Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftan ƙasashe da kuma sauran sassan duniya na ranar Juma'a 21 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello, Haruna Kakangi

  1. Yadda Ebola ke mayar da yara marayu a Kwango

    Wani sabon rahoton da ƙungiyar kula da yara ta Save the Children ta fitar ya ce aƙalla yara 180 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango ne suka rasa uwa da uba ko kuma ɗaukacin masu kula da su sanadiyyar ɓarkewar cutar Ebola tun daga watan Mayu.

    Hukumomi a lardin Ituri, inda nan ne cibiyar yaɗuwar cutar sun ce an kuma raba yara sama da 100 sanadiyyar karɓar magani.

    Ƙungiyar ta nuna damuwa kan cewa yaran da abin ya shafa na cikin haɗarin fuskantar cin zarafi da kuma shiga cikin damuwa.

    A yanzu ƙungiyar ta samar da wuraren kulawa da irin waɗannan yara yayin da iyayensu ke karɓar magani.

    Cutar na ci gaba da yaɗuwa cikin sauri, inda aka samu sama da mutum 5,000 da suka harbu.

  2. Mutum takwas sun mutun bayan jirgi ya faɗi a sansanin sojin Amurka

    Rundunar sojin saman Amurka ta ce mutum takwas sun mutu bayan wani jirgin sama da ke aiki da rundunar ya fadi a jihar Alaska.

    Jirgin wanda wani kamfanin farar hula ke aiki da shi ƙarkashin wani kwantiragi da gwamnati ya faɗi ne da rana a kusa da Cape Newenham a yankin Anchorage.

    Hukumomi sun ce har yanzu ba a bayyana mutanen da ke cikin jirgin ko kuma manufar tafiyarsu ba.

    Shugaban rundunar sojin saman Amurka a Alaska, Laftanar Janar Robert Davis, ya bayyana waɗanda suka mutu a matsayin ƙwararru masu sadaukar da kai da ke gudanar da wani muhimmin aiki a wani yanayi mai matuƙar wahala.

    "Wannan babban rashi ne mai raɗaɗi ga iyalan sojinmu da kuma al’ummomin da muke yi wa hidima," in ji Davis a cikin wata sanarwa.

    Ya ƙara da cewa babban abin da suka fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne tallafa wa iyalan waɗanda suka mutu da kuma abokan aikinsu a wannan lokaci na jimami.

    A cewar rundunar sojin saman Amurka da ke Alaska, jirgin ya tashi ne daga babban filin jirgin sama na Anchorage zuwa Cape Newenham, mai nisan kusan kilomita 725 daga birnin Alaska.

    Masu aikin ceto da suka isa wurin da hatsarin ya auku sun tabbatar da cewa babu wanda ya tsira.

    An fara bincike domin gano musabbabin hatsarin, yayin da hukumomi suka ce za a bayyana sunayen mamatan ne bayan an sanar da iyalansu.

  3. Zan kai wa Iran hari a kowane lokaci matuƙar akwai buƙatar hakan – Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai iya kai wa Iran hari ko sau 100 ne domin ganin ya hana ƙasar mallakar makamin nukiliya.

    A wata tattaunawa ta rediyo, Trump ya ce in ban da matakin da ya ɗauka, da yanzu babu Isra’ila ko ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

    A cikin tattaunawar Trump ya ce ya bayar da umarnin kai wa Iran hari ne yayin da bai wuce mako biyu ta mallaki makamin nukiliya ba.

    Trump ya ce duk da irin labaran da ake yaɗawa amma Amurka ce ke iko da mashigar Hormuz.

    Ya kuma dage kan cewa an yi matuƙar illa ga ɓangaren makamai masu linzami da kuma na jirage marasa matuƙa na ƙasar ta Iran, yayin da aka yi matuƙar raunana tattalin arziƙinta.

  4. Mutanen da suka mutu a haɗarin kwale-kwale a Sokoto sun kai 48

    Kimanin mutum 48 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman yara 12 bayan haɗarin jirgin ruwa da ya faru a yankin Goronya da ke jihar Sokoto.

    Akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su yara ne waɗanda ke kan hanyar zuwa gona a safiyar jiya Alhamis.

    A tattaunawarsa da BBC, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gada da Goronyo a majalisar wakilan Najeriya Bashir Gorau ya ce a halin yanzu masu ninkaya na ci gaba da aikin ceto domin ganin ko za a samo sauran yaran da suka ɓace da ransu.

    “Akasarin waɗanda abin ya rutsa da su yara ne da mata, yara ƴan ƙasa da shekara 10,” a cewar Gorau.

    “Rafi ya raba mutanen ƙauyen da gonakinsu, shi ya sa a kodayaushe mutane ke amfani da kwale-kwalen katako domin zuwa gona,” kamar yadda ɗan majalisar ya yi ƙarin haske.

    A Najeriya ana yawan fuskantar hatsarin kwale-kwale wanda ke laƙume rayuka musamman a yankunan karkara.

    Lamarin ya fi ƙamari ne a lokacin damina, inda rafuka kan cika da ruwa, sannan kuma babu wasu matakan kariya da ake amfani da su wajen irin wannan sufuri, haɗi da rashin ingancin kwale-kwalen.

  5. Iyayen yara sun yi zanga-zanga a Borno

    Iyayen yaran da aka sace a jihar Borno da ke arewa maso yammacin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a garin Uba jiya Alhamis domin neman gwamnati ta ceto kusan yara 100 da ake garkuwa da su daga yankin.

    A ranar 15 ga watan Mayu ne wasu mahara da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai farmaki a wata makaranta da ke ƙauyen Mussa mai maƙwaftaka da dajin Sambisa, inda suka sace ɗalibai kimanin 45 cikin har da ƙananan yara, wadanda har yanzu suke hannun ƴan bindiga.

    Zanga-zangar ta nuna yadda iyaye ke cikin damuwa kan yawaitar garkuwa da mutane da kuma hare-haren ƙungiyar Boko Haram duk da kasancewar sojoji a yankin.

    ISWAP da Boko Haram sun riƙa kai hare-hare da sace ɗalibai a makarantun yankin tsawon sama da shekara 15.

    Baya ga satar ɗaliban na ƙauyen Mussa, an kuma kai hari a wata makaranta a ƙauyen Lassa mai maƙwaftaka ranar 29 ga watan Yuni inda aka sace ɗalibai 36 da kuma malami waɗanda su ma har yanzu suna hannun masu garkuwa da su.

    A watan da ya gabata ne hukumomin ƙasar suka karɓo ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jiyar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

  6. Japan ta zartar da hukuncin kisa karo na farko cikin shekara ɗaya

    Japan ta aiwatar da hukuncin kisa na farko cikin sama da shekara guda.

    An yanke wa Sunayo Takami hukuncin kisa ne bayan samun shi da laifin kashe mutane biyar a wani hari da aka ƙona wani wurin wasa a shekarar 2009.

    Hakan na zuwa ne bayan shekaru 17 da aikata laifin, kuma shi ne na farko tun bayan zuwan wannan gwamnatin mai ci.

    Japan na daya daga cikin kasashe biyu kacal, wato ita da Amurka da ke cikin kungiyar G7 da ke aiwatar da hukuncin kisa, amma ba kasafai take aiwatar da shi ba.

  7. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'a a wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.