Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 22/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 22/10/2026

Taƙaitattu

  • An sauke wani malami daga limanci a Bauchi saboda zargin yi wa Tinubu kamfe
  • Iran ta ce ta tarwatsa jiragen ruwa huɗu a tekun Fasha

Rahoto kai-tsaye

Rabi'atu Kabir Runka

  1. Wace ce matar da aka tabbatar ta kamu da cutar Ebola a Najeriya?

    Shugaban hukumar lafiya ta Afirka ya shaida wa BBC cewa matar da aka tabbatar ta kamu da cutar Ebola ta farko a Najeriya a wannan karon, tun bayan ɓarkewar cutar a Gabashin Afirka a watan Mayu matar wani jami'in diflomasiyya.

    Matar ƴar asalin ƙasar Uganda ce, amma tana zaune a Abuja babban birnin Najeriya, inda yawancin ofisoshin jakadancin ƙasashen duniya suke, sannan ma'aikatan suke zama.

    A cewar shugaban hukumar, Dokta Jean Kaseya, matar ta fara rashin lafiya ne a ranar 3 ga watan Oktoba, kwana uku bayan ta koma babban birnin Najeriya bayan hutun da ta je a Uganda.

    Ministan lafiya na Najeriya ya tabbatar wa BBC cewa majinyaciyar mai shekara 42 ta shafe makonni biyu da rabi a Kampala, babban birnin Uganda, inda ya ƙara da cewa ta kuma yi hutun sa'o'i biyu a babban birnin Habasha bayan dawowarta.

    "Tana cikin kwanciyar hankali, tana samun sauƙi," in ji Muhammad Ali Pate.

    Ministan ya ce hukumomi na aiki don hana yaɗuwar cutar kuma sun gano mutane 44 da suka yi mu'amala da matar, waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a ranar Talata.

    "Ba dukkansu sun kasance kusa da juna ba. Mun jefa ragar a fili domin mu iya shawo kanta gwargwadon iyawa," in ji Pate ga BBC.

    Ministan lafiya ya ce babu wani daga cikin waɗanda suka yi mu'amala da matar, wanda yanzu ke killace, da aka san yana da alamun cutar, ciki har da mutumin da suka yi tafiya tare da majinyaciyar, yana ƙara cewa matar ba ta yi tafiya zuwa wani wajen ba, bayan Abuja ba tun komawarta.

  2. Babu wata tattaunawa da ake tsakanin Amurka da Iran - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce a halin yanzu babu wata tattaunawa da ke gudana tsakanin ƙasarsa da Iran. Da aka tambaye shi ko ya janye daga tattaunawar da ake yi da Tehran, ya amsa cewa, "Ba ma tattaunawa da Iran a yanzu, amma za mu kai ga matsaya kan wannan batu. Hakan zai faru nan ba da jimawa ba."

    Trump ya ƙara da cewa mafi yawan mutane na ganin za a samu ci gaba kan batun ne bayan zaɓen tsakiyar wa'adin mulki na Amurka da ake sa ran za a yi nan gaba kaɗan.

    Shugaban na Amurka ya ce gwamnatinsa ta yi "abin da ya dace" kan batun Iran, yana mai bayyana takun saƙar da aka yi tsakanin ƙasashen biyu a matsayin "ƙaramin rikici."

    Kalaman Trump na zuwa ne a daidai lokacin da babban kwamandan sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, wanda ake ganin ya taka rawa wajen shiga tsakanin Amurka da Iran a baya-bayan nan, ya kai ziyara Tehran.

    Haka kuma, kafin wannan ziyara, Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ziyarci Iran domin tattaunawa da jami'an ƙasar.

  3. Amurka ta umarci ƴanƙasarta su fice daga Saudiyya

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta umarci jami'an diflomasiyyarta da iyalansu su fice daga Saudiyya saboda barazanar hare-haren da mayaƙan Houthi ke kai wa ƙasar.

    Jami'an Saudiyya sun ce an daƙile wani hari da aka kai ta sama kan wani wurin samar da man fetur.

    Sai dai mutum biyu sun mutu bayan wani jirgi mara matuƙi ya faɗi, yayin da wani mutum ya mutu a wani hari da aka kai filin jirgin saman King Fahad.

    Rikici tsakanin mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran da kuma Saudiyya ya ƙara tsananta tun daga watan da ya gabata.

    Houthi na mayar da martani kan hare-haren Saudiyya ta hanyar kai hare-hare kan filayen jiragen sama, cibiyoyin makamashi da sansanonin soji.

    Wani mai magana da yawun Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce an umarci ma'aikatan da ba sa gudanar da ayyukan gaggawa su fice daga ƙasar tare da iyalansu.

    Ya ƙara da cewa rikice-rikicen da ke gudana na iya ƙara tsananta cikin gaggawa.

    Rahotanni sun kuma ce mutum takwas sun jikkata sosai a harin da aka kai filin jirgin saman King Fahad.

  4. Lana Nusseibeh: Bafalasɗiniyar da ke takarar shugabancin MDD

    Hadaddiyar Daular Larabawa ta tsayar da wata karamar ministar harkokin waje a matsayin yar takarar da za ta gaji Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, da zarar wa'adinsa na biyu ya kare a karshen wannan shekarar.

    Lana Nusseibeh ta yi aiki a matsayin jakadiyar Abu Dhabi a Majalisar Dinkin Duniya na fiye da shekara goma.

    Wakilin BBC ya ce Idan aka zabe ta, Ms Nusseibeh, wadda asali ƴar Falasdin ce , za ta zama mace ta farko da za ta jagoranci wannan ƙungiya, kuma ta biyu daga yankin Gabas ta Tsakiya bayan Boutros Boutros Ghali.

    Akwai wasu ƴan takara shida da ke fafatawa, inda Rebeca Grynspan daga kasar Costa Rica ke kan gaba da tazara kadan a kuri'un zaben share fage.

  5. An sauke wani malami daga limanci a Bauchi saboda zargin yi wa Tinubu kamfe

    An sauke Limamin masallacin unguwar Madina da ke cikin garin Bauchi daga muƙaminsa bayan da aka zarge shi da yaɗa manufofin sake zaɓar shugaban Najeriya Bola Tinubu a cikin wa'azinsa.

    Rahotanni sun ce limamin mai suna Dahiru Abubakar na amfani da lokutan huɗuba bayan kammala sallolin farilla wajen bayyana ra'ayoyi da ake kallon suna goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Da yake magana kan lamarin, Liman Dahiru Abubakar ya ce a wa'azinsa yana jan hankalin jama'a ne cewa Shugaba Tinubu ba shi ne silar wahalhalun tattalin arziki da matsalolin tsaro ba, yana mai cewa waɗannan ƙalubalen suna da alaƙa da abin da ya kira "alamomin ƙarshen zamani."

    "Na kasance ina wa'azin mutane su daina ɗora alhakin matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki a kan Shugaba Tinubu. Ina kuma ƙarfafa musu gwiwa su sake zaɓensa tare da ba shi wata dama a zaɓen 2027 domin ya ci gaba da manufofinsa," kamar yadda Daily Trust ta ambato sgi yana cewa.

    Ya ci gaba da cewa wa'azinsa ya fi karkata ne kan tsoron Allah da kuma daina ɗora wa shugabanni laifin matsalolin tsaro, musamman Tinubu, domin Allah kaɗai ne zai iya kawo ƙarshen waɗannan matsaloli ta hanyar amsa addu'a.

    "A wa'azina nakan mayar da hankali kan tsoron Allah da ayyukanmu na yau da kullum. Na kan kawo misalan matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu ƙasashen Afirka kamar Sudan, Chadi da Mali, sannan in tambaya ko Tinubu ne ke da alhakin abin da ke faruwa a waɗannan ƙasashe."

    Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban kwamitin gudanarwar masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya ce matsalar kwamitin da limamin ba ta taƙaitu ga zargin yaɗa manufofin Tinubu kaɗai ba.

    "Babbar matsalarmu da shi ita ce ba wai yaɗa manufofin Tinubu kawai yake yi ba, har ma da yadda yake tara mutane a gaban masallaci, kuma wani lokaci yakan shiga cikin masallacin ne da gangan domin tattauna harkokin siyasa."

  6. Mutane sama da 800,000 za su iya rasa muhallansu a Somalia - IOM

    Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ta yi gargaɗin cewa kusan mutum 874,000 na iya rasa matsugunansu a Somalia cikin watanni uku masu zuwa sakamakon ambaliya.

    Hukumar ta ce kogunan da ke cika da ruwa da kuma mamakon ruwan sama na barazana ga al'ummomin da tuni suke fama da fari da kuma yawan ƙaura.

    Shugaban IOM a Somalia, Manuel Marques Pereira, ya ce akwai fargabar cewa dubban iyalai za su rasa gidajensu na makonni. Ya ce mutane da dama sun riga sun kaurace wa muhallansu, kuma ba su da isassun hanyoyin da za su dogara da su wajen tinkarar sabon bala'in.

    Ya kuma yi kira da a samar da kuɗaɗe cikin gaggawa domin taimaka wa mutane kare gidajensu da rayukansu.

    Sabbin hasashen da IOM da Hukumar ƴan gudun hijira ta Denmark (DRC) suka fitar sun nuna cewa mutum 874,319 na iya ƙaura daga gidajensu tsakanin Oktoba da Disamba, inda ambaliya za ta haddasa kashi 92 cikin 100 na wannan ƙaurar.

    Gargaɗin na zuwa ne yayin da Somalia ke shiga lokacin damina, tare da hasashen samun ruwan sama fiye da yadda aka saba sakamakon tasirin El Niño.

    IOM ta ce ya zuwa yanzu ta samu kashi 14.4 cikin 100 ne kawai na kuɗaɗen da take buƙata domin shirin tunkarar ambaliyar.

    Tuni dai alamun ambaliya suka fara bayyana a yankuna kamar Doolow, Jowhar da Baidoa, yayin da ake hasashen cewa Beledweyne da Gaalkacyo za su kasance daga cikin wuraren da za su fi fuskantar barazanar ƙaura sakamakon ambaliya.

  7. Masu zanga-zanga sun tayar da hayaniya wajen taron Trump

    Masu zanga-zanga sun tayar da hayaniya a wani gangamin da Shugaba Trump ya gudanar a jihar South Carolina kafin zaben tsakiyar wa'adi da ke tafe a Amurka.

    Jami'an tsaro sun kori akalla masu zanga-zanga goma daga wurin taron da aka yi a Jami'ar Clemson, wanda Mista Trump ya halarta, da nufin kara wa sanata Darline Graham na jam'iyyar Republican kwarin gwiwa.

    Wani mai zanga-zanga ya kira Mista Trump maci amana kuma ya yi nemi da a saki bayanan Jeffrey Epstein.

    Wani kuma ya kira shi mai aikata laifukan yaki. Mista Trump ya bayana masu zanga-zangar a matsayin sojojin haya kuma ya yaba wa wani mai goyon bayansa da ya cusa wa daya daga cikinsu naushi.

  8. Ana ci gaba da luguden wuta tsakanin Rasha da Ukraine

    Ana ci gaba da artabu tsakanin Rasha da Ukraine, duk da cewa Shugaba Trump ya bayyana ra'ayinsa na cewa bangarorin da ke yaki da juna a yanzu sun fi kusa da kawo karshen yaƙin fiye da kowane lokaci tun farkon rikicin.

    Rasha ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a Kyiv, babban birnin Ukraine, kwana guda bayan ta amince da sabon zagayen tattaunawar zaman lafiyar.

    Magajin garin Kyiv, Vitaliy Klitschko, ya bayyana cewa mutum shida ne suka jikkata sakamakon hare-haren.

    Duk da wadannan hare-hare da Rasha ke kai wa, Shugaban Ukraine ya bayyana goyon bayansa ga shawarar Amurka na sake fara tattaunawa da Rasha.

    Ya ce ganawar da Steve Witkoff ya yi da Rasha na da matukar muhimmanci, abin da muka fahimta daga ganawar shi ne Rasha na goyon bayan tattaunawa tsakanin kasashen mu uku

  9. Iran ta ce ta tarwatsa jiragen ruwa huɗu a tekun Fasha

    Rundunar ruwa ta dakarun juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce ta kai hari kan wasu jiragen ruwa huɗu da take sanya ido a kansu a arewa maso tsakiyar Tekun Fasha.

    Dakarun sun ce lamarin ya faru ne yayin da jiragen ke jigilar man fetur zuwa wani jirgi, inda daga bisani gobara ta tashi a cikinsu.

    A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana jiragen ruwan a matsayin waɗanda suka karya doka, tana mai cewa sun bi hanyoyin ruwa da ba su dace ba.

    Iran ta ce ba za ta amince da wasu hanyoyin da jiragen ruwa ke amfani da su a kudancin mashigin Hormuz ba, duk da cewa ana amfani da su wajen zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

    Rundunar ta kuma ce wasu jiragen ruwa uku sun yi hatsari a daren Laraba bayan sun taka nakiyoyin da aka dasa a cikin ruwan a yammacin mashigin Hormuz, lamarin da ya haddasa gobara.

    A cewarta, yawan irin waɗannan haɗurran na da alaƙa da amfani da hanyoyin ruwa da ta ce ba su da tsaro.

    A ƙarshen sanarwar, rundunar ruwa ta IRGC ta zargi sojojin Amurka da ci gaba da abin da ta kira tsokana a yankin.

    Ta kuma yi gargadin cewa ci gaba da irin waɗannan matakai na iya janyo martani mai faɗi da zai shafi sansanonin sojin Amurka da ke yankin.

  10. Assalam alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya.

    Kamar dai jiya, yau ma Rabi'atu Kabir Runka ke muku fatan an wayi gari lafiya domin kawo muku wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa