Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 12 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

  • Iran ta sanar da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka biyar a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Tsohon sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya rasu
  • Iran da Oman sun tattauna kan gudanar da zirga-zirgar Jirage a mashigar Hormuz
  • Za mu tsananta martaninmu idan hare-haren Amurka da saɓa alƙawurra suka ci gaba - Iran
  • Tarihin yadda aka assasa rundunar sojin Najeriya da Hausawa 18 a Legas

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. NDLEA ta kama ƴar Afirka Ta Kudu da hodar iblis a filin jirgin Abuja

    Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama wata ’yar ƙasar Afirka ta Kudu mai shekara 38 a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan gano kilo 5.75 na hodar iblis da aka ɓoye a cikin kayanta.

    Hukumar ta ce matar ta yi ƙoƙarin amfani da ɗanta mai shekara uku a matsayin kariya don kauce wa cikakken binciken jami’an tsaro.

    An kama ta ne bayan isowarta daga Doha a ƙasar Qatar.

    NDLEA ta bayyana cewa da farko matar ta musanta mallakar jakunkunan da aka kama da hodar, amma bincike ya nuna alamun kayanta sun yi daidai da bayanan da ke fasfot ɗinta.

    Daga bisani ta amsa cewa kayanta ne, bayan ta yi iƙirarin cewa ta manta ta yi rajistarsu.

    A wani samame na daban, NDLEA ta kama wani ɗan Najeriya a filin jirgin saman Legas da ƙwayar methamphetamine, sannan ta ƙwace tabar wiwi mai nauyin kilo 4,143.5 da aka shigo da ita daga Canada, wadda darajarta ta haura naira biliyan 10.3.

  2. Afirka ta Kudu za ta miƙa wanda ake zargi da kashe matarsa da ƴaƴansa a Birtaniya

    Gwamnatin Afirka ta Kudu ta sanar da cewa za ta miƙa wani mutum da ake zargi da kashe matarsa da ƴaƴansa mata biyu a Birtaniya domin ya fuskanci shari'a.

    An kama wanda ake zargin, Ndodana Mkhanyisi Tshuma ɗan asalin ƙasar Zimbabwe da ya zama ɗan ƙasar Birtaniya a birnin Johannesburg ranar Juma'a.

    Ana sa ran zai gurfana a gaban kotu a Johannesburg ranar Litinin, kafin a tura shi zuwa Birtaniya domin ya fuskanci shari'a kan zarge-zargen da ake masa.

  3. Sojojin Najeriya sun kama wata mota ɗauke da miyagun ƙwayoyi a titin Lagos-Calabar

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama wata mota da ke ɗauke da tarin miyagun ƙwayoyi a kan titin Lagos zuwa Calabar bayan samun sahihan bayanan sirri daga wata majiya.

    Aikin da aka gudanar a ranar 9 ga Yulin 2026 ya kai ga cafke direban motar tare da ƙwace kayan da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.

    Binciken farko ya nuna cewa ana safarar kayan ne zuwa yankin Berger da ke Jihar Legas, amma wanda aka kama ya kasa bayyana masu kayan ko wanda za a kai wa su.

    Bayan kammala matakan farko na bincike, an miƙa wanda ake zargi da kuma miyagun ƙwayoyin ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Legas domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban doka.

    Babban Kwamandan Runduna ta 81, Manjo Janar Adebayo Babalola ya kuma buƙaci sojojin da su ƙara zage damtse wajen yaƙi da masu safarar miyagun ƙwayoyi da sauran masu aikata laifuka a yankin da suke kula da shi.

  4. Burkina Faso da Mali da Nijar sun tattauna domin ƙarfafa rundunar haɗin gwiwar ƙasashensu

    Ministocin tsaron ƙasashen Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar sun gudanar da taro a Ouagadougou ranar 10 ga Yuli domin duba matakan da za su ɗauka domin ƙarfafa rundunar haɗin gwiwar ƙasashen ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES), kamar yadda RFI ta ruwaito a ranar 11 ga Yuli.

    Ministan Yaƙi na Burkina Faso, Celestin Simpore, ya ce manufar tattaunawar ita ce fayyace tsare-tsare da ayyukan jami'an haɗin gwiwar.

    An gudanar da wannan taro ne a daidai lokacin da hare-haren masu iƙirarin jihadi suka sake ƙazancewa, inda aka kai manyan hare-hare a Mali da Burkina Faso. Waɗannan hare-haren na da alaƙa da ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da al-Qaeda.

    Simpore ya ce: "Dole rundunar haɗin gwiwar ta tashi tsaye wajen yaƙi da ta'addanci. Dole ne mu shirya domin fuskantar faɗa na gaske."

  5. Oman ta gayyaci jakadan Iran bayan sababbin hare-hare tsakanin Amurka da Iran

    Oman ta gayyaci jakadan Iran da ke birnin Muscat domin bayyana mata matsayinta bayan sabbin hare-haren sama da aka yi tsakanin Iran da Amurka.

    A wani mataki da ba kasafai Oman ke ɗauka ba, gwamnatin ƙasar ta soki Tehran a fili, tana mai bayyana damuwa kan abin da ta kira "rahin kyautawa."

    Rundunar juyin-juya-hali ta Iran ta ce ta kai hare-hare kan wuraren tallafi da na shan man Amurka a Oman, ƙasar da ke taka muhimmiyar rawa a matsayin mai shiga tsakani domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ƙasashen biyu.

    A nata ɓangaren, Amurka ta kai zagaye na uku na hare-hare kan Iran a wannan makon, a matsayin martani ga harin da sojojin Iran suka kai kan wani jirgin ruwa a mashigar Strait of Hormuz.

    Iran ta kuma sanar da cewa an rufe wannan mashigar ruwa har mama ta gani.

  6. Direbobin motocin dakon kayan agaji a Gaza sun yi zanga-zanga

    Direbobin manyan motocin da ke kai kayan agaji a Gaza sun gudanar da zanga-zanga bayan da sojojin Isra'ila suka kashe ɗaya daga cikin abokin aikinsu a kudancin yankin a ranar Laraba.

    Daya daga cikin direbobin manyan motocin ke nan ke cewa sun sha fada a lokacin yakin cewa mu daina shiga da kayan agaji cikin Gaza, to amma mu damuwarmu ita ce idan mu dakata da shigar kayan agajin mutane za su kasance cikin yunwa.

    Iyalan Ahmad Salim, sun ce ba ya dauke da makami, kuma ya daga hannuwansa sama lokacin da wani soja da ya kira shi ya harbe shi a ka.

    Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta ce Salim ya tunkaro wajensu ne a guje, kuma sojojin sun bude masa wuta ne saboda sun yi zargin cewa yana barazana a gare su ne.

    A wani rahoto da Kwamitin Bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar kwanan nan, ya ce Isra'ila na aikata abin da ya kira kisan kiyashi a Gaza. Isra'ila dai ta sha musanta zarge-zargen aikata kisan kiyashi a Gaza.

  7. Amurka ta ce mashigar Hormuz na buɗe duk da iƙirarin Iran na rufewa

    Amurka ta nanata cewa har yanzu jiragen ruwa na ci gaba da wucewa ta mashigar ruwan mashigar Hormuz, duk da cewa Iran ta sanar da cewa ta rufe wannan muhimmiyar hanya har sai mama ta gani.

    Rundunar CENTCOM, wadda ke kula da dakarun Amurka a yankin gabas ta tsakiya, ta ce mashigar a buɗe take ga dukkan jiragen ruwa da ke da haƙƙin wucewa a doka, tare da jaddada cewa Iran ba ita ce ke da iko da mashigar ba a yanzu.

    Haka kuma Amurka ta zargi Tehran da ƙaddamar da hare-hare na wauta.

    A daren jiya, Amurka ta kai zagaye na uku na hare-hare kan Iran a cikin wannan mako, a matsayin martani ga harin da sojojin Iran suka kai kan wani jirgin ruwa da ke amfani da ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar danyen mai a duniya.

    Bayan haka, Iran ta kai hare-hare kan ƙadarorin Amurka a sassa daban-daban na yankin, ciki har da Oman.

  8. Ƴanbindiga sun harbe mutum biyu a Toronto

    Ƴansanda a kasar Canada sun ce mutum biyu sun mutu, yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harbe-harben da aka yi a wani biki a birnin Toronto na kasar.

    Mataimakin shugaban 'yan sandan birnin, Frank Barredo, ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu ba a gano musabbabin harbe-harben ba.

    Sai dai ya ce alamu na nuna cewa an yi musayar wuta tsakanin mutane biyu da suka kai wa juna hari. Jami'an tsaron sun ce sun kwato bindigogi biyu, sannan sun tabbatar da cewa akwai wurare uku da lamarin ya shafa.

    Sai dai zuwa yanzu ba a kama kowa da hannu a kan harbe-harben ba.

  9. Iran ta ce ta kakkaɓo makami mai linzamin da Amurka ta harba mata

    Rundunar juyin juya halin Iran IRGC a lardin Lorestan ta ce ta kakaɓo wani makami mai linzami da sojojin Amurka suka harba mata a bayan garin Khorramabad, babban birnin lardin.

    Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto sashen hulɗa da jama'a na IRGC yana cewa sabon tsarin kariyar sararin samaniya na rundunar ne ya kakkaɓo makamin da safiyar Lahadi a yankin Dareh da ke wajen birnin Khorramabad.

    A wani bangare kuma, jami'an tsaron lardin Lorestan sun bayyana cewa wani ɓangare na makamin da Iran ta harba ya faɗo a wani wurin ajiye motoci da ke unguwar zama a birnin Durood, lamarin da ya jawo lalacewar kadarori kaɗan.

    Mataimakin jami'in siyasa da tsaro na gwamnatin lardin, Saeed Pourali, ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata sakamakon lamarin, yana mai jaddada cewa ba a kai wani harin makami mai linzami kan birnin Durood ba.

  10. INEC ta ƙara wa’adin miƙa sunayen ƴan takarar zaɓen 2027

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ƙara wa'adin da ta bai wa jam'iyyun siyasa na miƙa sunayen 'yan takararsu na zaɓen 2027 da kwana uku, kamar yadda jaridar intanet mai zaman kanta ta Daily Post ta ruwaito a ranar 12 ga Yuli.

    INEC ta ce jam'iyyun siyasa yanzu suna da damar miƙa sunayen 'yan takararsu har zuwa tsakar dare na ranar 14 ga Yuli agogon Najeriya.

    Hukumar ta bayyana cewa ta yanke wannan shawara ne bayan majalisar tuntuɓa ta jam'iyyun siyasa ta buƙaci hakan sakamakon ƙorafin fuskantar matsaloli wajen saka sunayen ƴantakarar a shafin yanar gizon hukumar.

    A cewar INEC, ƙarin wa'adin zai ba bai wa jam'iyyu damar shiga tsarin zaɓe cikin sauƙi tare da tabbatar da bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta Najeriya.

    Ana sa ran Najeriya za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da majalisun tarayya a watan Janairun 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi za su gudana a watan Fabrairun 2027.

  11. Oman ta yi allawadai da harin Iran a ƙasarta

    Ƙasar Oman ta yi allawadai da harin jiragen sama marasa matuƙa da Iran ta kai a yankin lardin Musandam, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito.

    A wata sanarwa da aka wallafa, Oman ta bayyana cewa tana matuƙar tir da harin, tare da jaddada cewa ta ɗauki dukkan matakan da suka dace domin kare tsaron ƙasar da mazaunanta.

    Wannan na zuwa ne bayan rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta ce ta kai wani "harin ba-zata mai ƙarfi" kan wuraren Amurka da ke tashar Duqm da ke Oman.

    Lamarin ya faru ne sa'o'i kaɗan bayan ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya gana da takwaransa na Oman a Muscat domin tattauna yadda za a gudanar da zirga-zirga da safarar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

    A wata sanarwa ta daban, IRGC ta zargi Amurka da matsa wa Oman lamba domin karkatar da wasu jiragen ruwa zuwa wata hanya da ta kira "ba bisa ƙa'ida ba" a kudancin mashigar Hormuz, tana mai cewa rundunar ruwan Iran ta dakatar da wannan yunkuri

  12. Rukuni na shida na ƴan Najeriya da aka kwashe daga Afirka ta Kudu sun isa Legas

    Wasu ’yan Najeriya 40 da aka kwaso daga Afirka ta Kudu sun isa filin jirgin saman Legas, wanda ya kai jimillar mutanen da aka dawo da su a rukuni na shida zuwa 1,174.

    Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ta ce mutanen sun isa ne cikin wani jirgin haya.

    Waɗanda aka kwaso sun nuna godiyarsu ga Shugaba Bola Tinubu bisa amincewa da dawo da su cikin gaggawa, tare da yabawa duk masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen gudanar da aikin.

    NiDCOM ta ce gwamnatin Jihar Imo ta bai wa mutanen jihar da suka dawo tallafin naira miliyan ɗaya kowannensu, yayin da kamfanin MTN ya ba su layukan waya da data kyauta tare da alƙawarin tura naira 100,000 ga kowane mutum.

    Haka kuma, gwamnatocin jihohin Edo da Delta da wasu ƙungiyoyi sun sanar da shirye-shiryen tallafa wa waɗanda suka dawo gida.

  13. Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican kuma aminin Trump ya rasu

    Sanata mai wakiltar jam'iyyar Republican daga jihar South Carolina a Amurka, Lindsey Graham, ya rasu yana da shekaru 71 bayan wata gajeriyar jinya.

    Ofishinsa ne ya sanar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da aka fitar da yammacin ranar Asabar.

    Graham ya shafe fiye da shekaru ashirin yana aiki a Majalisar Dattawan Amurka, inda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun 'yan Republican kuma aminin shugaban ƙasar Amurka Donald Trump.

    Marigayin ya yi fice saboda tsattsauran ra'ayinsa kan manufofin harkokin waje, musamman game da Iran.

    Ya kasance mai goyon bayan matakan matsin lamba kan Tehran, ciki har da ƙaƙaba ƙarin takunkumai da kuma ɗaukar matakai masu tsauri kan shirin nukiliyar ƙasar da ayyukanta a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Rasuwar Lindsey Graham ta girgiza harkokin siyasar Amurka, inda shugabanni da abokan aikinsa suka fara aikewa da saƙonnin ta'aziyya.

    Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun sanatoci masu tasiri a jam'iyyar Republican, kuma wanda ya taka rawa sosai a manufofin tsaron Amurka da dangantakarta da ƙasashen duniya.

  14. Senegal ta kori kocinta bayan ficewa daga gasar Kofin Duniya

    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal (FSF) ta sanar da fara aikin sallamar kocin ƙasar, Pape Thiaw, da ma'aikatansa bayan ficewar Senegal daga gasar Kofin Duniya ta 2026.

    Matakin ya biyo bayan rashin nasarar ƙungiyar ta kai wa zagaye na 16 bayan ta sha kashi a hannun Belgium da ci 3-2, duk da cewa ta fara wasan da ci 2-0.

    FSF ta ce an yanke shawarar kawo ƙarshen kwangilar Pape Thiaw da ma'aikatansa ne a wani taron kwamitin zartarwa da aka gudanar ranar Asabar, wanda ya duba sakamakon da ƙungiyar ta samu a gasar.

    Hukumar ta kuma ɗora wa shugabanta, Abdoulaye Fall, alhakin sanar da kocin hukuncin a hukumance tare da jagorantar wani sabon shiri na sake fasalin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙasar.

    Ana sa ran Abdoulaye Fall zai yi wa manema labarai bayani a Dakar ranar Litinin kan dalilan ɗaukar wannan mataki da kuma shirye-shiryen da hukumar ke yi domin farfaɗo da ƙwallon ƙafar Senegal, wadda kafin fara gasar ake hasashen za ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Afrika masu fafutukar lashe kofin.

  15. Za mu tsananta martaninmu idan hare-haren Amurka da saɓa alƙawurra suka ci gaba - Iran

    Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya yi gargaɗin cewa Tehran za ta ƙara tsananta martaninta idan hare-haren Amurka suka ci gaba ko kuma idan ba a cika alƙawurran da aka ɗauka ba.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, ya ce “zaman yarjejeniyoyin da bangare ɗaya kawai ke ɗaukar nauyi ya ƙare.”

    Qalibaf ya bayyana cewa Iran ta sha kira ga sauran ɓangarori su mutunta alƙawurra da wajibansu, yana mai cewa duk wanda ya ƙi yin hakan dole ne ya fuskanci sakamakon abin da ya aikata.

    Tare da saƙon nasa, ya wallafa wani ɓangare na sashe na biyar na takardar yarjejeniyar Islamabad, wanda ya jaddada gudanar da harkokin mashigar Hormuz bisa ga tsare-tsaren Iran.

    Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun-saƙa tsakanin Iran da Amurka, tare da ƙarin fargaba game da tsaro da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

  16. Iran ta harba mana makaimai masu linzami uku - Jordan

    Sojojin Jordan sun sanar da cewa makamai masu linzami uku da aka harba daga Iran sun faɗo a wasu sassan ƙasar da safiyar Lahadi.

    A cikin wata sanarwa, wata majiya ta soja ta ce makaman sun sauka ne a wurare daban-daban na masarautar Jordan, amma babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata sakamakon lamarin.

    Majiyar ta ƙara da cewa ɓarnar da aka samu ta takaita ne ga ƙananan lalacewar kadarori kaɗai.

  17. Iran da Oman sun tattauna kan gudanar da zirga-zirgar Jirage a mashigar Hormuz

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce tattaunawar da ministan harkokin wajen ƙasar Abbas Araqchi ya yi da jami'an Oman a Muscat ta mayar da hankali ne kan yadda za a gudanar da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

    Baghaei ya bayyana cewa tawagogin ƙwararru na fannin shari'a da fasaha daga ƙasashen biyu sun halarci tattaunawar, inda suka yi musayar ra'ayi kan tabbatar da tsaro da lafiyar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar.

    Ya ce an tattauna batutuwan da suka shafi mutunta 'yancin mallaka na ƙasashen biyu da ke gaɓar mashigar, da kuma bin dokokin ƙasa da ƙasa, tare da tanade-tanaden sashe na biyar na Yarjejeniyar Fahimtar Juna ta Islamabad.

    Baghaei ya ƙara da cewa Iran ta jaddada cewa duk wani sabon tsari na gudanar da zirga-zirga a mashigar Hormuz ya kamata ya kasance sakamakon shawarwari tsakanin Iran da Oman.

  18. Tsohon sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya rasu

    Gwamnatin Qatar ta sanar da rasuwar tsohon sarkin ƙasar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, yana da shekaru 74 a duniya.

    Sheikh Hamad ya jagoranci harkokin mulkin Qatar daga shekarar 1995 zuwa 2013, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu gina Qatar ta zamani.

    A lokacin mulkinsa, ƙasar ta samu gagarumin ci gaban tattalin arziki, wanda ya taimaka wajen ɗaga darajar Qatar a idon duniya.

    Haka kuma, a shekarar 1996 ne aka ƙaddamar da tashar talabijin ta Al Jazeera bisa umarninsa, lamarin da ya sanya kafar yada labaran ta zama ɗaya daga cikin shahararrun kafofin watsa labarai a duniya.

    Rasuwarsa ta jawo alhini a Qatar da ma sauran sassan duniya, inda ake tuna irin rawar da ya taka wajen sauya fasalin ƙasar.

  19. Iran ta sanar da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka biyar a yankin Gabas ta Tsakiya

    Iran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka guda biyar da ke Oman, Jordan, Kuwait, Bahrain da Qatar, a wani mataki da ta bayyana a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ke kai wa yankunan kudancin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa, rundunar juyin juya halin Iran ta ce rundunar sararin samaniyarta ta kai hari kan cibiyoyin kayan aikin jiragen ruwa masu ɗaukar jiragen yaƙin Amurka da kuma wuraren man fetur a tashar jiragen ruwa ta Duqm da ke Oman.

    IRGC ta kuma bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami wajen kai harin kan muhimman cibiyoyin soja da kayayyakin more rayuwa a sansanin sojin sama na Prince Hassan da ke Jordan.

    Iran ta ce hare-haren wani ɓangare ne na martanin da take mayarwa kan abin da ta zargi Amurka da aikatawa na "cin zarafin soja", yayin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Har yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumomin Amurka, Kuwait, Bahrain ko Qatar kan waɗannan iƙirare.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Lahadi.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.