Manchester United na neman Simeone, Chelsea na shirin miƙa tayi kan Scott

Giuliano Simeone
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United za ta sa ido sosai kan ɗan wasan gaba na Atletico Madrid, ɗan ƙasar Argentina mai shekara 23 Giuliano Simeone, yayin da ƙungiyoyin biyu za su kara a gasar Champions League. (Mundo Deportivo)

Chelsea a shirye take ta biya kuɗin da Bournemouth ke buƙata kan dan wasan tsakiya na Ingila mai shekara 23 Alex Scott a watan Janairu, duk da cewa ƙungiyar ta Bournemouth na ci gaba da fatan zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya. (Teamtalk)

Chelsea na buƙatar ta biya aƙalla fam miliyan 50 domin shawo kan Barcelona ta sayar da dan wasan tsakiya na Netherlands, Frenkie de Jong, mai shekara 29, a watan Janairu. (Football Insider)

Ƙungiyoyi da dama na gasar Premier League na sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Inter Milan, dan ƙasar Serbia mai shekara 21 Aleksandar Stankovic. (AS)

Werder Bremen ba ta da damar sayen ɗan wasan gaba na Jamus Niclas Fullkrug, mai shekara 33, wanda ke buga wasa a ƙungiyar a matsayin aro daga West Ham, kuma ƙungiyoyin ba su fara tattaunawa kan yarjejeniyar ta nan gaba ba tukunna. (Sky Sports Germany)

Mai tsaron ragar Belgium Thibaut Courtois, mai shekara 34, ya kusa tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid har zuwa shekarar 2028. (Mundo Deportivo)

Brighton ta bayyana ɗan wasan tsakiya mai kai hari na Red Bull Salzburg, ɗan ƙasar Poland mai shekara 19 Bartosz Mazurek, a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan da take son ɗauka a watan Janairu. (Teamtalk)