Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassa na duniya 06/07/2026

Wannan shafin ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassa na duniya na ranar Litinin 6 ga watan Yulin, 2026

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida

  1. Pezeshkian, Qalibaf da babban ɗan Ali Khamenei za su halarci jana’izarsa a Iraq

    Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa za a kai gawar marigayi Ali Khamenei zuwa birnin Najaf gobe, Talata bayan an gudanar da jana’izarsa a birnin Qom.

    Rahoton ya ce Mustafa Khamenei, wanda shi ne babban ɗansa tare da shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian da kuma kakakin majalisar dokokin ƙasar Mohammad Baqer Qalibaf, za su tafi Najaf a gobe domin halartar jana’izar da za a gudanar a Iraq.

    An shirya gudanar da jana’izar Ali Khamenei a ranar Laraba a biranen Karbala da Najaf na ƙasar Iraq.

    Bayan haka, za a binne Khamenei ta Iran a ranar Alhamis a harabar hubbaren Imam Reza da ke birnin Mashhad.

  2. Cutar Ebola ta kashe mutum fiye da 500 a Gabashin DR Congo

    Mahukuntan lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DR Congo) sun sanar da cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon ɓullar cutar Ebola nau'in Bundibugyo ya kai 506.

    Tun bayan ayyana ɓarkewar cutar a ranar 15 ga Mayun 2026, an tabbatar da kamuwar mutum 1,561, yayin da mutum 628 ke killace ko kwance a asibiti a larduna uku na gabashin ƙasar.

    Lardin Ituri ne har yanzu ke kan gaba wajen yawan waɗanda suka kamu da cutar, inda yake da fiye da kashi 90 cikin 100 na dukkanin waɗanda aka tabbatar sun kamu.

    Haka kuma jami'an lafiya sun nuna damuwa kan yawaitar zirga-zirgar jama'a a yankunan da ke cikin haɗari, musamman sakamakon rikice-rikice da ayyukan haƙar ma'adinai.

    Barkewar cutar ta kuma shafi ma'aikatan lafiya, inda mutum 96 daga cikinsu suka kamu da cutar, yayin da 19 suka mutu. Duk da ƙarancin kayan kariya da matsalolin da ake fuskanta, jami'an lafiya sun ce ana samun ci gaba wajen bibiyar mutanen da suka yi hulɗa da masu ɗauke da cutar, kuma adadin waɗanda suka warke ya kai 254.

  3. Hatsarin mota a Ogun ya yi sanadin mutuwar mutum 10

    Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu shida suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a gadar Saapade da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.

    Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Afolabi Odunsin, ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata babbar mota da kuma wata motar bas.

    Ya ce mutum 18 ne ke cikin motocin biyu a lokacin da hatsarin ya faru.

    A cewarsa, mutum 10 sun mutu nan take, ciki har da maza tara da yaro ɗaya, yayin da mutum shida suka samu raunuka daban-daban.

    Binciken farko ya nuna cewa saurin da ya wuce kima da kuma tuƙin ganganci ne suka haddasa hatsarin.

    Ma'aikatan ceto na FRSC sun garzaya wurin da hatsarin ya faru inda suka kai waɗanda suka ji rauni Asibitin Victory da ke Ogere domin samun kulawa, yayin da aka kai gawarwakin mamatan ɗakin ajiye gawa na FOS da ke Ipara.

    Kwamandan FRSC na jihar Ogun, Oludare Ogunjobi, ya jajanta wa iyalan mamatan tare da gargadin direbobi musamman na motocin haya da manyan motoci da su guji yin tuƙin ganganci da gudun da wuce kima da sauran laifukan tuki da ke jefa rayuka cikin haɗari.

  4. Tsohon shugaban Iran Ahmadinejad ya halarci jana'izar Ali Khamenei a Tehran

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun wallafa hotunan da ke nuna tsohon shugaban ƙasar, Mahmoud Ahmadinejad, yana cikin mahalarta jana'izar tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, da ake gudanarwa a birnin Tehran.

    Bayyanar Ahmadinejad a wajen jana'izar ta janyo hankali, kasancewar ba a gan shi a bainar jama'a ba tun bayan fara yaƙin Iran.

    A lokacin yaƙin, rahotanni sun ce yankin da gidansa yake ya fuskanci hare-hare.

    Ahmadinejad ya shugabanci Iran daga shekarar 2005 zuwa 2013, kuma ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2009 mai cike da cece-kuce.

    Bayan zaɓen ne aka tsare manyan jagororin adawa, ciki har da Mir Hossein Mousavi, Zahra Rahnavard da Mehdi Karroubi, lamarin da ya haifar da zanga-zangar Green Movement a fadin ƙasar.

  5. Yadda ake zagaya wa da gawar Khamenei a tsakiyar miliyoyin mutane a Tehran

    Hotunan da kafafen yaɗa labarai suka wallafa sun nuna ɗimbin jama'a da suka mamaye tituna da manyan filayen taro a birnin Tehran domin yi wa tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, bankwana na ƙarshe.

    Maza da mata sanye da baƙaƙen kaya sun hallara tun daga safiyar ranar jana'izar, inda wasu ke ɗauke da hotunansa da tutocin Iran.

    A wasu daga cikin hotunan, ana iya ganin yadda gawar Khamenei ke tafiya a cikin wata mota ta musamman yayin da dubban masu makoki ke rakiyar ta a kan titunan birnin.

    Mahalarta taron sun nuna alhini da jimami, inda wasu ke yin addu'o'i tare da bayyana girmamawarsu ga mutumin da ya shafe shekaru yana jagorantar ƙasar.

    Jana'izar ta zama ɗaya daga cikin manyan tarukan da aka gani a Iran cikin 'yan shekarun nan, lamarin da ya sa hukumomi suka ɗauki matakan tsaro da na zirga-zirga na musamman.

    Ana sa ran bukukuwan za su ci gaba kafin daga bisani a kai gawar marigayin zuwa birnin Mashhad, inda za a yi masa jana'iza ta ƙarshe da kuma binne shi.

  6. Ana ci gaba da gudanar da jana'izar Ali Khamenei a Tehran

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da jana'izar tsohon jagoran addinin ƙasar, Ali Khamenei, a babban birnin ƙasar, Tehran.

    Rahotannin sun nuna cewa miliyoyin mutane ne suka fito domin halartar taron jana'izar, yayin da aka wallafa hotuna da ke nuna dimbin mahalarta taron.

    Masu shirya jana'izar sun ce za a yi tattaki da gawar ta amfani da wata mota ta musamman da aka tanada domin ɗaukar gawar marigayin, kuma ana sa ran tattakin zai ɗauki tsakanin sa'o'i 10 zuwa 12.

    Saboda yawan mahalarta da kuma buƙatar tabbatar da tsaro, hukumomin Iran sun sanar da sabbin matakan zirga-zirga a biranen Tehran da Qom, inda aka yi gyare-gyare na musamman domin sauƙaƙa gudanar da bukukuwan jana'izar.

    A ranar Lahadi, sabon jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei, bai halarci sallar jana'izar mahaifinsa ba. Sai dai daga baya an fitar da wata sanarwa da aka danganta da shi, wadda ta sake tabbatar da naɗin Gholamhossein Mohseni Ejei a matsayin shugaban ɓangaren shari'ar ƙasar.

    Ana sa ran bukukuwan jana'izar za su ci gaba cikin kwanaki masu zuwa, kafin daga bisani a kai gawar Ali Khamenei zuwa birnin Mashhad domin yi masa jana'iza ta ƙarshe da kuma binne shi.

  7. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da wannan safiya ta ranar Asabar.

    A yau zamu kawo muku labarai da hotunan ci gaban tarukan jana'izar jagoran addinin Iran, da sauran labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.