Yadda 'yan bindiga suka kashe manoma 14 a gonakinsu a Sakkwato

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Aƙalla manoma 14 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hare-hare a garuruwa kusan bakwai da ke ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni a jihar Sakkwato.

Rahotanni sun ce maharan sun farmaki manoman ne yayin da suke gudanar da ayyukan noma a gonakinsu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutanen tare da haddasa fargaba a tsakanin al'ummomin yankin.

Honarabul Muhammad Sa'idu Bargaja, mai wakiltar mazabar Isa da Sabon Birni a majalisar wakilan kasar, ya shaida wa BBC cewa barayin sun daidaici lokacin da aka samu ruwa yayin da manoma ke fitowa gonakinsu don yin shuga, inda suke amfani da wannan dama wajen aiwatar da manufarsu.

''Wannan al'amari ya faru ne a yammacin Isa, da Tidibale, da Mansalawa, da Tsabare, da Hadawa, da Masawa, Gidan Nagora,

Ya ce baya ga wadanda aka kashe akwai kuma mutane da dama da yanzu haka ke cikin daji bayan yan bindigar sun yi awon gaba da su.

Dan majalisar ya shaida wa BBC cewa ko a makon da ya gabata sai da yan fashin suka kai wa mutane hari tare da kashe kimanin mutum bakwai a wurare daban-daban.

Mazauna yankunan sun ce hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen noma da kuma shuka amfanin gona, abin da ya sa manoma da dama ke nuna damuwa kan komawa gonakinsu.

Ana fargabar cewa rashin tsaro a yankunan na iya yin tasiri ga harkokin noma a bana, musamman idan ba a ɗauki matakan da za su tabbatar da tsaron manoma ba.

Jihar Sakkwato na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka dade suna fama da hare-haren 'yan bindiga, musamman a ƙananan hukumomin da ke makwabtaka da jamhuriyar Nijar. A shekarun baya-bayan nan, yankunan Isa, da Sabon Birni, da Goronyo, Tangaza da Gudu sun sha fama da hare-hare, sace-sacen mutane da kuma tilasta wa mazauna kauyuka gudun hijira.

Matsalar tsaron ba ta tsaya a Sakkwato kaɗai ba. Jihohin Zamfara da Katsina, waɗanda ke makwabtaka da ita, sun kasance daga cikin wuraren da hare-haren 'yan bindiga suka fi kamari, inda ake yawan kashe mutane, sace su domin neman kuɗin fansa da kuma kai hare-hare kan ƙauyuka.

Masana da hukumomi sun danganta ci gaban wannan matsala da ƙarancin tsaro a yankunan karkara, da yaɗuwar makamai da kuma sauyin yanayin rayuwa da ya ƙara tsananta rikice-rikicen da ke tsakanin al'ummomi.

A jihar Kebbi ma, wadda ke iyaka da Sakkwato, hare-haren 'yan bindiga da garkuwa da mutane sun ci gaba da kasancewa barazana ga rayuka da dukiyoyi, musamman a yankunan Danko/Wasagu da sauran ƙananan hukumomin da ke kusa da dazuka da kan iyaka.

Masu lura da al'amura na gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare kan manoma na iya yin tasiri ga samar da abinci a yankin arewa maso yamma, kasancewar dubban manoma na fargabar komawa gonakinsu. Rahotanni sun nuna cewa matsalar tsaro ta riga ta haddasa ficewar mutane da dama daga garuruwansu, da kuma durkusar da harkar noma a wurare da dama.

Mazauna yankunan da abin ya shafa sun yi kira ga gwamnati da jami'an tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyi, tare da samar da tsaro ga manoma yayin da kakar noma ke ƙara kankama.