaman nukiliya ba.
Sai dai masana na gargaɗin cewa idan Iran ta mallaki makaman nukiliya, hakan na iya sauya yadda ake kallon batun tsaro a Gabas ta Tsakiya, tare da sa wasu ƙasashen yankin su sake nazarin manufofinsu game da makaman nukiliya.
Duk da haka, shiga sahun ƙasashen da ke mallakar makaman nukiliya ba abu ne mai sauƙi ba.
Duk ƙasar da ke son ƙera irin waɗannan makamai tana buƙatar kuɗaɗe masu yawa, fasahar zamani da kuma kayan aiki da ƙasashen duniya ke sanya ido sosai a kansu.
Haka kuma, wannan tsari na iya ɗaukar shekaru masu yawa kafin ya kai ga nasara.
Saboda haka, duk da fargabar da ake da ita na cewa adadin ƙasashen da ke mallakar makaman nukiliya zai iya ƙaruwa, manyan ƙalubalen siyasa da tattalin arziki da kuma na fasaha na ci gaba da kasancewa babban cikas ga duk wata ƙasa da ke son shiga wannan sahu.