Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Litinin 18/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Kotu ta umarci a biya Shakira kusan dala miliyan 70

    Babbar Kotu a Sifaniya ta umarci hukumomin haraji na ƙasar da su biya fitacciyar mawaƙiyar nan Shakira, kusan dala miliyan 70 sakamakon shari'ar da aka shafe shekara takwas ana yi.

    Ta yi maraba da hukuncin inda ta ce matakin ya fayyace komai bayan tsawon shekarun ƙunci da ta ce ta fuskanta na ƙoƙarin ɓata mata suna.

    Shakira ta sadaukar da nasararta ga ɗumbin mutanen da suka fuskanci ƙalubale makamancin haka.

    Kotun ta gano cewa an yi ta karɓar miliyoyin daloli a matsayin haraji a hannun Shakira a 2011 bisa kuskure kuma kotun ta gano cewa a lokacin doka ba ta hau kan mawaƙiyar ta biya haraji ba a matsayin mai zama a Sifaniya.

    A don haka kotun ta umarci a mayar mata da cikakken kuɗin tare da kuɗin ruwa.

  2. Najeriya na ƙara sa ido bayan ɓarkewar Ebola a Congo

    Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka a Najeriya, NCDC ta ce duk da cewa ba a samu ɓullar cutar Ebola ba a ƙasar, tana ƙarfafa matakai don sa ido sakamakon mutuwar mutum 88 a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da kuma samun mutum guda da aka bayar da rahoton ya kamu da cutar a Uganda.

    Cikin wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar, Jide Idris ya fitar a ranar Lahadi, hukumar NCDC tana shirya ayyukan wayar da kai da kuma a faɗin ƙasar.

    Matakin na zuwa ne yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ayyana ɓarkewar Ebola a Congo da Uganda a matsayin babban abin damuwa.

    Hukumomin lafiya ta ce ɓarkewar cutar tana ɗauke da babban haɗari saboda tuni aka gano ƙwayar cutar a Uganda sannan kuma an samu mutanen da suka kamu a Kinshasa da ke Congo.

    Cutar da ta fara ɓulla a Lardin Ituri na Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo ta shafi kusan mutum 246.

  3. Kotu ta ba da belin El Rufai kan naira miliyan 100

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El Rufai.

    An bayar da belinsa ne kan naira miliyan 100 da mutum guda da zai tsaya masa kan makamancin kuɗin.

    Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta bayyana tsauraran ƙa'idodin belin inda ta ce wanda zai tsaya masa dole ne ya zama mazaunin Maitama ko Asokoro da ke Abuja sannan kuma dole a miƙa wa kotu takardar shaidar mallakar wata kadara.

    Kotun ta kuma sake bayar da umarni cewa dole ne wanda zai tsaya masa ya zama ma'aikacin gwamnatin tarayya da ke mataki na 17 na ɗaukan albashi sannan kuma ya nuna shaidar albashi na aƙalla wata uku.

    Kotun ta umarci El Rufai ya miƙa duka fasfonsa na fita ƙasar waje da yake da su.

    Mai shari'a Abdulmalik ta kuma umarce shi da ya riƙa zuwa hukumar DSS kowace Juma'ar ƙarshe ta wata domin ya cike rajista har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan ƙarar.

    Kotun ta kuma gargaɗe shi kan saɓa ƙa'idojin da ta ce za su iya sa wa a soke belin da aka ba shi.

  4. Isra'ila ta halaka kwamandan Islamic Jihad da ƴarsa a Lebanon

    Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Lebanon ta ce wani harin makami mai linzami da Isra'ila ta kai kan wani gida a gabashin Lebanon ɗin ya kashe wani kwamandan ƙungiyar Islamic Jihad, da ƴarsa.

    A wani hari na daban kuma ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta ce wasu hare-haren sama na Isra'ilar a kudancin Lebanon ɗin ya kashe mutum biyar, da suka haɗa da yara biyu.

    Can a Gaza ma jami'an lafiya sun ce an kashe mutum biyar a wani hari da Isra'ila ta kai, uku daga cikin mutanen sun mutu ne a harin sama kan, wani wuri da ake dafa abincin jama'a a kusa da asibitin Al- Aqsa a tsakiyar birnin na Gaza.

    Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba dangane da hare-haren nata na baya-bayan nan walau a Lebanon ɗin ko a Gaza.

  5. An kashe malami guda cikin malaman da ƴanbindiga suka sace a Oyo

    Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, Seyi Makinda ya ce malaman makaranta bakwai aka sace sakamakon hare-haren da ƴanbindiga suka kai kan wasu makarantu uku a ƙaramar hukumar Oriire ranar Juma'a.

    Da yake magana da manema labarai ranar Lahadi, Mista Makinde ya ce an sace malamai bakwai yayin hare-haren inda ya tabbatar an kashe malami guda.

    "Mun samu wani bidiyo da safiyar nan cewa ƴan ta'addan sun kashe ɗaya daga cikin malaman," in ji shi.

    Ƴansanda da hukumomin gwamnati sun ce har yanzu suna ƙoƙarin gano ainahin adadin ɗaliban da suka ɓata.

    Kafafen yaɗa labarai sun ce aƙalla yara 45 aka sace.

    Gwamnan ya ce wasu daga cikin jami'an tsaron da suka kai ɗauki lokacin har-haren ƴanbindigar sun ji rauni.

    Mista Makinde ya ce gwamnati tana yin duk mai yiwuwa domin dawo da ɗaliban hannun iyayensu inda ya ce za su riƙa gabatar da bayanai kowace rana domin sanar da halin da ake ciki.

    Zuwa yanzu dai babau wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai hare-haren.

    Da farko an rufe makarantu a yankin da alamarin ya faru sai dai gwmanatin daga bisani ta bayar da umarnin a buɗe su sakamakon ruɓnya jami'an tsaro da aka yi.

    Najeriya dai ta fuskanci matsalar sace-sacen mutane da ƴanbindiga ke yi inda ake kai hari kan makarantu don neman kuɗin fansa. An fi samun irin hare-haren a arewacin Najeriya amma lamarin na zama abin damuwa a wasu yankunan kudu maso yammacin ƙasar.

  6. Sojojin Mali sun 'kashe farar hula 10' a harin jirgi mara matuƙi

    Rahotanni daga Mali na cewa wani harin jirgin sama maras matuƙi da dakarun gwamnati suka kai ya hallaka fararen hula aƙalla goma, yayin da suke shirin wani bikin aure a yankin San na tsakiyar ƙasar.

    Kamfanin dillancin labarai na Faransa, ya ce wata majiya ta jami'an tsaro ta ce sojin na gwamnatin Mali sun hari wani jerin gwanon babura ne.

    Wani mazaunin yankin ya ce abin da ya kamata ya zama na farin ciki ya zama na baƙin ciki da tashin hankali.

    Lamarin ya faru ne yayin da a watan da ya gabata Malin ta fuskanci gagarumar matsalar tsaro inda mayaƙan da ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda da kuma Buzaye ƴan tawaye suka kai mata wasu jerin hare-hare da suka jijjiga gwamnatin sojin ƙasar ta yammacin Afirka.

  7. Sabbin hare-haren Najeriya da Amurka sun kashe mayaƙan ISIS fiye da 20

    Najeriya da Amurka sun ce sun sake kai jerin hare-hare kan sansanonin mayaƙan ISIS da ke arewa maso gabashin Najeriyar a wani ɓangare na ayyukan fatattakar masu iƙirarin Jihadi a yankin.

    Amurka ta ce an kai hare-haren ne ranar Lahadi bisa haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.

    Sojojin Najeriya sun ce samamen na baya-bayan nan an ƙaddamar da su ba tare da wata matsala ba a yankin Metele da ke jihar Borno.

    A cewar sojojin, an kai samamen ne bayan da aka gano taruwar ƴan ta'adda a wajen inda suka ce hare-haren sun halaka fiye da mayaƙan Iswap da Isis 20.

    Hare-haren na baya-bayan nan na zuwa ne kwana ɗaya bayan wani hari na haɗin gwiwa na Najeriya da Amurka wanda ya yi sanadin mutuwar Abu Bilal al-Minuki, da ƙasashen biyu suka bayyana shi a matsayin ƙusa a ƙungiyar Isis.

    Hukumomi sun ce samamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin murƙushe mayaƙan.

    Cikin wata sanarwa da aka fitar yau Litinin, rundunar Amurka da Afirka, Africom ta ce bayanan sirri da aka tattara sun tabbatar cewa mayaƙan Isis ne a wajen sannan kuma babu wani sojin Najeriya ko Amurka da lamarin ya shafa.

    Rundunar ta ce kashe mayaƙan na ƙara raunana ƙarfin ƙungiyar na shirya share-hare da ke barazana ga tsaron Amurka da ƙawayenta.

  8. Hukuncin kisa da aka aiwatar bara shi ne mafi yawa cikin shekara 40 - Amnesty

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'Adam ta Amnesty International ta ce hukuncin kisa da aka aiwatar a faɗin duniya a shekarar da ta wuce, shi ne mafi yawa a cikin shekara arba'in 40.

    Ƙungiyar ta ce an samu ƙaruwar ne musamman saboda haddin da aka aiwatar a Iran, inda aka zartar da hukuncin kisa a kan mutum sama da 2,000.

    Hakan ta ce ya wuce ninki biyu na yawan waɗanda aka yi wa hukuncin kisan a shekarar da ta gaba ta.

    Yawanci waɗanda aka kashe masu laifin ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ne ko kuma laifin kisan kai.

    Amma kuma duk da hakan ƙungiyar ta Amnesty da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce an samu karuwa sosai ta yawan mutanen da ake zartar wa da hukuncin kisa saboda bambancin ra'ayi na siyasa.

    Wani mutum da aka kashe a 'yan makonnin da suka gabata an zarge shi ne kawai da laifin kai hari kan motocin 'yan sanda - amma ba wani mugun laifi ba.

  9. Trump ya ce lokaci na ƙure wa Iran kan yarjejeniyar tsagaita wuta

    Shugaban Trump ya sake yin gargaɗi ga Iran, yana mai kira gare ta, da ta fa hanzarta ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya, idan ba haka ba lokaci na ƙure mata.

    Shugaban na Amurka ya sake barazanar ne, bayan da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana da shi, a kan rikicin na Iran.

    Kafofin yaɗa labarai na Isra'ila, sun ruwaito cewa shugabannin biyu sun tattauna a kan komawa fagen yaƙin gadan-gadan, da kuma yiwuwar kai sababbin hare-hare na haɗin guiwa, to amma dai babu tabbacin hakan a hukumance.

    Wakilin BBC ya ce yanzu Iraniyawa na jin cewa su suke da dama sosai da ta cewa, ganin yadda suka iya jurewa har lamarin ya kawo yanzu

    Tun a watan da ya gabata aka ayyana dakatar da buɗe wuta a rikicin - domin bayar da damar tattaunawar zaman lafiya - wadda Pakistan ke shiga tsakani, kuma har yanzu ɓangarorin biyu sun yi hannun riga da juna sosai a matsayarsu.

  10. Barka da Safiya

    Masu bibiyar wannan shafi na Kai Tsaye, barka da warhaka. Da fatan mun wayi gari cikin ƙoshin lafiya.

    Kamar kullum, za mu ci gaba da kawo maku labarai kan yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Kuna iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo da tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.