Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za ku fara kasuwanci da ƙaramin jari har ya bunƙasa
A Najeriya da ke fama da hauhawar farashin kayayyaki, ƙarancin kuɗi da kuma tsadar yanayin gudanar da sana'a ko kuma kasuwanci, farawa da ƙaramin jari na iya zama babban ƙalubale.
Sai dai rashin babban jari ba yana nufin mutum ba zai iya kafa sana'ar da za ta riƙa samar masa da riba ba.
Masana na ganin abin da ya fi muhimmanci shi ne sanin irin kasuwancin da ya dace da jari da yanayin da ake ciki, yin amfani da kuɗi cikin tsari, da kuma guje wa kashe ribar da aka samu kafin kasuwancin ya samu ƙarfi.
Ƙananan riba da ake samu a kai a kai na iya zama babban jari idan aka riƙa mayar da wani ɓangare daga cikinta cikin kasuwancin.
To, ta yaya mutum zai fara kasuwanci da ƙaramin jari, ya kare abin da ya saka, sannan ya riƙa bunƙasa shi har ya zama babbar sana'a?
Wannan ne ya sa BBC ta zanta da Dr Ismail Muhammad Anchau, masanin harkokin kasuwanci kuma malami a kwalejin kimiyya da fasahar ta Kaduna, kuma ga wasu matakai da ya a bi domin gai wa ga gaci.
Shawarwarin masani
- Ilimi
Dr Ismail Muhammad Anchau ya ce abu na farko da mutum yake buƙata kafin fara kasuwanci shi ne ya fahimci irin kasuwancin da yake son shiga.
A cewarsa, ya kamata mutum ya nemi ilimi da ƙwarewa game da kasuwancin kafin ya saka jari, domin duk wata sana'a tana buƙatar a koye ta.
"Ana iya samun wannan ilimi ta hanyar karatu a makaranta ko kuma koyon sana'ar a ƙarƙashin wani ƙwararre da ya riga ya fahimci harkar."
Ya ce fahimtar kasuwancin da kyau na taimaka wa mutum wajen sanin yadda ake gudanar da shi, da matsalolin da ka iya tasowa, da kuma hanyoyin da za a bi wajen samun riba.
- Inganci
Ya kuma jaddada muhimmancin ingancin abin da mutum yake sayarwa.
Ya ce duk abin da mutum zai sayar ya kasance mai kyau kuma abin da al'umma ke buƙata, domin idan kwastomomi suka samu ƙima daga abin da suka saya, za su dawo kuma su ba da shawarar su zu su saya.
"Duk abin da za ka sayar ya zama mai kyau ne, wanda al'umma ke so. Kuma ya kasance mutane suna samun abin da suke so daga kayanka, sai mutane su riƙa dawowa," in ji shi.
- Ci gaba da neman ilimi
Dr Anchau ya ce bai kamata ɗan kasuwa ya daina koyo ba bayan ya fara sana'a. Ya kamata ya riƙa amfani da damar samun horo ko training a duk lokacin da ya samu.
A cewarsa, ƙarin ilimi da horo na taimaka wa ɗan kasuwa wajen samun ƙwarewar gudanar da kasuwanci, musamman yadda ake sarrafa kuɗi da kuma juya jari cikin hikima.
- Adana bayanan kasuwanci
Ya kuma bayyana muhimmancin yin kididdigar kasuwanci, wato adana bayanan kuɗin da ke shiga da wanda ke fita.
Ya ce ɗan kasuwa ya kamata ya san nawa ya sayi kaya, nawa ya sayar da su, da kuma irin ribar da ya samu. Wannan zai taimaka masa wajen sanin ainihin halin da kasuwancinsa yake ciki da kuma gano inda yake samun riba ko asara.
- Samun jari
A cewarsa, jari ma wani muhimmin abu ne, amma adadin jarin da mutum yake buƙata ya danganta da girman da irin kasuwancin da yake son gudanarwa.
Ya ce mutum ya kamata ya fahimci irin jarin da kasuwancin yake buƙata kafin ya fara, domin ƙarancin jari na iya kawo cikas ga gudanar da sana'a.
- Yanayin tattalin arzikin kasa
Wani abu da Dr Anchau ya ce ya kamata 'yan kasuwa su lura da shi, shi ne yanayin tattalin arzikin ƙasar, musamman a lokacin da ake fuskantar hauhawar farashin kayayyaki.
A irin wannan yanayi, ya ce ɗan kasuwa zai iya neman hanyoyin da zai samu kaya a farashi mai rahusa, domin rage tsadar da ake fuskanta da kuma ci gaba da samun riba.
- Fahimtar manufofin gwamnati
Ya ce fahimtar manufofin gwamnati ma na da matuƙar muhimmanci ga 'yan kasuwa.
A cewarsa, idan wasu manufofin gwamnati suna ƙara tsananta wa harkokin kasuwanci, ya kamata 'yan kasuwa su haɗa kai su nemi gwamnati ta duba irin waɗannan manufofi domin samun sauƙin gudanar da sana'o'insu.
Ya bayar da misalin batun tsaro, inda ya ce rashin tsaro na iya hana 'yan kasuwa safarar kayayyaki daga wata jiha zuwa wata.
"Misali, idan tsaro ya kasance mai kyau, 'yan kasuwa za su iya kwasan kayansu daga Zamfara su kai Benue," in ji shi.
Shawara ga masu shirin yin ritaya
Wani muhimmin batu da Dr Anchau ya ja hankalin ma'aikata a kai shi ne batun shiga harkar kasuwanci ko noma bayan ritaya.
Ya ce ba hikima ba ce mutum ya jira har sai ya yi ritaya sannan ya kwashi dukkan kuɗin da ya tara ya jefa su cikin kasuwanci ko noma ba tare da ya taɓa samun ƙwarewa a harkar ba.
"Kamar yadda na fada ne a baya, ba a fara kasuwanci daga sama. Kuskure ne babba mutum ya kwashi kuɗinsa kawai ya fada kasuwanci ko noma ba tare da ya koya ba," in ji shi.
Ya shawarci ma'aikata da su fara tun da wuri, misali suna da sauran kimanin shekaru 10 ko sama da haka kafin su yi ritaya, su fara koyon kasuwancin da suke sha'awa sannan su fara gwada shi a hankali.
A cewarsa, mutum zai iya fara kasuwancin da ƙaramin jari yayin da yake aiki, ya koyi yadda ake gudanar da shi, ya fahimci matsalolinsa, sannan ya riƙa faɗaɗa shi a hankali.
Wannan zai ba shi damar samun ƙwarewa da fahimtar harkar tun kafin ya yi ritaya, maimakon ya jira lokacin ritaya sannan ya fara daga farko.