'Ni ce mace ta farko da ta fara karatu har matakin NCE a ƙauyenmu'

Mata
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

A wasu ƙauyuka musamman a arewacin Najeriya, al'adu sukan zama cikas ga yara musamman mata wajen samun karatun boko, inda wasu ke ganin ilimi ƴaƴa mata ba shi da amfani sosai.

Wannan ne misalin rayuwar Sakina Abdulkadir, wadda ta kammala makarantar firamare, amma ba ta iya karatu da rubutu ba, amma kuma take da burin zama likita ko ma'aikaciyar asibiti.

Sakina ta taso ne a wani ƙauye da ake ganin ilimin yara mata ba shi da muhimmanci, waɗanda kuma suka yi karatun, suna tsayawa ne a matakin firamare.

Sai dai ba kamar sauran yara matan ba, ita Sakina kammala firamare ke da wuya, sai ta fara tunanin yaya rayuwa za ta kasance mata duk da cewa ta san al'adar ƙauyensu.

A daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin inganta ilimin yara mata a Najeriya, alƙaluma na nuna cewa har yanzu miliyoyin yara, musamman mata ba sa zuwa makaranta.

A Najeriya, musamman arewacin ƙasar dalilai da suka haɗa da talauci, al'adu da kuma matsalolin tsaro ne kan gaba wajen hana yara mata, musamman na karkara zuwa makaranta.

Gwagwarmayar cigaba da karatu

Sakina ta ce a daidai lokacin da take tunanin yadda za ta yi ne sai cibiyar Center for Girl's Education Zaria, ta isa ƙauyensu, wadda ta fara koya musu karatu tun daga farko.

"Suna fara koyar da mu aka fara mana karatu da rubutu da sana'o'in hannu da ma ilimin zamantakewa da sauran su," in ji Sakina wadda ta fito daga wani kauye a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Ta ce a lokacin ne aka yi wa iyayenta caa, "cewa me ya sa za su bar ni in koma makaranta, alhali ga sa'annina sun yi aure. Amma Allah ya taimake ni, mahaifina yana son karatu."

"Daga baya cibiyar ta kai ni makarantar kwana. Kawai suka fara cewa ai an kai ni in lalace ne kawai. A lokacin har ziyara wasu ke zuwa makarantar domin su gane wa idonsu halin da nake ciki," in ji ta.

Sai dai duk waɗannan ƙalubalen ba su hana Sakina cigaba da dagiya da ƙoƙarin ganin ta cika burinta ba.

"Har zuwa wajen kakana aka yi cewa ya yi wa mahaifina magana domin a dakatar da ni zuwa makaranta. Shi kuma ya ce babu ruwansa, a je sami mahaifina a yi masa magana."

Duk da irin ƙalubalen da Sakina take fuskanta, da irin suka, ta ce babu abin da sauya a burinta, inda ta ce a kullum ƙara samun ƙwarin gwiwa take yi domin ganin lallai ta samu nasara.

"A lokacin ina so ne in zama allon kwaikwayo a karkararmu a game ilimin boko da zamantakewa," in ji ta.

Samun nasara da zama abar koyi

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sakina ta ce ta fara ganin sakamakon jim kaɗan bayan ta kammala karatun sakandare ta koma gida.

Ta ce da ta koma gida ne sai mahaifinta ya ba ta shawarar ta fara zuwa ƙaramin asibtin ƙauyen domin taya ma'aikatan jinya aiki.

"A lokacin ne na fara ganin amfanin ilimi. Da ne je, sai aka fara ajiye ni a ɓangaren bayar da kati. Sai ya zama idan mutane sai suka ga Sakina. Sai labarin ya fara karaɗe ƙauyen, ana cewa an fa ga Sakina a asibiti."

Ta ce daga bisani aka mayar da ita ɓangaren bayar da magani, inda ake zuwa da maganin da aka rubuta, sai ta miƙa.

"A cikin ƙanƙanin lokaci kawai sai na zama abar kwatance. Daga wadda ake kwatance ana zagi, na zama wadda ake kwatance ana alfahari."

Sai dai duk da burinta na zama likita ko ma'aikaciyar jinya bai cika ba, sai ta koma karatu a kwalejin horar da malamai wato NCE.

"Ni na fara karatu har matakin NCE a ƙauyenmu," in ji Sakina cikin alfahari. "Da a ce na yarda da yanayin da na tsinci kaina a ciki, da ban kai inda nake a yau ba. Ina son sauran ƴan mata su fahimci cewa ilimi na iya canza rayuwa."

Yau, Sakina ba ta tsaya a mace mai ilimi ba kawai, ta zama abar koyi ga ƴan mata da dama a ƙauyenta.

"Bayan yara matan ma, yanzu a sanadiyar ilimin da na yi, iyaye mata da dama a ƙauyenmu yanzu suna sha'awar yaransu su samu ilimin boko mai zurfi domin su yi alfahari da su."

Rayuwa tsakanin gona da gida

A wani labarin daban, Hafiza da Khadija ne suka dage domin cika burinsu na samun ilimi mai zurfi duk da yanayin da suka tsinci kansu a ciki na tasowa a karkara da kuma ayyukan da suka taso suka ga mata na yi.

a ƙauyensu, a duk safiya, a daidai lokacin da yara a wasu garuruwa ke shirye-shiryen tafiya makaranta, ita Hafiza Surajo tunaninta kawai shi ne yadda za ta je gona taya iyayenta ko ƴan'uwanta maza aiki.

A wasu lokuta tana ɗebo ruwa, wani lokaci tana farawa da zuwa gona ne, sannan ta koma gida domin gudanar da ayyukan gida. Wasu ranakun kuma tana haɗa ayyukan ne da zuwa Islamiyya.

Hafiza ta bayyana cewa tun tana ƙarama rayuwarta ta kasance tsakanin gida da gona.

Ita ma Khadija Ibrahim, wata yarinya daga karkara a yankin Zaria da ke jihar Kaduna, ta bayyana irin rayuwar da ta taso a cikinta.

"A rayuwata ta baya muna zuwa gona, muna tsinkar wake, muna girbin masara da barkono," in ji ta, sannan ta bayyana cewa daga cikin abubuwan da suka fi tayar mata da hankali akwai tafi mai tsawon gaske domin ɗebo rua a duk safiya.

Ta ce duk da waɗannan aikace-aikacen da ke gabansu, suna zuwa makarantar allo domin karatun addini.

Duk da haka, rayuwar Hafiza da Khadija ta fara sauyawa ne bayan sun samu shiga wani shirin tallafawa ilimin yara mata.

Dukkaninsu sun samu shiga cibiyar tallafawa ilimin ƴaƴa mata ta Center for Girls Education, inda aka musu wani horo na musamman da ake kira "Safe Space", inda suka kwashe wata goma ana wayar da kansu kan muhimmancin ilimi da sauran su.

Bayan kammala shirin, an taimaka musu wajen shiga makarantar boko.

A cewar Khadija, shirin ya sauya yadda take kallon rayuwa. "Da aka ɗauke mu zuwa cibiyar, aka saka mu makarantar boko. Tun daga lokacin na fara fahimtar cewa ilimi na iya canza rayuwata."

Hafiza da Khadina sun ce har yanzu suna taimakawa iyayensu, amma yanzu sun koyi tsara lokaci. "Yanzu mun fi ba karatu muhimmanci saboda shi ne zai taimaka mana a rayuwa."

Burinsu na rayuwa

Yayin da suke ci gaba da karatu, kowacce daga cikinsu na ɗauke da babban buri a rayuwarsu.

Ga Khadija, burinta shi ne zama lauya. "Ina son in zama lauya domin in taimaka wa mutane kuma in kare haƙƙinsu."

Ita kuwa Hafiza tana da burin zama malamar makaranta. "Ina son in zama malamar makaranta domin in koyar da mutane ilimi da taimaka wa yara kamar yadda aka taimaka min."

Duk da bambancin burikansu, abu ɗaya ne ya hada su: amannar cewa ilimi zai iya sauya rayuwarsu.

Abu 5 da ke hana matan karkara zuwa makaranta

A cewar Daraktar Centre for Girls Education, Habiba Muhammad, duk da ci gaban da ake samu, har yanzu akwai manyan ƙalubale da ke hana yara mata musamman na karkara samun ilimi.

Ta bayyana manyan matsaloli guda biyar da ke hana yara mata zuwa makaranta:

1. Matsalolin al'ada da ra'ayoyin jama'a

A cewarta, wasu iyaye har yanzu na ganin ilimin boko bai da wani amfani ga mace.

"Wasu na tunanin cewa mace ba ta buƙatar ilimi sosai saboda daga ƙarshe za ta yi aure ne."

2. Nisan makarantu

A wasu ƙauyuka, yara mata kan yi tafiya mai nisa kafin su isa makaranta.

Wannan nisan na sa iyaye da dama tsoron tura ƴaƴansu, musamman idan hanyar ba ta da jama'a.

3. Matsalolin tsaro

Habiba ta ce rashin tsaro na daga cikin manyan abubuwan da ke hana yara mata zuwa makaranta.

"Idan hanyar makaranta ba ta da tsaro, iyaye kan fi son yarinya ta zauna a gida."

4. Rashin Ingantaccen Ilimi

Ta ce a wasu yankuna akwai makarantu amma ba a samun ingantaccen koyo saboda ƙarancin malamai da kayan koyarwa.

"Sau da yawa za ka ga yarinya ta yi shekaru a makaranta amma ba ta iya karatu da rubutu yadda ya kamata."

5. Talauci da Kudaden Makaranta

A cewarta, talauci na ci gaba da zama babban ƙalubale. "Wani lokaci ko karamin kudi ne kamar kudin tsintsiya zai hana yarinya zuwa makaranta."

Hanyoyin rage matsalar

Habiba Muhammad ta yi imanin cewa magance waɗannan matsaloli ba aikin gwamnati kadai ba ne, har da al'umma baki ɗaya.

Ta ce malamai, limamai da shugabannin al'umma su ƙara wayar da kan iyaye kan muhimmancin ilimin yara mata. "Ko a addini ilimi farilla ne. Idan muka ci gaba da fadakar da jama'a za a samu sauyi."

Ta ƙara da cewa samar da tsaro na da muhimmanci, domin a cewarta, gwamnati ta tabbatar da tsaron makarantu da hanyoyin zuwa makaranta.

A wuraren da babu makarantu, ta ce ya zama dole gwamnati ta samar da su domin rage nisan tafiya.

Habiba ta ce inganta ilimi ba zai yiwu ba sai an ba malamai ƙarin horo da walwala, domin "Malamai suna buƙatar horaswa, ingantaccen albashi da kyawawan yanayin aiki."

Ta kuma yi kira da a cire duk wasu kuɗaɗe da ke hana yara mata samun damar shiga makaranta.