Fitattun mata 5 da ke takarar gwamna a Najeriya a 2027

Wasu daga cikin mata ƴantakara
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta fitar da jerin sunayen ƴantakarar gwamna a zaɓen 2027, wasu sun fara kokawa kan rashin ganin sunayen mata da yawan cikin jerin.

Batun ƙarancin wakilcin mata a siyasar Najeriya ya kasance abin tattaunawa tsawon lokaci, inda masu rajin kare haƙƙin mata ke kiran a ba su damar shiga harkokin mulki da siyasa yadda ya kamata.

A cewarsu, samun ƙarin mata a manyan muƙaman siyasa zai taimaka wajen samar da daidaito da kuma faɗaɗa wakilcin al'umma.

Yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen 2027, wasu fitattun mata suna ƙara bayyana a matsayin masu neman kujerar gwamna a jihohinsu.

Wasu daga cikinsu sun daɗe suna siyasa, yayin da wasu kuma suka yi suna ne ta hanyar gudanar da mulki ko kuma ayyukan gwamnati.

Masu nazarin siyasa na ganin cewa wasu daga cikin matan za su iya taka muhimmiyar rawa a fafatawar da ke tafe, musamman idan aka yi la'akari da gogewa da tasirin da suke da shi a jihohinsu.

A wannan muƙala za mu duba wasu fitattun mata biyar da ke takarar gwamnan a zaɓen da ke tafe.

Aishatu Binani - Adamawa

Aisha Binani fitacciyar ƴar siyasa ce daga Adamawa wadda ta taɓa zama Sanata mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya kuma 'yar Majalisar dattawa da ta wakilai.

Ba wannan ne karon farko da take tsayawa takarar gwamna a Adamawa ba.

A zaɓen 2023 da ya gabata, ta nuna kanta tsanakin ƴansiyasar jihar, inda ta zo ta biyu bayan zaɓen gwamnan jihar da ya ɗauki zafi ta yadda har sai da ya kai zagaye na biyu.

A wancan lokaci Binani ta zo ta biyu, bayan da ta samu ƙuri'a 390,275, yayin da gwamna Fintiri ya samu ƙuri'a 421,524 a zaɓen.

Ana kallon Binani a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƴan takarar da ke da damar yin tasiri a zaɓen 2027 da ke tafe.

Jimmy Stella Monday - Akwa Ibom

Jimmy Stella Monday na daga cikin matan da suka samu tikitin takarar gwamna a jihar Akwa Ibom da ke yankin kudu maso kudancin Najeriya.

Tana takarar ne a ƙarƙashin jam'iyyar APGA, wadda ke cikin jam'iyyun hamayya a jihar.

Ms Stella mai shekara 41 na son zama mace ta farko da za ta mulki jihar, ƙarƙashin tsarin zaɓe.

Joelyn Hogan-Bassey - Cross River

Joelyn Ita Hogan-Bassey ƴar siyasa ce daga Cross River wadda ta daɗe tana fafutika a jam'iyyar ADP.

Ta taɓa neman wasu muƙaman siyasa a baya, ciki har da kujerar majalisar dokokin jihar.

Duk da cewa tana da gogewa a siyasa, ƙarancin tasirin ADP a jihar na iya zama ƙalubale ga takararta

Esther James - Delta

Esther James ita ce ƴar takarar gwamnan Delta ta jam'iyyar Labour Party.

Kasancewarta a jam'iyyar LP na ba ta damar cin gajiyar magoya bayan jam'iyyar a jihar.

Duk da haka, tana fuskantar gasa daga manyan jam'iyyu masu ƙarfi.

Nwodom Lucy Chinwe - Ebonyi

Lucy Chinwe Nwodom ƴar takarar gwamna ce ƙarƙashin jam'iyyar APGA a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Tana cikin mata ƙalilan da suka samu tikitin takarar gwamna a zaɓen 2027.

Duk da cewa APGA na da tarihi a yankin Kudu maso Gabas, tana fuskantar ƙalubale daga APC da PDP waɗanda suka fi ƙarfi a jihar.