Yadda wata barasa haɗin gida ke kashe wasu mutane a Najeriya

Asalin hoton, Mobolaji Olatunde/BBC and Ondo Police
Elo Moses, mai shekara 34 da haihuwa kuma mai sana'ar tuka babur (okada), ya gama aikinsa a ranar da ya yanke shawarar fita tare da abokansa domin ya sayi barasa.
An yi ruwan sama a ranar kuma yanayin ya yi sanyi sosai, don haka yana son ya ɗan dumama jikinsa kafin ya koma gida.
Ya je wurin da ya saba zuwa tare da wasu abokansa biyu, inda ya sayi wata giya da aka haɗa a gida, sannan ya sha ta a wurin. Bayan ƴan mintuna kaɗan, ya fara nuna alamun rashin lafiya. Daga nan aka garzaya da shi asibiti, inda ya rasu a can.
Ƙanwarsa, Abigail, wadda ke tare da shi ƴan lokuta kafin rasuwarsa, ta ce Moses ya gaya mata cewa yana zargin abin da ya sha ne ya jawo masa matsalar.
Ta ce: "Yayana yana acaba ne. Bayan da aka yi ruwan sama a ranar, sai ya je ya sayi giya a wani wuri. Ya tafi tare da abokansa uku, biyu daga cikinsu sun sayi giyar, amma na ukun ba shi da kuɗi, don haka bai saya ba.
"Yayana yana shan giyar, nan take ya yi barci a kan kujera. Da alama giyar ta fara yin tasiri a jikinsa, amma bai ce komai ba," in ji Abigail.

Asalin hoton, Abigail Moses
Abigail ta bayyana cewa daga baya ne wani abokin ɗan'uwanta ya kira mahaifiyarsu kafin a garzaya da shi asibiti. Amma ta ce ɗan'uwanta bai faɗa musu da wuri cewa ya sha wani nau'in giya ta gargajiya da aka gauraya ba.
Ta ce a lokacin da ɗan'uwanta ke dab da mutuwa ne ya amsa cewa yana zargin abin da ya sha ne ya jawo masa matsalar, amma a lokacin babu abin da za a iya yi domin cetonsa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ce: "Sun yi masa allura, sun ba shi magunguna. Amma da yamma ya kasa tsayawa da ƙafafunsa, kuma duk abin da ya ci ko ya sha sai ya yi amai. Cikinsa ya kumbura, ƙafafunsa suka yi sanyi, sannan ya fara daina gani sosai.''
Yayin da Abigail ke bayyana irin halin ɗan'uwanta, ta ce rasuwarsa ta yi wa danginsu mummunan tasiri, musamman ganin cewa ya bar mata da yara uku.
Ta ce ɗan'uwanta ne kaɗai ɗan'uwan da take da shi, kuma tun bayan mutuwarsa suna fama da wahalar ciyar da matarsa da yaransa da ya bari.
Ta ƙara da cewa: "Ina matuƙar kewar ɗan'uwana, mutuwarsa tana ci min tuwo a ƙwarya. Wannan shi ne karo na farko da na ga irin wannan lamari, mutum ya mutu kamar kaza. Da abin ba a gabana ya faru ba, da ban yarda da shi ba."
Moses ba shi ne kaɗai ya rasu bayan shan irin wannan tsumammiyar giya ta gargajiya ba.
A watan Satumban 2026, mutane da dama sun fara mutuwa ba zato ba tsammani a wasu yankuna da ke jihar Ondo. Daga baya aka gano cewa ba mutuwar haka kawai bace.
An samu waɗannan mace-mace a ƙananan hukumomin Odigbo da ke jihar Ondo a kudu maso yammacin Najeriya, inda aka samu mutane da dama da suka kamu da matsananciyar rashin lafiya ko suka rasu bayan shan giya da magungunan gargajiya da aka sarrafa a gida.
Daga cikin al'ummomin da abin ya shafa sama da shida, garin Araromi-Obu, wanda ke kan iyaka da jihar Ogun, shi ne ya fi fuskantar mace-mace, a cewar mahukunta.
A Araromi-Obu kaɗai, sama da mutum 11 sun mutu nan take, yayin da sama da mutum 50 aka kwantar da su a asibiti.
Binciken 'yan sanda ya gano cewa wani sinadari mai guba ne ke kashe mutanen bayan sun sha wannan gaurayen giya, inda aka tabbatar cewa an gauraya masa sinadarin methanol.
Hukumar NAFDAC ta bayyana cewa an samu jimillar mutane 182 da abin ya shafa, tare da tabbatar da rasuwar mutane 48.
Sama da mutum 100 aka kwantar da su a asibiti, yayin da mutum biyar suka makance gaba ɗaya.
Wata guda bayan aukuwar lamarin, BBC News Pidgin ta ziyarci Araromi-Obu domin jin ta bakin waɗanda lamarin ya shafa da kuma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, don gano yadda wannan mummunan al'amari ya faru.
An kuma tattauna da waɗanda suka tsira da kuma iyalan mutanen da suka rasa 'yan uwansu sakamakon wannan bala'i.
Mun rasa mutum biyu a gidanmu
Wani daga cikin labaran da suka fi tada hankali da BBC ta gano a garin Araromi-Obu shi ne na wasu 'yan'uwa maza biyu da suka halarci wani biki a garin. Bayan an kammala bikin, sun yanke shawarar ci gaba da zama na wasu kwanaki, amma daga baya suka rasu bayan sun sha giyar gargajiya da aka gauraya.
Adesebolu Adenikinju ya yi magana cikin raɗaɗi yayin da yake tuna rasuwar 'yan'uwansa biyu, Adedayo Adenikinju da Kola Adenikinju, waɗanda suka mutu a rana guda.
Ya ce ba su san cewa mai sayar da giyar yana haɗa ta da wasu sinadarai ba. Sai bayan da mutane suka fara mutuwa ne aka gano cewa ana gauraya abubuwa masu haɗari a cikin giyar.
Ya ce: "Mun rasa mutane da yawa. A danginmu kaɗai, na rasa 'yan'uwa biyu masu uba ɗaya. Iyali gaba ɗaya ba su cikin farin ciki saboda wannan babban rashi ne.
Abin da ya fi yi wa Adesebolu ciwo shi ne cewa 'yan'uwansa ba sa zama a Araromi-Obu a da. Sun zo ne saboda bikin da aka gayyace su, kasancewar su manyan jiga-jigai ne a iyalin.
Ya ce: "Mun yi babban rashi kuma abin yana da matuƙar ciwo," yayin da hawaye suka kusa zubo masa.
Adesebolu, wanda shi ma ɗaya ne daga cikin wakilan matasan Araromi-Obu, ya ce bincike ya nuna cewa mai sayar da giyar ya sayi methanol ne maimakon ethanol.
Ya bayyana cewa mutumin yana gauraya sinadarin da ruwa da giya sannan yana sayar wa jama'ar gari.
"Babu wanda ya san cewa an gauraya giyar da wannan sinadari. Ya haɗa wani sinadari da ake amfani da shi wajen adana gawarwaki, mutane kuma suna saya suna sha ba tare da sun san abin da ke cikinta ba."

Asalin hoton, Mobolaji Olatunde/BBC
Wani daga cikin waɗanda suka tsira daga wannan lamari ya shaida mana cewa kaɗan ya sha giyar. Da ya fara jin jikinsa ba daidai ba, sai ya gaggauta daina shanta.
Ya ce waɗanda suka sha da yawa ne suka fi fuskantar haɗari. Amma lokacin da aka fara jin labarin cewa mutane na mutuwa bayan sun sha wannan gaurayen abin sha da aka sarrafa a gida, lokaci ya riga ya kure domin ceto da dama daga cikinsu.
A cewarsa, da aka gano haɗarin da wuri, da an samu damar ceton rayukan wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa. Amma saboda rashin sani da jinkirin gano musabbabin matsalar, mutane da yawa sun riga sun rasa rayukansu.
NAFDAC da 'yan sanda na bincike game da mutuwar
Hukumar NAFDAC ta ce ta fara bincike kan lamarin domin gano ainihin abin da ke cikin abin shan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
An tattara samfura 15 na barasar, waɗanda ba su da wata alama ko bayanin asalinsu, sannan aka kai su dakin gwaje-gwaje domin a gudanar da bincike a kansu. Sakamakon binciken ya nuna cewa samfuran sun ƙunshi sinadarin cannabis indica tare da yawan sinadarin methanol mai matuƙar haɗari.
Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ita ma ta tabbatar da cewa abin shan da ya yi sanadiyyar mace-macen mutanen Araromi-Obu na ɗauke da sinadarin methanol.
'Yan sanda sun kuma sanar da kama wanda ake zargi da sayar da barasar, wanda aka bayyana sunansa da "Meko". Wannan ne sunan da yawancin mutanen da BBC ta tattauna da su suka ce daga gare shi ne mutanen da suka rasu suka sayi abin shan.
A halin yanzu, wasu daga cikin gawarwakin waɗanda suka mutu suna hannun hukumomi domin ci gaba da gudanar da gwajin bayan-mutu (post-mortem), wanda zai taimaka wajen gano ƙarin bayanai game da musabbabin mutuwarsu.
Yaya methanol ke cutar da mutum?
Methanol sinadari ne na masana'antu, kuma ba a samar da shi domin ɗan Adam ya sha ba saboda yana da matuƙar guba.
Ko da mutum ya sha kaɗan daga cikinsa, zai iya cutar da jikinsa. Bincike ya nuna cewa duk da yana kama da barasa a launi da ɗanɗano, yana iya sa mutum ya ji kamar ya bugu tare da fara rashin lafiya.
Idan mutum ya sha methanol, illolinsa ba sa bayyana nan take. Sau da yawa sai bayan wasu sa'o'i yayin da jiki ke ƙoƙarin sarrafa shi da fitar da shi. A lokacin ne hanta ke canza methanol zuwa wasu sinadarai masu tsananin guba.
Waɗannan sinadarai ne ke kai hari ga gabobin jiki, musamman ido da kwakwalwa. Hakan na iya haddasa makanta, suma, lalacewar gabobin jiki da ma mutuwa.
Dokta Christopher Morris, babban malami a Newcastle University, ya bayyana cewa methanol na iya "haifar da lalacewa ga wasu sassan kwakwalwa. Haka kuma idanu suna samun mummunar illa kai tsaye, wanda zai iya jawo makanta."
Me zai biyo baya ga waɗanda abin ya shafa da kuma al'ummar Araromi-Obu?
Dayo Akinro, shugaban matasan Araromi-Obu, ya ce abin ya zo musu a matsayin babban abin mamaki ganin yadda mutane da yawa suka fara mutuwa a lokaci guda.
Ya ce ba zato ba tsammani suka lura da cewa matasa da dama a cikin al'ummar garin suna fama da rashin lafiya, lamarin da ya sa aka garzaya da su asibiti.
A cewarsa, a ranar farko mutum uku ne suka mutu, sannan wani ya rasu washegari.
Ya ce: "Dukansu sun amsa cewa sun sha wannan abin sha. Alamomin da suka nuna iri ɗaya ne, da farko sai su fara rasa gani, bayan wasu sa'o'i kuma jikinsu ya fara karkarwa, daga bisani kuma su mutu."
Daga baya ne aka gano cewa ba barasar da aka saba sayarwa ba ce ke haddasa mutuwar, sai dai kasancewar an gauraya ta da methanol, wani sinadari mai matuƙar guba da haɗari ga rayuwar ɗan Adam.
Yanzu haka a Araromi-Obu, an haramta amfani da giya ta gargajiya da ake sarrafawa a gida. Haka kuma al'ummar garin sun kafa kwamitin sa ido da ke zagayawa daga shago zuwa shago domin bincike da tabbatar da cewa ba a sayar da irin waɗannan kayayyaki masu haɗari.
































