Ka samar da mafita ga 'yan Najeriya ba zargin 'yan adawa ba - Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi martani ga kalaman Shugaba Bola Tinubu da ke dora alhakin yunwa da talauci kan ‘yan adawa, inda ya bayyana zargin a matsayin kokarin kauce wa alhakin matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yakin neman zaben ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce ba daidai ba ne gwamnati ta kirkiri manufofin da suka janyo tsadar rayuwa sannan ta zargi wasu da bayyana matsalolin da jama’a ke ciki.
Ya ce jam’iyyar APC ce ta yi mulkin Najeriya na tsawon shekara takwas kafin Tinubu ya hau mulki, kuma yanzu gwamnatin tasa ta shafe sama da shekara uku tana jagoranci. A cewarsa, ‘yan Najeriya sun san waɗanda ke da alhakin tafiyar da harkokin ƙasar, don haka bai kamata a dora laifin tabarbarewar tattalin arziki kan ‘yan adawa ba.
Atiku ya kuma soki wasu manufofin gwamnati, ciki har da cire tallafin man fetur da faduwar darajar naira, yana mai cewa wadannan matakai sun kara jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali. Ya yi tambaya kan yadda gwamnati ke tafiyar da wasu kudade da aka ware wa ayyuka daban-daban tare da neman karin bayani kan wasu gibin kudade da ake magana a kai.
Ya ce babban abin da ‘yan Najeriya ke son ji shi ne matakan da gwamnati ta dauka domin magance yunwa, talauci da rashin tsaro, ba zargin ‘yan adawa ba. Atiku ya kara da cewa zaben shugaban kasa na 2027 zai bai wa masu kada kuri’a damar yanke hukunci kan ayyukan gwamnatin Tinubu bisa yanayin rayuwar da suke ciki.