Tottenham ta doke Aston Villa har gida ta fito daga ƙarshen teburi

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta fito daga ƙarshen teburin gasar Premier bayan doke Aston Villa har gida da ci 1-2.
Tottenham ta da take matsayi na 18 gabanin wannan wasan ta dawo matsayi na 17 a teburi, saman West Ham da ke matsayi na 18.
Spurs ta samu nasarar ne bayan wani wasa da ta buga na kwarewa da zafin nama tsakaninta da Aston Villa.
A minti na 12 da fara wasan ɗan wasan tsakiya na Tottenham Gallagher ya jefa kwallo ta ɗaya, abin da ya sa ƙungiyarsa ta shiga gaba kenan a wasa.
Sai kuma a daidai minti na 25 ɗan wasan gaban ƙungiyar ɗan Brazil Richarlison ya jefa kwallo ta biyu wadda ta kwantar da hankalin ƙungiyar ta ba ta damar ci gaba da jan ragamar wasan.
A ƙarƙashin teburin Premier, akwai Wolves da ta gama faɗawa championship tare da takwararta Burnley da itama ta dawo gasar a bana.
Yanzu cikon ƙungiya ta uku da za ta faɗa gasar Championship ake nema tsakanin ƙungiyoyin birnin London biyu, Tottenham da West Ham United.
Maki ɗaya ne ya raba ƙungiyoyin biyu, inda Tottenham dake matsayi na 17 ke da maki 37, ita kuma West Ham da ta sha kashi a hannun Brentford ke matsayi na 18 da maki 36.
Tottenham na da wasanni uku da suka rage mata da suka haɗa da na Leeds United wanda Spurs ɗin za ta ƙarbi baƙunci, sai wanda za ta Stamford Bridge inda za ta fafata da Chelsea, sannan ta ƙarƙare gasar a gida da wasa tsakaninta da Everton.
A gefe ɗaya kuma Wset Ham United za ta karɓi baƙuncin Arsenal da ke saman teburin gasar da maki 76 bayan buga duka wasanninta 35.
Wasa ne da zai ɗuki hankalin 'yan kallo ganin cewa wasan na hamayyar birnin London ne, sa'annan kungiyoyin biyu kowacce cikinsu na da abin da ta sa a gaba, Arsenal na son cin kofi, yayin da ita kuma West ham ke neman tsira daga komawa gasar Championship tun shekarar 2004/05.
Kakar bana na cikin waɗanda Tottenham za ta tuna ba tare da fatan sake gani ba a nan gaba, ko da yake rashin ƙoƙarin nata na da sanadin jinya da mafi yawan yan wasanta 11 farko ke fama da shi.









