Me ya sa kotu ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa shugaban 'hukumar bogi' a Najeriya?

Prince Adeniyi Adeyemi
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhume-tuhume aikata manyan laifuka takwas da gwamnatin tarayya ta shigar kan Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargin ya yi iƙirarin zama Darakta-Janar na wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).

Mai shari'a Mohammed Umar ne ya soke shari'ar bayan gwamnatin tarayya ta nemi hakan.

Gwamnatin Najeriyar ta ce za ta sake shigar da karar a Babbar Kotun Birnin Tarayya, domin a sake fara shari'ar tun daga farko.

Antoni-Janar Rotimi Oyedepo, SAN, ne ya sanar da mai shari'ar cewa an riga an shigar da sabuwar kara a Babbar Kotun FCT.

A ranar Litinin, Oyedepo ya gabatar da bukatar a soke tuhume-tuhumen da ake yi wa Adeyemi.

Ya shaida wa kotun cewa Antoni-Janar kuma Ministan Shari'a sun sake duba takardun shari'ar Adeyemi, inda suka gano cewa akwai matsaloli a tuhumar da Sufeto-Janar na ƴansanda ya shigar.

Ya kara da cewa, laifin yin jabun takardun da ake zargin Adeyemi ya aikata yana cikin ikon babbar kotun birnin tarayya ta yi shari'a a kai, ba babbar kotun tarayya ba.

Daraktan Masu Gabatar da Kara na Tarayya (DPPF) ya shaida wa kotun cewa sun riga sun shigar da sabbin tuhume-tuhume a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya, kuma za su gurfanar da Adeyemi domin a sake fara shari'ar daga farko nan ba da jimawa ba.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu, SAN, bai ƙalubalanci bukatar gwamnatin ba.

Bambancin kotunan biyu ya ta'allaka ne da dokokin da suke gudanar da aikinsu, da kuma kasancewar daya kotun tarayya ce, yayin da dayan kuma kotun babban birnin tarayya ce.

Ana tuhumar Adeyemi da wasu mutum biyu da ba a bayyana sunayensu ba, kan zargin hada baki da yin jabun takardu.

Gwamnatin Najeriya ce ta fara bayyana cewa hukumar PFIPC/PEAC, wadda Adeyemi ke ikirarin zama darakta-janar, ba halastacciyar hukumar gwamnati ba ce.

Fadar shugaban kasa ta ce hukumar ba ta cikin hukumomin gwamnatin tarayya da doka ta amince da su, duk da cewa tana aiki daga Sakatariyar Tarayya, tana da asusun banki na hukuma, sannan akwai takardun da ke nuna cewa ta samu amincewa daga shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Adeyemi ya musanta zarge-zargen, inda ya dage cewa ba ta hanyar yaudara ya samu mukaminsa ba. Ya yi ikirarin cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya taimaka aka nada shi, kuma ya sanya hannu a takardar nadin nasa.

Sai dai Gbajabiamila ya musanta wannan ikirari, kuma ya shigar da karar Adeyemi a kotu bisa zargin bata masa suna.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Rundunar 'yan sanda ta ce bincikenta ya nuna cewa Adeyemi ne kaɗai ke gudanar da ayyukan hukumar PFIPC, kuma shi da kansa ya riƙa bayyana cewa shi ne darakta-janar ɗinta.

Daga bisani, 'yan sanda suka gurfanar da Adeyemi a gaban Mai shari'a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Alƙalin ya ba da umarnin a kama shi bayan ya ƙi halartar zaman kotun.

A watan Yuli, Majalisar Wakilai ta kafa wani kwamiti domin bincikar yadda hukumar PFIPC ta samu shiga cikin kasafin kuɗi har da naira biliyan 1.302 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, duk da cewa babu wata doka da ta kafa hukumar.

A wani zaman sauraron bayanan binciken, shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Didi Esther Walson-Jack, ta amince cewa ofishinta ne ya bayar da amincewar ɗaukar ma'aikata na hukumar PEAC/PFIPC.

Walson-Jack ta amince cewa ofishinta bai gudanar da cikakken bincike kan hukumar ba kafin bayar da muhimman amincewar da suka ba ta damar gudanar da ayyukanta.

"Ofishina ya karɓi takardar naɗin da kuma dokar kafa hukumar. Bisa waɗannan takardu, da kuma tattaunawar da muka yi da wakilan PEAC/PFIPC, sai muka bayar da takardar amincewa da kafa hukumar, daga bisani kuma muka bayar da izinin ɗaukar ma'aikata," in ji ta.

"Yanzu da muka ga dukkan bayanai da kuma nazarin takardun, mun amince cewa ya kamata mu ƙara zurfafa bincike wajen gudanar da ayyukan ofishinmu, musamman kafin bayar da amincewar kafa hukumar da kuma izinin ɗaukar ma'aikata na PEAC/PFIPC," in ji Walson-Jack.

Haka kuma, wani darakta a ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Joshua Luka, ya shaida wa kwamitin Majalisar Wakilai cewa ɗaya daga cikin ƙananan ma'aikatan ofishinsa ne ya yi sakaci da aikinsa, ta hanyar barin Adeyemi ya karɓi wata takarda da ya kamata a aika wa ofishin Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa.

Abin da Adeyemi ya ce

Sai dai Adeyemi, wanda shi ma ya kamata ya halarci zaman sauraron bayanan domin ya bayyana nasa ɓangaren, bai halarta ba. Sufeto-Janar na 'Yan Sanda ya ce tuni ana shari'ar batun a kotu, kuma suna buƙatar umarnin kotu kafin su iya gabatar da wanda ake zargin a gaban kwamitin.

A ƙarshe, kwamitin Majalisar Wakilai ƙarƙashin jagorancin Yusuf Gagdi, ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Kanke/Kanam/Pankshin a jihar Filato, ya bayyana cewa Adeyemi ne ya tsara zamba ta hukumar, sannan ya ba da shawarar a gurfanar da shi a gaban kotu.

Da yake mayar da martani, lauyan Adeyemi, Festus Akhigbe, ya ce an tauye wa wanda yake karewa haƙƙinsa na sauraron adalci, saboda ana son mayar da shi saniyar ware.

Akhigbe ya kuma zargi wasu hukumomin gwamnati da hannu a badakalar, ciki har da Babban Bankin Najeriya (CBN), Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Tu'annati (EFCC), ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, da kuma ofishin Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya. Ya ce bai kamata a ɗora wa Adeyemi laifi shi kaɗai ba, alhali akwai wasu hukumomin da ake zargin sun taka rawa a lamarin.