Muna ci gaba da tattaunawa da Iran - Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ana ci gaba da tattaunawa da Iran.
Da yake amsa tambayar wani ɗan jarida a Fadar White House game da waɗannan tattaunawa, Trump ya ce:
“Suna son yin magana, kuma suna magana na gaskiya."
Trump ya kuma bayyana yaƙin da ake yi da Iran a matsayin wani yanayi na musamman, yana mai cewa ya zuwa yanzu bai jefa wa masu biyan harajin Amurka wani nauyi mai yawa ba.
A halin da ake ciki, rahotanni na nuni da cewa masu shiga tsakani daga Qatar sun shafe lokaci suna tattaunawa a Tehran kan sabon tayin da Amurka ta gabatar domin dawo da tattaunawar zaman lafiya.