Kane ya ƙara nuna cancantar lashe kyautar Ballon d'Or 2026

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ko da yake Harry Kane ya saba da yin abubuwan ban mamaki, wannan karon ya zarce yadda aka saba gani daga gare shi.

Ba a kai minti 25 da fara wasa ba a fafatawar da Bayern Munich ta tashi 2-2 da Arsenal a Gasar Zakarun Turai ta Champions League, lokacin da ɗan wasan gaba ya ɗauki al'amura a hannunsa domin ƙoƙarin karya lagon kungiyar Landan mai buga Premier League.

Yayin da Arsenal ke shirin kare bugun falan daya daga Bayern, Kane ya ɗauki kwallon ya buga tun daga yadi na 80 da karfi.

Wani kwazo ne na musamman daga kyaftin din tawagar Ingila, wanda ya kusa ya zura kwalon a ragar Arsenal.

"A ƙarƙashin Vincent Kompany, an ba shi wani matsayi da amana da wataƙila bai taɓa samu a ƙarƙashin wani koci ba a can baya," in ji tsohon mai tsaron baya na Manchester City, Nedum Onuoha a hirar da ya yi da BBC Sport.

"Duk da abubuwan da muka ga yana yi da kuma wuraren da muka ga yana kai-komo a cikin filin wasa, babu wanda ya taɓa ganin ya yi bugun falan daya.

"Amma har idan Manuel Neuer, wanda ya fi shi dadewa a kungiyar da zama ginshiki a Bayern, zai ga Harry Kane ya ajiye ƙwallo zai buga bai hana shi ba, kenan yana ganin dan kwallon ya san abin da yake zai kuma yi abin da ya dace.

"A lokaci guda kuma, 'yan wasan Bayern sun yi gudu zuwa gaba saboda sun san ƙwallon za ta iya zuwa wajen da suke.

"Ya kasance yana bugan falan daya akai-akai, wanda ba lallai ba ne ka so ɗan wasanka mai buga lamba tara ya kasance a wannan matakin ba, amma salon wasansa a lokacin da yake taka leda a Bayern Munich shi ne yawan kai-komo, kuma a yau hakan ya amfani ƙungiyar sosai."

Ko da yake Kane bai samu damar bayar da kwallo an zura a raga ba da zai kara tarihi a kundinsa mai cike da tarin nasarori, sai kawai wata dama ta samu da zai yi hakan a cikin ruwan sanyi.

Bayan da Eberechi Eze ya fara ci wa Arsenal kwallo, sai Kane ya doka wata kwallon da ta wuce Jurrien Timber kafin Alphonso Davies ya zura ta a raga karawar ta koma 1-1.

Daga nan kyaftin ɗin Ingila ya bai wa masu masaukin baƙi jagoranci a bugun fenariti a zagaye na biyu, inda ya kai adadin ƙwallayen da ya ci Arsenal zuwa 16 tun daga lokacin da yake Tottenham da kuma yanzu a Bayern Munich.

Sai dai kuma Arsenal ta farke ta biyun daf a tashi ta hannun Declan Rice da aka tashi 2-2.

'Idan kana fuskantar shi, za ka gane yake da wahalar tunkara'

Wannan shi ne wani abin birgewa daga Kane, wanda ya ƙara tabbatar da cancantarsa a matsayin wanda ke kan gaba wajen takarar lashe kyautar Ballon d'Or na 2026.

Tsohon kyaftin din Tottenham Hotspur mai shekara 33 na iya zama dan Ingila na farko tun bayan Michael Owen a 2001 da zai lashe wannan babbar kyautar, inda Lamine Yamal na Barcelona da kuma ɗan wasan Paris St-Germain, kuma mai rike da kyautar a halin yanzu, Ousmane Dembele, suke cikin waɗanda ake ganin za su iya lashe babbar kyautar a fanni taka leda a duniya.

An sanya sunan Kane cikin jerin 'yan wasa 30 da aka fitar a watan Satumba, inda za a sanar da wanda zai yi nasara a ranar Litinin, bayan kada ƙuri'a da kwamitin alƙalai da na 'yan jarida 100 daga ƙasashe daban-daban za su yi.

"Shi ne wanda ake hasashen ya kamata ya lashe kyautar bana ba tare da wata gardama ba. Alƙaluman da ya tara a bana, sun isa ya zama gwarzon bana.

Shekarar da ya yi ta kasance ta musamman," in ji ɗan wasan Arsenal da Ingila Declan Rice a hirar da ya yi da TNT Sports.

"Idan kana wasa tare da shi, za ka fahimci irin ƙwarewarsa, kuma idan kana fuskantarsa a matakin abokan hamayya, za ka ga irin yadda yake wahalar da yan baya.

"Yana da abin ban mamaki, ƙwararren ɗan wasa ne sosai, kuma na yi sa'a ina wasa tare da shi, amma ba ni da sa'ar da zan yi irin abinda yake yi."

Da ya zura ƙwallo a ragar Arsenal a daren Laraba, Kane ya zama ɗan wasa na biyu a tarihin Gasar Zakarun Turai da ya ci ƙwallo a wasa 10 a jere a gasar.

Wanda yake da wannan tarihin shi ne Cristiano Ronaldo, wanda ya lashe Ballon d'Or sau biyar, inda ya ci ƙwallo a wasa 11 a jere a Champions League, yayin da yake taka leda a Real Madrid tsakanin Yunin 2017 zuwa Afrilun 2018.

"Lallai Kane ya dace sosai da Bayern Munich. Ya fahimci ƙungiyar da tsarin wasanta, kuma su ma sun fahimce shi. Sun san cewa idan ƙwallo ta zo ƙafafunsa, ko a ina ne, wani abu mai kyau na iya faruwa," in ji Onuoha.

"Ina ganin dukkan 'yan wasan Bayern Munich suna taka rawa sosai a fafatawa da Arsenal, sai kuma Harry ya zo ya ci bugun fanareti.

''Yancin da yake da shi ne mafi kyau ta hanyar bayyana yanayin da yake ciki a Bayern Munich, domin yana aiki tuƙuru wajen kare gida, wanda ke ba shi damar nuna kwazonsa idan yana kai hari. A halin yanzu dai yana taka rawar gani cikin nasara."

Ƙwallon da Kane ya ci Arsenal a Champions League ranar Laraba ta kai jimillar 156 a wasa 158 tun bayan da ya koma Bayern Munich daga Tottenham a 2023.

Rana ce mai kyau a tare da shi na ci gaba da yin bajinta, yayin da bikin bayar da kyautar Ballon d'Or da za a yi a Landan a wannan watan ke ƙaratowa.

Saboda haka Kane zai yi farin ciki sosai idan ya lashe kyautar, ganin yadda za a gudanar a Landan, kuma zai zama na biyu da zai daga Ballon d'Or a tarihi, bayan Owen.