Hawaye na ci gaba da bin kumatun Salah
Mo Salah ya kasa daina zubar da hawaye lokacin da yake bankwana da masoyansa da na ƙungiyarsa.
Liverpool da magoya bayanta ba za su taba mantawa da Salah ba
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku wainar da ake toyawa a ranar ƙarshe ta gasar Premier Ingila
Muhammad Buhari Fagge
Mo Salah ya kasa daina zubar da hawaye lokacin da yake bankwana da masoyansa da na ƙungiyarsa.
Liverpool da magoya bayanta ba za su taba mantawa da Salah ba
Samun nutsuwa da kwanciyar hankali
Duka magoya bayan Sunderland sun tashi cikin murna da farin ciki na yadda suka kai ga nasara a wasan da suka buga na kakarsu ta farko daga ɗagowa daga Premier bana.
A bara ƙungiyar ta buga Championship, wadda sai da ta buga wasa sama da 10 ba a iya doke ta ba a gida.
Yanzu ta samu tikitin zuwa gasar Europa, gasa ta biyu mafi daraja a nahiyar Turai.
An kawo Roberto de Zerbi lokacin da ya rage saura wasa bakwai a gama Premier ga kuma firgicin faɗawa Champioship.
Babu yabo babu fallasa, yayi nasara uku ya yi canjaras biyu, an kuma doke shi wasa biyu ya kuma dawo da ƙungiyar ta arewacin London Premier.
Dan ƙasar Italiyan na da damar haɗa tawagar da yake so a kaka mai zuwa ya kuma yi gyaran da ya kamata a ƙungiyar.
Komai ya ƙare bayan shekaru 14 da ta kwashe a Premier a ƙarshe West Ham ta koma Championship, gasar kwallon ƙafa ta Ingila mai daraja ta biyu.
Hammers sun faɗa ne da maki 39 da suka iya haɗawa kacal a Premier bana.
Tuni wasu magoya bayan ƙungiyar suka fice dga filin wasan na London, saboda zamansu a gasar ya ta'allaƙa ne da nasarar Everton a wasanta da Tottenham.
Abin da suke tsoro ya afku.
Tottenham ta tsallake rijiya da baya.
Mogoya bayanta sun fara murna.
Wasan Andoni Ariola na ƙarshe a Bournemouth, ya buga wasa 19 ba a yi nasara a kansa ba.
Yanzu sun samu damar zuwa gasar Europa a kaka mai zuwa.
Sunderland na da babban fata
Masu kofi sun tashi suna ci gaba da murnar ɗaukar kofinsu.
Wasa na dab da ƙarewa kuma yana sake ɗaukar zafi.
Damar da ke gaban West Ham na hannun Everton kuma Tottenham na iya ƙoƙarinta na tsira da kwallonta ɗaya.
Callum Wilson (90+4 mins)⚽️
Ko kwallayen za su yi wa West Ham amfani,
Yanzu suna jira su ji sakamakon wasan Tottenham domin sanin makomarsu.
An kara minti 10 a wasan.
Burin Brentford na Europa na dab da cika.
A cire Mo Salah, wasansa na ƙarshe a ƙungiyar Liverpool.
An shiga rudani a filin wasa na Anfield, magoya baya na ta zubar da hawaye.
Jean-Philippe Mateta (89 mins)⚽️
Phil Foden (90+1 mins)⚽️
Amma ana dubawa.
VAR ta kashe kwallon
Fulham ta yi canji:
Shiga - Josh King, Harry Wilson, Tom Cairney, Raul JImenez.
Fita - Kevin, Emile Smith Rowe, Oscar Bobb, Rodrigo Muniz.
Tom Cairney (81 mins) ⚽️
Jarrod Bowen ⚽️
Ko shakka babu West Ham na yunwar maki uku a wasan nan.
Villa ta yi canji uku.
Shiga: Amadou Onana, Youri Tielemans, Pau Torres.
Fita: Lamare Bogarde, Douglas Luiz, Victor Lindelof.