Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 05/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 05/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala Umarah a Saudiyya

    Shugabna Najeriya, Bola Tinubu ya koma ƙasar bayan kammala ziyarar Umara zuwa Saudiyya.

    Jirgin shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin saman Abuja, babban birnin ƙasar ranar Laraba da daddare.

    A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya ya tafi ziyarar ibadar zuwa Saudiyya.

    A lokacin ziyarar shugaban ya samu damar shiga ɗakin Ka'abar.

  2. Wasu ƴan Republican sun fara nesanta kansu da Trump

    Jamiyyar Republicans mai mulki a Amurka, ta fara nazari kan dalilan da suka sa jam'iyyar ta sha mummunan kaye a zaɓen tsaiyar wa'adi.

    Sakamakon zaɓen ya sa jam'iyyar Demokrats mai hamayya ta ƙwace rinjayen majalisun dokokin kasar biyu.

    Faɗuwar da Repbulican ta yi a zaɓen, na ɗaya daga cikin munanan shan kayen da ta taɓa fuskanta a tarihi.

    Ƴan jam'iyyar sun fara nazari kan makomar jamiyyar bayan shugabancin Donald Trump.

    Wasu daga cikin aminansa sun fara nesanta kansu da shugaban Amurkan, musamman mataimakinsa, JD Vance.

    Mista Vance ya ɗora alhakin shan kayen kan yakin da Amurka ke yi da Iran, kodaya ke ra’ayinsa ya zo ɗaya da na Shugaba Trump wanda da kansa ya ce yaƙin Iran ne ya sa suka faɗi a zaɓen.

  3. Maraba lale

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Yau ma dai kamar jiya Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.