Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su-34M: Jirgin yaki kirar Rasha da kasashen Afirka suke rububi
Nahiyar Afirka ta kai wani mataki a ɓangaren makaman soji, bayan rahotanni sun bayyana cewa jirgin yaƙin Rasha mai suna Su-34m ya isa ƙasar Algeria.
Mallakar wannan jirgin ya ja hankali matuƙa sosai, inda ya buɗe wata sabuwar muhawara kan ko dai an fara sabuwar gogayya ce wajen mallakar manyan makamai yaƙi a nahiyar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Afirka ke gogoriyon mallaka da ƙara ƙarfin soji, musamman ta hanyar amfani da fasaha.
Masana tsaro na cewa samun jirgin yaƙin a Afirka ya wuce maganar cewa wata ƙasa ta mallaki babban jirgin yaƙi, inda suke ganin hakan a matsayin cigaba babba a ƙasar ta Afirka ta Yamma da ma nahiyar baki ɗaya.
Bayan haka, samun jirgin Su-34M na ƙasar Rasha wata ƴar manuniya ce da ke ƙara bayyana cewa Rasha na ƙara kutsawa a Afirka, musamman ƙasashen da suke ta'allaƙa da Rasha wajen makamai.
Babbar tambayar da ake yi yanzu ita ce shin samun jirgin a Afirka zai canja yanayin ƙarfin soji a ƙasashen Afirka, ko kuma kawai harka ce ta kasuwancin makamai tsakanin ƙasashen duniya.
Wane irin jirgi ne Su-34M?
Jirgin Su-34M babba jirgin yaƙi ne na Raha mai cin dogon zango da aka tsara domin ƙaddamar da hari ta ƙasa da ta sama da ta ruwa da kuma tsaron sararin samaniya duk a tare.
Kamfanin Sukhoi, mallakin United Aircraft Corporation na Rasha na ya haɗa jirgin yaƙin.
Duk da cewa na kamfanin Rasha ne, jirgin Su-34M na cikin jiragen da ƙasar ta haɗa domin amfanin abokan hulɗarta.
A game da Afirka, Algeria na cikin ƙasashen farko-farko a nahiyar da suka kasance cikin tsare-tsaren jirgin tun a farko. Wannan ya sa jirgin ya zama na dabam, saboda yawancin ƙasashen Afirka sun fi amfani da tsofaffin jiragen ƙasashen yamma ko Rasha, kamar MiG da Su-30.
Don haka mallakar jirgi Su-34m ta buɗe wata babbar ƙofar kasuwanci da alaƙar soji tsakanin Rasha da ƙasashen Afirka.
Wane aikin soji za a yi da Su-34M?
Ana tsara jirgin Su-34M ne domin kai hari mai cin dogon zango, sannan yana iya jigilar bama-bamai da wasu makamai, har da masu cin dogon zango.
Jirgin na iya tafiya mai tsawo ba tare da buƙatar ƙara man jirgin sama ba, wanda ke sauƙaƙa masa kai hare-hare da sauran aikace-aikace.
Haka kuma jirgin na da tsarin laturoni mai kyau da inganci, wanda ke taimaka masa wajen tserewa daga tsaron sararin samaniyar wuraren da yake aiki.
Haka kuma jirgin na iya aiki komai lalacewar yanayin sararin samaniya, inda yake iya kutsawa ya yi aiki a yanayin ruwa da iska da sauran yanayi da ake mara kyau ne da ke hana jirgi aiki.
A ɓangaren tsari, jirgin na Su-34M na da kujerar direba guda biyu ba kamar sauran jiragen yaƙin ba. Wannan ya sa jirgin ke da daɗin aiki mai yawa da tafiya mai nisa cikin sauƙi.
Jimilla dai ana ganin jirgin a matsayin daga ciki jirage masu ƙarfi sosai, musamman idan aka yi la'akari da tsarin jirgin na kai hare-hare da ɓangaren sadarwa na zamani.
Shin jirgin Su-34M zai sauya salon ƙarfin sojin ƙasashen Afirka?
Zuwan jirgin Su-34M Afirka zai ƙara zafafa muhawara kan yanayin ƙarfin sojin ƙasashen Afirka, musamman arewacin Afirka, inda ƙasashe irin su Morocco da Algeria da Masar suke ta ƙara zuba kuɗaɗe a ɓangaren tsaro.
Duk ƙasashen suna ƙara ƙoƙari wajen inganta tsaron sararin samaniyarsu da mallakar makamai masu linzami da ƙarfin iko a nahiyar.
Ƙasashe irin su Masar na da jirage kamar F-16 da Rafale da Mig-29, Morocco na da irin su F-16 kuma tana da alaƙar tsaro sosai da Amurka da Isra'ila.
Amma duk da haka, idan aka kwatanta jiragen sauran ƙasashen da Su-34M, za a iya cewa yanzu Algeria ta wuce sauran ƙasashen a wannan ɓangaren, musamman ida aka yi la'akari da jiragen da suka fi yawa na F-16 da Rafale.